Sabuwa

Karamar hukuma a Najeriya

Sabuwa karamar hukuma ce dake a Jihar Katsina, Arewa maso yammacin Nijeriya. Karamar hukumar Sabuwa ta kasance a karshen jihar katsina ta kudu maso yamma, inda kuma tayi iyaka da jihar Kaduna.

Sabuwa

Wuri
Map
 11°18′N 7°06′E / 11.3°N 7.1°E / 11.3; 7.1
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Katsina
Labarin ƙasa
Yawan fili 642 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Galibin mutanen karamar hukumar Sabuwa manoma ne da 'yan kasuwa da suka shahara wajen noma da kasuwanci a jihar katsina.

Sannan Kuma karamar Hukumar Sabuwa Tana Daya daga cikin kananan Hukumomi Ukku Dake ciyar da jihar Katsina Dama kasa Baki Daya ta Hanyar Noma da kiwo,

Sabuwa tanada Albarkar Fatar kasa inda yakaiga babu Wani Kalar tsiro ko Hatsi da baza'a iya Noma Dubunnan buhunanshi ba, Kabar Maganar Masara, Dawa, Wake, Shinkafa da Sauransu.

Karamar Hukumar Sabuwa Tanada Manyan Mutane da Sukayi Shura ta Bangaren Siyasa da Mulki daga Matakin Jiha Har Tarayya, Wannan Yasa Mutanen Sabuwa Sukeda Idanu a bangarori da dama.

Kasuwanci a Karamar Hukumar Sabuwa Ba Wani Abu bane mai Tasiri Musamman a Shekarun Baya, Amma yanzu Abubuwan Sun Canza Mutane sun rungumi Kasuwancin Hannu biyu Sakamakon Rashin Tsaron da Yankin yake fama dashi, Domin kuwa a yanzu Ba kowanne Yanki na Sabuwa bane ake nomawa Saboda Yan Ta'adda sun kwace Dayawan wurare, Hakan Yasa Abinci yayi karanci a wasu yankunan na Jihar Katsina Dama kasa Baki daya.

Sabuwa tayi Iyaka da Jihar Kaduna ta Bangaren Kudu da Yamma, Karamar Hukumar Giwa daga Kudu sai Karamar Hukumar Birnin Gwari daga Yamma.

Sai Karamar Hukumar Dandume Ta Jihar Katsina daga Gabas, sai Karamar Hukumar Faskari ta Jihar Katsina daga Kudu.

A kidaya ta Shekarar 2006 Sabuwa Tanada yawan Jama'a da yakai 140,679 Amma a Hasashe na 2023 Sabuwa takai 251, 400.

Karuwar Bata Wuce Kashi 3.7 daga Shekarar 2006 zuwa022.

Tanada Gundumomi da yawa da Suka hada da

Sabuwa A

Sabuwa B

Machika

Damari

Gamji

Sayau

Rafin'iwa

Dugu Mu'azu

Gazari

Maibakko

✍️ Abuzarri Salisu Sabuwa

Manazarta gyara sashe

Abuzarri S (2023)


https

://nigeriadecide.org/polling_unit_category.php?state=Katsina&lga=Sabuwa

https://citypopulation.de/en/nigeria/admin/NGA021__katsina/

https://citypopulation.de/en/nigeria/admin/NGA021__katsina/