Nasarawa
Jihar Nasarawa: jiha ce dake, a Arewa ta tsakiyar ƙasar Najeriya. Tana da yawan filaye kimanin kilomita murabba’in 27,117 da yawan jama’a miliyan ɗaya da dubu ɗari takwas da sittin da tara da ɗari uku da saba'in da bakwai (ƙidayar shekara ta 2006). Babban birnin tarayyar jihar shi ne Lafia. Abdullahi Sule, shi ne gwamnan jihar tun zaɓen shekara ta 2011, har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shine Emmanuel Akabe. Dattijai a jihar sun haɗa: Philip Aruwa Gyunka, Abdullahi Adamu da Suleman Asonya Adokwe.
Nasarawa | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Lafia | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 2,523,395 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 93.06 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 27,117 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Filato | ||||
Ƙirƙira | 1 Oktoba 1996 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Majalisar Zartarwa ta Jihar Nasarawa | ||||
Gangar majalisa | Majalisar Jihar Nasarawa | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-NA | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | nasarawastate.gov.ng |
Jihar Nasarawa tana da iyaka da jihohi huɗu: Plateau, Kogi, Taraba, Benue da Abuja.
Ƙananan hukumomi
gyara sasheJihar Nasarawa nada adadin ƙananan hukumomi guda goma sha uku (13),ga kowanensu tare da kuma adadin yawan Mutanen dake a Ƙaramar hukumar. (Ƙidayar ahekara ta 2006)[1]:
gyara sasheShiyar Sanata ta Yamma a Nasarawa | 716,802 | Shiyar Sanata ta Arewa a Nasarawa | 335,453 | Shiyar Sanata ta Kudu a Nasarawa | 811,020 | ||
---|---|---|---|---|---|---|---|
Karu | 205,477 | Akwanga | 113,430 | Awe | 112,574 | ||
Keffi | 92,664 | Nasarawa Egon | 149,129 | Doma | 139,607 | ||
Kokona | 109,749 | Wamba | 72,894 | Keana | 79,253 | ||
Nasarawa | 189,835 | Lafia | 330,712 | ||||
Toto | 119,077 | Obi | 148,874 |
Labarin Yanayi
gyara sasheYanayi
gyara sasheNasarawa tana da yanayi mai zafi mai zafi da savanna. Yanayin zafin birnin na shekara shine 29.39°C (84.9°F) kuma ya kan yi ƙasa da -0.07% idan aka kwatanta da na Najeriya. Nassarawa na samun hazo kusan milimita 136.71 (inci 5.38) kuma tana da kwanaki 155.37 na ruwan sama (42.57% na lokacin) kowace shekara.
A jihar Nasarawa, lokacin rani yana da danshi kuma wani bangare na gajimare, kuma ana yin zafi duk shekara. Lokacin damina yana da tsauri da yawa. Matsakaicin zafin jiki na shekara-shekara yana daga 63 zuwa 95 digiri Fahrenheit, da wuya yana faɗuwa ƙasa da 57 ko sama da 101.
Daga ranar 29 ga Janairu zuwa 14 ga Afrilu, lokacin zafi, tare dkuma a matsakaita yawan zafin rana da ya wuce 93°F, yana ɗaukar watanni 2.5. Watan da ya fi zafi a jihar Nasarawa a duk shekara shi ne Maris, inda matsakaicin zafin jiki ya kai 95°F, kuma mafi karancin zafin jiki ya kai 74°F.
Lokacin sanyi na watanni 3.7, wanda ke gudana daga Yunin shekarar 22 zuwa 13 ga Oktoba, yana da matsakaicin zafin rana na ƙasa da 85°F. Nasarawa ta fuskanci wata mafi sanyi a cikin shekara a cikin Disamba, tare da matsakaicin yanayin ƙasa na 64 ° F da mafi girma 89 ° F.
Ma'adanai
gyara sasheMa'adanai a jihar basarawa sun haɗa da;[2]
- Ma'adanin Baryte
- Ma'adanin Bauxite
- Ma'adanin Coal
- Ma'adanin Dolomite
- Ma'adanin Sapphire
- Ma'adanin Talc
- Ma'adanin Quartz
- Ma'adanin Tantalite
- Ma'adanin Tourmaline
- Ma'adanin Mica
- Ma'adanin Iron
Ilimi
gyara sasheJihar Nasarawa naɗa makartun masu yawa , waɗanda suka hada da kamarantun primare, sakandare dakuma makarantun gaba da sakandare:
Makaratn gaba da Sakandare
gyara sashe- College of Education Akwanga[3]
- Federal polytechnic Nasarawa[4]
- College of Agriculture Lafiya
- Nasarawa State University [5]
- Federal Government College
Addini
gyara sasheMafiya yawan al'umar dake zaune a jihar Nasarawa Musulmai ne[6] ko Kuma kiristoci[7], amma akwai kaɗan da suke addinin Mazuganci
Adadin Al'umma
gyara sasheJihar Nasarawa naɗa adadin mutane 1,869,377 a kididdigar shekara ta 2006, wanda hakan ya bawa jihar zama ta biyu a yawan al'umma bayan jihal Bayelsa[8]
Gwamnati
gyara sasheJihar Nasarawa tana gudana a ƙarƙashin gunadar wa ta gwamnan jihar Abdullahi Sule[9], wanda shike jagoran sauran ayyuka na jihar. Garin na dauke da yan-majalisu, da wasu mukarraban gwamnati
Wuraren Bude Ido
gyara sasheJihar Nasarawa nada wurareb shakatawa da kuma bude ido masu yawa , wasu daga ciki sunhaɗa da
Sanannun Mutane
gyara sasheYare/Kabilu
gyara sasheJihar Nasarawa bada kabilu ma bam-banta guda 25 , sanannu daga cikinsu sun hada da
Manazarta
gyara sashe- ↑ 2006 Population Census, Federal Republic of Nigeria, National Bureau of Statistics. Archived from the original Archived 2007-07-04 at the Wayback Machine on 2009-03-25.
- ↑ https://nigerianembassythehague.nl/about-nigeria/natural-resources/
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-10-27. Retrieved 2023-01-06.
- ↑ https://myschool.ng/classroom/institution-courses/federal-polytechnic-nasarawa
- ↑ https://www.myschoolgist.com/ng/fulafia-courses/
- ↑ https://tribuneonlineng.com/nasarawa-school-graduates-7-honours-4-muslims-for-contributions-to-islam/
- ↑ https://duniyarmuayau.com.ng/2020/12/25/me-ya-faru-da-mabiya-addinin-kirista-a-jihar-nasarawa-shugaban-ƙaramar-hukumar-lafia/[permanent dead link]
- ↑ https://web.archive.org/web/20110519235026/http://www.population.gov.ng/files/nationafinal.pdf
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-01-06. Retrieved 2023-01-06.
- ↑ http://www.globalpost.com/webblog/nigeria/dreaming-farin-ruwa
- ↑ https://thenationonlineng.net/mission-to-maloney-hill/
- ↑ https://newsdiaryonline.com/sulaiman-ibrahim-assumes-office-as-head-refugees-commission/
- ↑ https://www.blueprint.ng/osana-of-keana-five-years-of-impactful-royalty/
- ↑ https://emporiumreporters.com.ng/tag/hrh-alhaji-ahmadu-aliyu-ogah-onawo/
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/519885-profile-of-new-apc-national-chairman-abdullahi-adamu.html
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/opinion/135496-nasarawa-massacre-barbarians-on-rampage-by-dele-agekameh.html
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |