Mai'Adua (ko Maiaduwa ) karamar hukuma ce a jihar Katsina a Najeriya, tana iyaka da Jamhuriyar Nijar. Hedikwatarta tana kuma cikin garin Mai'Adua akan babbar hanyar A2 .

Mai'Adua

Wuri
Map
 13°11′26″N 8°12′42″E / 13.1906°N 8.2117°E / 13.1906; 8.2117
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Katsina
Yawan mutane
Faɗi 201,178 (2006)
• Yawan mutane 381.02 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 528 km²
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 824
Kasancewa a yanki na lokaci

Yana da yanki na 528 km2 da yawan jama'a 2 a ƙidayar shekarar 2006.

Lambar ofishin tura sakonni na yankin ita ce 824.[1]

Tana da babbar kasuwar ƙauye mai dumbin tarihi da ke ci a duk ranar Lahadi. Kasuwar ta kuma kasance cibiyar cinikayya ta ƙasa da ƙasa tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar. Dabbobi da suka hada da shanu, tumaki, awaki, rakuma, jakuna da dawakai su ne muhimman hajoji daga kasar Nijar, yayin da hatsi irin su masara, dawa, gero da waken suya mafi yawanci daga Najeriya.

Manazarta gyara sashe

  1. "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 2012-11-26. Retrieved 2009-10-20.