Musawa

Karamar hukuma a Najeriya

Musawa karamar hukuma ce a jihar Katsina a Najeriya . Hedikwatarta tana cikin garin Musawa. Musawa na daya daga cikin tsofaffin kananan hukumomi guda bakwai (7), wadanda aka kirkira bayan da katsina ta samu jaha. Wadannnan kananan hukumomi sun hada da: Funtua, Malunfashi, Mani, Dutsen ma, Musawa, Daura da kuma ita kanta Katsina. Musawa na da kasuwa guda daya wadda take ci a duk ranar Asabar da Laraba. Mutanen garin Musawa suna kasuwanci da noma, Kuma suna karatu na addini dana zamani. A kwanan nan aka bada mukamai masu girma a garin Musawa wadanda suka hada da Hannatu Musa Musawa wadda aka baiwa mukamin minista, Hadiza Bala Usman itama an bata mukamin mai baiwa shugaban kasa shawara, sai Zainab Musa Musawa wadda aka baiwa kwamishina a jihar Katsina. Garin Musawa yana da yawan matasa sosai sai dai basu cika yin karatu mai zurfi ba, duk da yawan manyan mukaman da ake baiwa 'yan garinsu. Garin Musawa na da masallatan juma'a guda uku (3), inda bangaren izala ke da guda biyu (2) bangaren darika ke da guda daya (1). Suna masallatan Khamsus Salawat da yawa a Kowane bangare. Garin Musawa na da yanki na 849 km2 da yawan jama'a 171,714 a ƙidayar shekara ta 2006.

Cikin garin Musawa
Musawa

Wuri
Map
 12°07′46″N 7°40′08″E / 12.1294°N 7.6689°E / 12.1294; 7.6689
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJahar Katsina
Labarin ƙasa
Yawan fili 849 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Cikin garin Musawa

Lambar ofishin tura sakonni na yankin ita ce 833.[1] Garin Musawa Yana da tsohon tarihi Kuma suna da manyan mutane irin sure Alh. Musan Musawa, Alh. Dr. Bala Usman, Alh Abdullahi Dikko Inde da dai sauransu.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 2009-10-07. Retrieved 2009-10-20.