Zurmi

ƙaramar hukuma a jihar Zamfara, Najeriya

Zurmi karamar hukuma ce dake a Jihar Zamfara, Arewa maso yamman Nijeriya.Zurmi tana daya daga cikin manya manyan kananan hukumomi dake da yawan fadin qasa a jihar baki daya,

Zurmi

Wuri
Map
 12°48′41″N 6°47′38″E / 12.8114°N 6.7939°E / 12.8114; 6.7939
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Zamfara
Labarin ƙasa
Yawan fili 2,834 km²
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa supervisory councillors of Zurmi local government (en) Fassara
Gangar majalisa Majalisar Zurmi
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

Karamar Hukumar tana da garuruwa da kauyuka da dama kamar Gurbin Bore, Kwashabawa, Birane, Mayasa, Tungar Fulani, Mashema, da Tubali. An kiyasta yawan al'ummar karamar hukumar Zurmi ya kai 258,731. Mafi yawan mazauna yankin 'yan kabilar Hausa/Fulani ne. Ana amfani da harshen Hausa a karamar hukumar, kaso tis'in da biyar na mazauna yankin mabiya addinin musulunci ne. Fitattun alamomin karamar hukumar Zurmi sun hada da bankin Zurmi Microfinance Limited da Makarantar Sakandaren Larabci ta Gwamnati, Zurmi.Karamar Hukumar Zurmi tana da fadin kasa murabba'in kilomita 2,834 kuma tana da matsakaicin zafin jiki na digiri 34. Yankin yana da yawan zafi kuma yana da busasshiyar ƙasa.

TATTALIN ARZIKI NA ZURMI Noma wani muhimmin aiki ne na tattalin arziki a karamar hukumar Zurmi tare da kayayyaki iri-iri da ake nomawa a yankin. Ana kiwon dabbobi da dama irin su jakuna, rakuma, da raguna da kuma sayar da su a karamar hukumar. Sauran muhimman sana’o’in al’ummar karamar hukumar Zurmi sun hada da farauta, kasuwanci, da sana’ar fata.

Manazarta

gyara sashe