Charanchi
Charanchi (ko Cheranchi ) ƙaramar hukuma ce a jihar Katsina, arewacin Najeriya. Garin, akan babbar hanyar A9, shi ne hedkwatar karamar hukumar.[1]Shugaban karamar hukumar shine Dr.Badamasi Lawal Charanchi[2] yawan jama'a ya kai kimanin 79,000 (2003), kuma yankin ya kai 471. 2. [1]
Charanchi | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jahar Katsina | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 471 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Tarihi
gyara sasheAn kafa karamar hukumar ne daga tsohuwar karamar hukumar Rimi a shekarar 1996. A yanzu haka akwai kansiloli 11 da ke wakiltar mazabarsu a harkokin gudanarwar karamar hukumar. Wadannan kansilolin suna da hakkin tsige Shugaban Karamar Hukumar idan aka yi rashin da’a ko almubazzaranci da asusun gwamnati.
Hakimi
gyara sasheAkwai hakimai biyu a karamar hukumar; Sarkin Shanun Katsina Hakimin Charanchi da Sarkin Kurayen Katsina Hakimin Kuraye.
Sauran garuruwa
gyara sasheSauran garuruwan karamar hukumar sun hada da Kuraye, Banye, Radda, Koda, Ganuwa, Yana, sabon Gari da Maje.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Charanchi". nigeriacongress.org. Archived from the original on 2003-12-31. Retrieved 2007-02-08.
- ↑ Labaran, Abdu (2003-05-27). "Charanchi LG boss tasks wealthy individuals". Daily Trust. Archived from the original on 2007-09-27. Retrieved 2007-02-08.