Damboa ƙaramar hukuma ce dake Jihar Borno Nijeriya. H Shelkwatar ƙaramar hukumar na nan ne a cikin garin Damboa. Tana da girman ƙasa kimanin 6,219 km² da kuma yawan jama'a da suka kai 233,200 tun daga alƙaluman ƙidayar shekara ta 2006.[1]

Damboa

Wuri
Map
 11°09′N 12°45′E / 11.15°N 12.75°E / 11.15; 12.75
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Borno
Labarin ƙasa
Yawan fili 6,219 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Wani yanke a domboa na jahar barno

Lambar aika saƙo zuwa ƙaramar hukumar ta postal itace 601.[2] Asalin mazauna ƙaramar hukumar Damboa sune Mutanen Marghi, amma saboda haɓakar tattalin arziki Damboa ta hanyar sana'ar kamun kifi a wancan lokaci yasa aka samu mutanen Kanuri da wasu suke yawan kai komo a Damboa har yakai ga sun zama mazauna garin da auren matan garin Damboa. Hakan yasa a, yawancin mutanen Damboa akasarin su rabi Kanuri ne kuma rabi Marghi, dukda haka dai har yanzu akwai gidajen Marghi tsantsa waɗanda basu cuɗanya ba. Sanadiyar cuɗanyar al'ada a garin yasanya yawancin ƴan'asalin garin Damboa sunfi son jingina su da Marghi wasun su kuma Kanuri, amma dai ayau a Damboa akwai mutanen Marghi waɗanda sune ke da rinjaye da kuma mutanen Kanuri waɗanda suke binsu kuma suna zaune a garin kansu ɗaya.[1]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Brinkhoff, Thomas (2013-11-20). "Damboa (Local Government Area, Nigeria) – population statistics, map and location". www.citypolulation.de. Retrieved 2014-05-21.
  2. "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 2012-11-26. Retrieved 2009-10-20.
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.