Ƙananan hukumomin Najeriya
yanki na kusa da na ƙarshe sama da mazaɓa a tsarin yankuna na mulkin Najeriya
(an turo daga Kananan Hukumomin Nijeriya)
Ƙananannan hukumomi a Najeriya Najeriya nada adadin ƙananan hukumomi ɗari bakwai da saba'in da huɗu (774). Kuma kowace ƙaramar hukuma tana da sugabanni da suke da ikon gudanar da harkokin ƙaramar hukumar. Shugaba a ƙaramar hukuma shi ne (chairman), wanda shi ne Babban mai ikon zartarwa sannan mambobinsa waɗanda ake zaɓen su tare wato Kansiloli. Akan rarraba kowace ƙaramar hukuma zuwa ƙananan mazaɓu mazaɓu wanda duk ƙaramar hukuma nada adadin mazaɓa ƙaranci guda goma (10), mafi yawa kuma guda goma sha biyar (15).[1]
ƙananan hukumumin a Nijeriya | |||||
---|---|---|---|---|---|
Bayanai | |||||
Ƙaramin ɓangare na | Yankunan Najeriya, second-level administrative division (en) da mazaunin mutane | ||||
Ƙasa | Najeriya | ||||
Wuri | |||||
|
Ayyukan Ƙaramar Hukuma a Nijeriya.
gyara sasheAyyukan da Kananan hukumomin da ke Najeriya ke yi ko suke da damar yi, na nan a bayyane cikin Constitution (kundin tsarin mulki) amma daga cikin irin ayyukan da suke yi:
- Bijiro da tsarin tattalin arziƙi ga gwamnatin jiha;
- Karbar haraji da kuɗaɗen da ta yi ayyuka;
- Samarwa, Kafawa da kula da maƙabartu, wuraren binne mutane da gidajen gajiyayyu ko marasa karfi;
- Bayar da izini ga masu ababen hawa, kamar, keke, trucks (other than mechanically propelled trucks), kwale-kwale, baro, da amalenke;
- Samarwa, Kulawa da gudanar kasuwanni, wuraren ajiye motoci da wuraren shakatawan jama'a;
- Ginawa da kuma kula da Kananan hanyoyi (roads), layika (streets), hanyoyin ruwa (drains) da wasu manyan hanyoyin jama'a, wurin hutu, da wasu budaddun wuraren;
- Sama hanyoyi da layika suna, daba gidaje lamba;
- Samarwa da kula da ababen tafiye-tafiye na jama'a da wurin zubda shara;
- Yin rijista wadanda aka haifa, wadanda suka mutu, da wadanda suka yi aure;
- Binciken gidajen al'ummah ko na 'yan haya saboda kayyade adadin kudin daya kamata su biya haraji, kamar yadda majalisar jiha ta kayyade,
- Tsarawa da kula da yadda ake gudanar da tallace-tallace, tafiya da ajiye dabbobin kiwo, shaguna da kiosks, wuraren cin abinci da wasu wuraren da ake sayar da abinci ga jama'a, da kuma wuraren wanki da guga.
Jerin Ƙananan Hukumomi.
gyara sasheManazarta.
gyara sashe- ↑ https://carnegieendowment.org/2022/07/18/halting-kleptocratic-capture-of-local-government-in-nigeria-pub-87513
- ↑ 2.00 2.01 2.02 2.03 2.04 2.05 2.06 2.07 2.08 2.09 2.10 2.11 2.12 2.13 2.14 2.15 2.16 2.17 Cite web |title=List of Local Government Areas in Cross River State |url=http://www.the-nigeria.com/2014/05/local-government-areas-in-cross-river.html%7Carchiveurl=https://www.webcitation.org/6XzVnEOmv?url=[permanent dead link] |archivedate=23 April 2015 |deadurl=no |df= }}