Open main menu

Jamhoriya Tarayyar Najeriya
Flag of Nigeria.svg Coat of arms of Nigeria.svg
Location Nigeria AU Africa.svg
Nigeria - Location Map (2013) - NGA - UNOCHA.svg
Taken Kasa:

Zaman lafiya,Haɗin kai da kuma cigaba

Yaren Kasa Turanci
Babban Birni Abuja
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
Fadin Kasa 923 768 km2
Manyan yaruka Hausa, Yoruba, Igbo, Kanuri, Fulani, Marghi, Igala, Nupe, Egbira, Ijaw
Girman Ruwa % (1.4)%
Adadin Al'umma 182 202 000 (2015)
Yawan Mutane 197/ 2km
Shekarar 'Yanci

1960
Kudin Kasa Naira
Bambancin Lokaci +1 UTC
Yanar gizo .ng
Lambar wayar hannu ta Kasa-da-Kasa +234

Najeriya ko Nijeriya kasa ce dake nahiyar Afirka ta yamma. Tana da al'umman dasu kai fiye da mutum miliyan dari da saba'in da kabilun da suka haura 300. Hasali ma ita ce kasa ta uku a yawan kabilu a duniya. Najeriya ta samu mulkin kanta ne a 1 ga watan oktoba, shekarar 1960 daga Turawan mulkin mallaka na Birtaniya. Najeriya ta yi iyaka da kasashe uku; Daga arewacin kasar, akwai kasar Nijar , daga gabashi akwai Cadi da Kamaru, daga yammacin kasar akwai kasar Benin sannan daga kudancin kasar akwai tekun atalantik ko tabkin Gine.

A da, Lagos ne baban Birnin kasar kuma mazaunin gwamnati, amma a shekarar 1991 aka maida Abuja ta zama babban birnin Najeriya.

TarihiGyara

Tarihi ya nuna cewar Nijeriya dadaddar kasa ce, kuma tarihi yanuna kasar nanan tun a shekara ta 500 kafin haihuwar Yesu Almasihu wato Annabi Isah (A.S), a wannan lokaci suka samata Ƙasar Hausa, addinin musulunci ya shiga Kasar Hausa ne tun karni na goma sha uku miladiya, akarshen karni na goma sha daya zuwa tsakiyar karni na goma sha hudu miladiya, kanim barno suka mamaye Kasar Hausa, kuma fulani sun mamaye kasar Hausa a farkon karni na goma sha tara miladiya har zuwan turawan mulkin malaka suka mamaye Lagos a shekara ta 1881 miladiya, ana cikin Yakin duniya I na farko sai turawan mulkin mallaka suka karo sojojin ruwa saboda suna tsoran jamusawa da ke kamaru kada sumamaye Nijeriya, amma mulkin Nijeriya na farko a hannun turawan Burtgal. A shekara ta 1885 sai turawan Birtaniya suka mamaye duk fadin Nijeria har zuwa 01 ga oktoba 1960 Nijeriya ta samu 'yancin kanta daga a turawan Biritaniya.

AddiniGyara

Tsarin MulkiGyara

A shekara ta 1966 zuwa shikara ta 1979 sojoji ne ke ikon kasar, a shekara ta 1979 akayi tsari wanda yabawa talaka ikon zaben gwamna. A shekara ta 1983 sojoji suka rushe wannan tsarin da juyin mulki har zuwa shekara ta 1998 bayan rasuwar Sani Abacha, sai aka maido tsarin mulki na dimokaradiya akabawa talakawa ikon zaben shugaban da suke so, a shekara ta 1999 aka yi zabe a kasa Obasanjo ya lashe zabe yazama shugaban kasa na farko wanda talaka suka zaba yahau kare na biyu har zuwa shekara ta 2007, a wannan shekara aka yi zabe Umaru Yar'Adua ya lashe shine shugaban kasa a 2011. Dukkan su sun fito daga kungiya dayane (PDP). hukuncin nasu shima duk taure ne dan saboda da karfin iko sukaci zabe

JihohiGyara