Neja
Jihar Niger Sunan barkwancin jiha: Jihar Makamashi. | ||
Wuri | ||
---|---|---|
![]() | ||
Ƙidaya | ||
Harsuna | Hausa, Turanci, Nupe, Gbagyi | |
Gwamna | Abubakar Sani Bello (APC) | |
An ƙirkiro ta | 1976 | |
Baban birnin jiha | Minna | |
Iyaka | 76,363km² | |
Mutunci 2006 (ƙidayar yawan jama'a) |
3,954,772 | |
ISO 3166-2 | NG-NI |
Jihar Niger Jiha ce dake ƙasar Najeriya. Tana da yawan fili kimani na kilomita murabba’i 76,363 da yawan jama’a milyan uku da dubu dari tara da hamsin da huɗu da dari bakwai da saba'in da biyu (ƙidayar yawan jama'a a shekara ta 2006). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Minna. Abubakar Sani Bello shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Ahmed Muhammad Ketso. Jahar ta Naija tanada manyan mutane da dama wadanda suka rike manyan mukamai a Najeriya sannan jaha ce wacce ta ke da tsofaffin shugabanni kasa na Najeriya har guda biyu a lokacin mulkin soja, wato Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) mai ritaya da kuma Abdusalami Abubakar mai ritaya dukkaninsu mutanan Jahar ta Neja ne.
Manyan kananan hukumomin Jahar sune, Chanchaga, Bosso da kuma kananan hukumomin Bidda, Suleja da kuma Kontagora.
Manyan yarukan jahar sune Nufanchi, Hausa, Gbagi da kuma turanci inda yankunan Bidda da Agaie da kuma Lapai, Mokwa sukafi yawan masu amfani da yaren Nufanci, Yankin Kontagora, Kagara, Mariga, Mashegu Rijau, Suleja sukeda mafi rinajayen masu amfani da yarukan Hausa. Paikoro, Chanchaga, Bosso, Edati dadai sauransu suna amfani da saura yarokan a matsayin masu rinjaye.
Akwai wuraren tarihi sosai a jahar ta Naija musamman a garin Zungeru inda anan nan ne turawan Yamma suka sanya hannun domin hadewan Nigeria kasa daya daga sauran yankuna sannan a wannan garin ne gwamnan farko na Najeriya ya yada zango a matsayin hedikwata gareshi.
Alhaji Umar Farouk Bahago shine sarkin Minna
Jihar Niger tana da iyaka da misalin jihohi shida, su ne: Babban birnin tarayya, Kwara, Kogi, Kaduna, Kebbi kuma da Zamfara. [1]
Kananan HukumomiGyara
Jihar Neja nada Kananan Hukumomi guda ashirin da biyar (25). Sune:
- Agaie
- Agwara
- Bida
- Borgu
- Bosso
- Chanchaga
- Edati
- Gbako
- Gurara
- Katcha
- Kontagora
- Lapai
- Lavun
- Magama
- Mariga
- Mashegu
- Mokwa
- Munya
- Paikoro
- Rafi
- Rijau
- Shiroro
- Suleja
- Tafa
- Wushishi
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |