Najeriya
Najeriya; (/nadʒɪəriyə/) ko Nijeriya (/niˈdʒɪəriyə/) da (turanci: Nigeria): A Gwamnatance Tarayyar Najeriya ƙasa ce da take a Afirka ta yamma.[1][2][3] Tana da iyaka da ƙasar Nijar daga Arewa, da Chadi daga Arewa maso gabas da Kamaru daga gabas da Benin daga yamma, daga kudanci kuma tana a gaɓar Tekun Atlantika.[4][5][6] Jamhuriyar Tarayyar Najeriya ta ƙunshi Jihohi guda (36) tare da Babban Birnin Tarayya Abuja inda fadar shugaban ƙasar wato "villa" take.[7][8][9]
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
Nijeriya (ha) Naigeria (ig) Nàìjíríà (yo) | |||||
|
|||||
![]() | |||||
| |||||
Take | Nigeria, Muna Godiya | ||||
| |||||
Kirari |
«Unity and Faith, Peace and Progress» «Единство и вяра, мир и прогрес» «Good people, great nation» «Undod a Ffydd, Heddwch a Chynnydd» | ||||
Official symbol (en) ![]() |
Costus spectabilis (mul) ![]() | ||||
Suna saboda | Nijar | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Babban birni | Abuja | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 211,400,708 (2021) | ||||
• Yawan mutane | 228.85 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | Afirka ta Yamma | ||||
Yawan fili | 923,768 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Tekun Atalanta | ||||
Wuri mafi tsayi | Chappal Waddi (2,419 m) | ||||
Wuri mafi ƙasa | Tekun Atalanta (0 m) | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Taraiyar Najeriya | ||||
Ƙirƙira | 1 Oktoba 1963 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Tsarin gwamnati | Jamhuriyar Tarayya | ||||
Majalisar zartarwa | Majalisun Najeriya | ||||
Gangar majalisa | Majalisar TaraiyaNn Najeriya | ||||
• Shugabani ƙasar Najeriya | Bola Ahmad Tinubu (29 Mayu 2023) | ||||
Majalisar shariar ƙoli | Kotun Koli Ta Najeriya | ||||
Ikonomi | |||||
Nominal GDP (en) ![]() | 440,833,583,992 $ (2021) | ||||
Kuɗi | Naira | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Suna ta yanar gizo |
.ng (mul) ![]() | ||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +234 | ||||
Lambar taimakon gaggawa |
*#06# da 199 (en) ![]() | ||||
Lambar ƙasa | NG | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | nigeria.gov.ng |






Abuja tana ɗaya daga cikin manyan birane a duniya.[10][11][12]


Najeriya ta kasance gida da dama ga ƴan asalin turawa masu mulkin mallaka, jihohin da suka mallaka tunda (BC)[13][14][15] tare da Nok Wayewa ta kasance ita ce karo na farko da Turawan mulkin mallaka suka fara mallakewa a Yammacin Africa a cikin ƙarni na sha biyar (15).[16][17][18] A zamani jihar an samo asali da Birtaniya a cikin karni na sha tara (19) yana ɗaukar yanayin na yanzu tare da haɗe yankin Kudancin Najeriya da kuma kare Arewacin Najeriya a cikin shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da goma sha huɗu (1914)[19][20][21][22] ta Lord Lugard. Ingilishi ya kafa tsarin gudanarwa da na doka yayin aiwatar da mulkin kai tsaye ta hanyar shugabannin gargajiya.[23][24][25] Najeriya, ta zama ƙasar tarayyar da ke da ƴanci kai tsaye a ranar (1)ga watan Oktoba, shekara ta alif dubu ɗaya da ɗari tara da sittin (1960).[26][27][28] Ta fuskanci yaƙin basasa daga shekara ta dubu ɗaya da ɗari tara da sittin da bakwai (1967) zuwa shekarar dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in da bakwai (1977).[29][30][31] Sannan a biyo bayan zaɓaɓɓun gwamnatocin farar hula da mulkin kama-karya na soja, har sai an sami tabbatacciyar dimokuraɗiyya a shekara ta alif dari tara da chasa'in da tara (1999) zaɓen shugaban ƙasa na shekara ta (2015) shi ne karo na farko da shugaban ƙasa mai ci ya faɗi zaɓensa. [32][33][34]
Najeriya; tafi Ko wace kasa yawan al'umma a nahiyar Afrika, ƙasa ce Kuma mai yawan al’umma da ke zaune sama da ƙabilu guda ɗari biyu da sittin (260)[35][36][37] waɗanda ke magana da yarurruka daban daban guda ɗari biyar (500) dukkansu suna ɗauke da al'adu iri daban daban. Manyan ƙabilun guda uku su ne; Hausa – Fulani a Arewa, Yarbawa a Yamma, da kuma Igbo a gabas, waɗanda suka hada da kashi (60%) na yawan mutanen. Yaren hukuma shi ne Ingilishi,[38][39][40] wanda aka zaɓa don sauƙaƙe haɗin harshe a matakin ƙasa. Tsarin mulkin Nijeriya ya tabbatar da ƴancin yin addini kuma ƙasa ce dake ɗauke da al’ummar musulmai da kirista, a lokaci guda. Najeriya ta kasu kashi biyu tsakanin musulmai, waɗanda yawanci ke zaune a arewacin ƙasar, da kuma kiristoci,[41][42][43] waɗanda yawanci ke zaune a kudancin ƙasar, tare da ƴan tsirarun da ke yin addinin asali, kamar waɗanda ke cikin ƙabilar Igbo da kuma yarbawa.[44][45][46]

Najeriya ,ita ce ƙasa mafi yawan mutane a Afirka kuma ƙasa ta bakwai mafi yawan mutane a duniya,[47][48][49] tare da kimanin mutane miliyan ɗari biyu da shida (2,00,000,006). Tattalin arzikinta shine mafi girma a Afirka, kuma shi ne na ashirin da shida (26)[50][51][52] mafi girma a duniya ta hanyar GDP maras faɗi, kuma na ashirin da biyar (25), mafi girma daga PPP. Najeriya galibi ana ƙiranta da "Giant of Africa", ma'ana ƙarfin Afrika saboda yawan jama'a da tattalin arziƙinta, kuma bankin duniya yana dauƙarta a matsayin kasuwa mai tasowa. Karamar yanki ce a cikin Afirka, matsakaiciyar ƙarfi a cikin al'amuran ƙasa da ƙasa, sannan kuma tana ɗaya daga cikin ƙasashe mafi yawan al’umma a duniya.[53][54][55] Koyaya ƙasar tana ƙasa sosai a cikin jerin ƙasashen duniya, kuma har yanzu tana ɗaya daga cikin ƙasashe masu rashawa a duniya. Najeriya memba ce ta kafuwar tarayyar Afirka, kuma memba ce a ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa da dama, waɗanda suka haɗa da Majalisar Ɗinkin Duniya, ƙungiyar ƙasashen Yammacin Africa (ECOWAS) ƙungiyar ƙasashe masu arziƙin man fetur, (OPEC) kuma memba ce na yau da kullum a gamayyar MINT, kuma tana ɗaya daga cikin ƙasashe goma sha ɗaya masu tashen ƙaruwan tattalin arziƙi wato "Next Eleven".[56][57][58]
Kirkira:
gyara sasheSunan Nijeriya an dauke shi daga Kogin Neja wanda ya ratsa kasar.[59][60][61] Wannan sunan ya samo asali ne a ranar takwas (8), ga watan Janairun shekara ta (1897) dan jaridar Ingila Flora Shaw, wanda daga baya ya auri Lord Lugard, mai kula da mulkin mallaka na Burtaniya.[62][63][64] Nijar da ke makwabtaka da ita sun samo sunan daga wannan kogin.[65][66][67] Asalin sunan Nijar, wanda asali ana amfani da shi ne kawai zuwa tsakiyar Kogin Neja, ba tabbas. Watakila kalmar ta canza sunan Tuareg egerew n-iger ewen da mazauna ke amfani da shi a tsakiyar kogin da ke kusa da Timbuktu kafin mulkin mallaka na Turai na karni na (19). [68][69][70]
Tarihi:
gyara sasheTarihi, ya nuna cewar Nijeriya dadaddar kasa ce, kuma tarihi yanuna kasar na nan tun a shekara ta (500),[71][72][73] kafin haihuwar Yesu Almasihu wato Annabi Isah (A.S) a wannan lokaci suka samata suna Kasar Hausa.[74][75][76] Addinin musulunci ya shiga Kasar Hausa ne tun a karni na goma sha uku (13) miladiya.[77][78][79] a karshen karni na goma sha daya (11) zuwa tsakiyar karni na goma sha hudu (14) miladiya. Kanem Barno suka mamaye Kasar Hausa, kuma Fulani sun mamaye Kasar Hausa a farkon karni na goma sha tara (19) miladiya har zuwan Turawan Mulkin Mallaka suka mamaye Lagos a shekara ta (1881) miladiyya, ana cikin Yakin duniya na farko sai Turawan Mulkin Mallaka suka karo sojojin ruwa saboda suna tsoran Jamusawa da ke Kamaru kada sumamaye Najeriya, amma mulkin Najeriya na farko a hannun Turawan Portugal.[80][81][82] A shekara ta dubu daya da dari takwas da tamanin da biyar (1885) sai Turawan Birtaniya suka mamaye duk fadin Nijeria har zuwa Daya (1) ga watan oktoba, 1960. Nijeriya ta samu 'yancin kanta daga Turawan Biritaniya.[83][84][85]
Addinai:
gyara sasheTsarin Mulki:
gyara sasheA shekara ta (1966) zuwa shekara ta (1979) sojoji ne ke da ikon a kan kasar, a shekara ta (1979) a ka yi tsari wanda ya bawa talakawa ikon zaben gwamna. A shekara ta (1983) sojoji suka rushe wannan tsarin da juyin mulki har zuwa shekara ta (1998) bayan rasuwar Sani Abacha, sai aka dawo da tsarin mulki na dimokaradiya aka bawa talakawa ikon zaben shugaban da suke so, a shekara ta (1999) aka yi zabe a kasa.[86][87][88]Obasanjo ya lashe zabe ya zama shugaban kasa na farko wanda talaka suka zaba, ya hau karo na biyu har zuwa shekara ta dubu biyu da bakwai (2007)a wannan shekara aka yi zabe, Umaru Yar'Aduwa ya lashe shi ne shugaban kasa a shekarar ta dubu biyu da sha daya (2011). Dukkansu sun fito daga jam'iyya daya ne, wato (jam'iyyar PDP).[89][90][91] Umaru musa yar'aduwa ya rasu a shekara ta dubu biyu da tara (2009) matemakin sa Jonathan Goodluck ebele , ya cigaba da Mulki zuwa shekara ta dubu biyu da sha daya (2011).[92][93][94] A yayin da a kayi zabe yalashe yacigaba da Mulki harzuwa she Kara ta dubu biyu da sha biyar (2015) yayin da a kayi zabe ta dubu biyu da sha biyar (2015) shugaban kasa wato General Muhammad Buhari yalashe zabe.[95][96][97] Bayan shekara Tara wato yadda dimokiradiya ta tanadar ya sauka daga gadan Mulki she Kara ta dubu biyu da (2023), yabaiwa dan jam'iyarasa wato Bola Ahmad Tunubu Wanda yanzu shiyake rike da mulkin kasar Najeriya.[7][98][99]
Jihohi:
gyara sasheJeri | Sunan Jiha | Babban Birnin Jiha | Gwamna |
---|---|---|---|
1 | |||
2 | |||
3 | |||
4 | |||
5 | |||
6 | |||
7 | |||
8 | |||
9 | |||
10 | |||
- .Abia. .
- Adamawa.
- Anambra.
- Akwa Ibom.
- Bauchi .
- Bayelsa .
- Benue .
- Borno.
- Cross River.
- Delta.
- Enugu.
- Edo.
- Ebonyi.
- Ekiti.
- Filato .
- Gombe.
- Imo.
- Jigawa.
- Kano.
- Katsina.
- Kaduna.
- Kebbi.
- Kogi.
- Kwara.
- Lagos.
- Neja.
- Nasarawa.
- Ogun .
- Osun .
- Oyo.
- Ondo
- Rivers.
- Sokoto.
- Taraba.
- Yobe.
- Zamfara .
Babban birnin tarayya Abuja.
Yarika:
gyara sasheManyan yarika a Najeriya sune guda uku kamar haka: Harshen Hausa da Yarbanci da Inyamuranci, yaren Fulatanci ma yana daya daga cikin manyan yaruka a Najeriya.[100]
-
Hausawa.
-
Shiga irin ta al'adar Hausawa.
-
Bahaushe.
-
Matsahin dan kabilar Ibo (Inyamuri) da daddare.
-
Mace da shiga iri ta matan Ibo.
-
Matan kabilar Ibo suna gudanar da biki a al'adarsu.
Yarabawa ;Sun kasance na biyu a wayanda suka fi kowa yawa a cikin kasar Najeriya,[101] suna zaune a garuruwa irin su, Legas da, Ondo da Oyo, da Osun da Kwara da kuma Kogi.
-
Taron yarabawa a wani yanki a kasar yoruba , sun sanya irin na kayan su na yarbawa.
Sauran yaruka: Sun hada da; Fulani da Ibibio da Kanuri da Tiv da Bura da Shuwa Arab daMarghi da Kare-kare da Ɓachama da Mandara da Higgi da Kilba da Kibaku da Mafa da Glavda da Jukun da Waha da Gamargu da Igala da Nufe da Idoma da Ibibio da Efik da Anang da Ekoi da Awak da Waja da Waka.
Arzikin :
gyara sasheWasanni;
gyara sashe-
Yan wasan kwallon mata na Najeriya.
-
Yan wasan Najeriya a 1978.
-
Yan Najeriya na wasan kwallon kafa.
-
Mata na wasan kwallon kafa.
-
team na wasannin mata.
-
John Mikel Obi
Fannin tsaro.
gyara sasheKimiya da Fasaha.
gyara sasheSifiri.
gyara sasheSifirin Jirgin Sama.
gyara sasheSifirin Jirgin Kasa.
gyara sasheAl'adu.
gyara sasheMutane.
gyara sasheYaruka.
gyara sasheAbinci.
gyara sasheTufafi.
gyara sasheIlimi.
gyara sasheAddinai.
gyara sasheMusulunci.
gyara sasheKiristanci.
gyara sasheHotuna.
gyara sasheManazarta.
gyara sashe- ↑ The countries with the 10 largest Christian populations and the 10 largest Muslim populations". Pew Research Center. April 2019. Archived from the original on 18 January 2021. Retrieved 25 May 2020.
- ↑ Nigeria Fact Sheet" (PDF). United States Embassy in Nigeria. Archived from the original (PDF) on 18 October 2020. Retrieved 23 September 2018.
- ↑ Nigeria: The African giant". The Round Table. 50 (197): 55–63. 1959. doi:10.1080/00358535908452221. ISSN 0035-8533.
- ↑ Online Etymological Dictionary". Etymonline.com. Archived from the original on 2 July 2017. Retrieved 28 July 2014
- ↑ Non-Aligned Movement (NAM) – The Nuclear Threat Initiative". Archived from the original on 19 October 2021. Retrieved 19 October 2021.
- ↑ Kperogi, Farooq A. "Natasha H. Akpoti's Wildly Inaccurate History of Nigeria". Notes From Atlanta. Archived from the original on 11 August 2023. Retrieved 11 August 2023.
- ↑ 7.0 7.1 http://www.unep.org/news-and-stories/story/unep-ogoniland-oil-assessment-reveals-extent-environmental-contamination-and
- ↑ https://www.greenleft.org.au/content/shell%E2%80%99s-nigeria-ecocide-creating-refugee-crisis,%20https://www.greenleft.org.au/content/shell%E2%80%99s-nigeria-ecocide-creating-refugee-crisis[permanent dead link]
- ↑ https://web.archive.org/web/20141205124719/http://www.punchng.com/news/us-sends-medical-experts-to-study-how-nigeria-contained-ebola/
- ↑ Muhammadu Buhari
- ↑ Tylecote 1975 (see below)
- ↑ Eggert, Manfred (2014). "Early iron in West and Central Africa". In Breunig, P (ed.). Nok: African Sculpture in Archaeological Context. Frankfurt, Germany: Africa Magna Verlag Press. pp. 51–59.
- ↑ Holl, Augustin F. C. (June 2020). "The Origins of African Metallurgies". Oxford Research Encyclopedias. 22 (4): 12–13. doi:10.1093/acrefore/9780190854584.013.63. ISBN 9780190854584. OCLC 7869925414.
- ↑ Eggert, Manfred (2014). "Early iron in West and Central Africa". In Breunig, P (ed.). Nok: African Sculpture in Archaeological Context. Frankfurt, Germany: Africa Magna Verlag Press. pp. 53–54. ISBN 9783937248462.
- ↑ Breunig, Peter. 2014. Nok: African Sculpture in Archaeological Context: p. 21.
- ↑ Nicole Rupp, Peter Breunig & Stefanie Kahlheber, "Exploring the Nok Enigma Archived 4 March 2016 at the Wayback Machine", Antiquity 82.316, June 2008.
- ↑ Eze–Uzomaka, Pamela. "Iron and its influence on the prehistoric site of Lejja". Academia.edu. University of Nigeria, Nsukka, Nigeria. Archived from the original on 6 December 2020. Retrieved 12 December 2014.
- ↑ Hrbek, Ivan (1992). Africa from the seventh to the eleventh Century. James Currey Publishers. p. 254. ISBN 978-0-85255-093-9.
- ↑ Uzukwu, E. Elochukwu (1997). Worship as Body Language. Liturgical Press. p. 93. ISBN 978-0-8146-6151-2. Archived from the original on 27 June 2024. Retrieved 27 June 2024
- ↑ The Constitution of the Federal Republic of Nigeria" (PDF). 1963. Archived from the original (PDF) on 18 August 2021.
- ↑ MacDonald, Fiona; Paren, Elizabeth; Shillington, Kevin; Stacey, Gillian; Steele, Philip (2000). Peoples of Africa, Volume 1. Marshall Cavendish. p. 385. ISBN 978-0-7614-7158-5.
- ↑ Laitin, David D. (1986). Hegemony and culture: politics and religious change among the Yoruba. University of Chicago Press. p. 111. ISBN 978-0-226-46790-0.
- ↑ Achebe, Nwando, 1970-. The female king of colonial Nigeria : Ahebi Ugbabe. Bloomington. ISBN 978-0-253-00507-6. OCLC 707092916.CS1 maint: multiple names: authors list (link)
- ↑ Falola, Toyin; Genova, Ann (2009). Historical Dictionary of Nigeria. Scarecrow Press. p. 328. ISBN 978-0-8108-6316-3. Retrieved 29 March 2015.
- ↑ Falola, Toyin; Paddock, Adam (2012). Environment and Economics in Nigeria. Routledge. p. 78. ISBN 978-1-136-66247-8. Retrieved 29 March 2015.
- ↑ Falola, Toyin, and Matthew M. Heaton, A History of Nigeria (2008), pp. 85–109
- ↑ Peterson, Derek R., ed., Abolitionism and imperialism in Britain, Africa, and the Atlantic (Ohio University Press, 2010).
- ↑ Falola, Toyin, and Matthew M. Heaton, A History of Nigeria (2008), pp. 85–109.
- ↑ Adam, Abba Idris, "Re-inventing Islamic Civilization in the Sudanic Belt: The Role of Sheikh Usman Dan Fodio." Journal of Modern Education Review 4.6 (2014): 457–465. online Archived 15 April 2021 at the Wayback Machine
- ↑ "Nigeria – CIA World Factbook 2019" (PDF). Archived from the original (PDF) on 23 September 2020. Retrieved 25 May 2020.
- ↑ Slow death slavery course abolition northern Nigeria 18971936 | Regional history after 1500". Cambridge University Press. Archived from the original on 8 March 2021. Retrieved 22 January 2020.
- ↑ https://www.theguardian.com/society/2015/may/29/outlawing-fgm-nigeria-hugely-important-precedent-say-campaigners
- ↑ "Buhari wins historic election landslide". Reuters (in Turanci). 2015-03-31. Retrieved 2020-05-25.
- ↑ Udofia, O.E. (1981). "Nigerian Political Parties: Their Role in Modernizing the Political System, 1920–1966". Journal of Black Studies. 11 (4): 435–447. doi:10.1177/002193478101100404. JSTOR 2784073. S2CID 143073983.
- ↑ Juang, Richard M. (2008). Africa and the Americas: culture, politics, and history: a multidisciplinary encyclopedia, Volume 2. ABC-CLIO. p. 597. ISBN 978-1-85109-441-7.
- ↑ Hrbek, Ivan (1992). Africa from the seventh to the eleventh Century. James Currey Publishers. p. 254. ISBN 978-0-85255-093-9.
- ↑ Eze–Uzomaka, Pamela. "Iron and its influence on the prehistoric site of Lejja". Academia.edu. University of Nigeria, Nsukka, Nigeria. Archived from the original on 6 December 2020. Retrieved 12 December 2014.
- ↑ Uzukwu, E. Elochukwu (1997). Worship as Body Language. Liturgical Press. p. 93. ISBN 978-0-8146-6151-2. Archived from the original on 27 June 2024. Retrieved 27 June 2024
- ↑ Laitin, David D. (1986). Hegemony and culture: politics and religious change among the Yoruba. University of Chicago Press. p. 111. ISBN 978-0-226-46790-0.
- ↑ Falola, Toyin; Heaton, Matthew M. (2008). A History of Nigeria. Cambridge University Press. p. 23. ISBN 978-0-521-68157-5.
- ↑ MacDonald, Fiona; Paren, Elizabeth; Shillington, Kevin; Stacey, Gillian; Steele, Philip (2000). Peoples of Africa, Volume 1. Marshall Cavendish. p. 385. ISBN 978-0-7614-7158-5.
- ↑ Falola, Toyin, and Matthew M. Heaton, A History of Nigeria (2008), pp. 85–109.
- ↑ Falola, Toyin, and Matthew M. Heaton, A History of Nigeria (2008), pp. 85–109.
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/520849-number-of-poor-people-in-nigeria-to-reach-95-million-in-2022-world-bank.html
- ↑ https://www.washingtonpost.com/outlook/2019/09/16/official-us-poverty-rate-is-based-hopelessly-out-of-date-metric/
- ↑ Juang, Richard M. (2008). Africa and the Americas: culture, politics, and history: a multidisciplinary encyclopedia, Volume 2. ABC-CLIO. p. 597. ISBN 978-1-85109-441-7.
- ↑ Hrbek, Ivan (1992). Africa from the seventh to the eleventh Century. James Currey Publishers. p. 254. ISBN 978-0-85255-093-9.
- ↑ Gordon, April A. (2003). Nigeria's Diverse Peoples: A Reference Sourcebook. ABC-CLIO. pp. 44–54. ISBN 978-1-57607-682-8. Retrieved 29 March 2015.
- ↑ Adam, Abba Idris, "Re-inventing Islamic Civilization in the Sudanic Belt: The Role of Sheikh Usman Dan Fodio." Journal of Modern Education Review 4.6 (2014): 457–465. online Archived 15 April 2021 at the Wayback Machine
- ↑ Slow death slavery course abolition northern Nigeria 18971936 | Regional history after 1500". Cambridge University Press. Archived from the original on 8 March 2021. Retrieved 22 January 2020.
- ↑ "The end of slavery". The Story of Africa. BBC News. Archived from the original on 23 July 2020. Retrieved 28 May 2011.
- ↑ Udofia, O.E. (1981). "Nigerian Political Parties: Their Role in Modernizing the Political System, 1920–1966". Journal of Black Studies. 11 (4): 435–447. doi:10.1177/002193478101100404. JSTOR 2784073. S2CID 143073983.
- ↑ Mann, Charles C. (1990). "Choosing an Indigenous Official Language for Nigeria" (PDF). Archived (PDF) from the original on 2 December 2020. Retrieved 10 July 2020.
- ↑ The Constitution of the Federal Republic of Nigeria" (PDF). 1963. Archived from the original (PDF) on 18 August 2021.
- ↑ Irede, Akin (17 March 2022). "Aguiyi-Ironsi: The murder that birthed Nigeria's northern hegemony". The Africa Report. Archived from the original on 23 February 2023. Retrieved 23 February 2023.
- ↑ https://www.fao.org/nigeria/fao-in-nigeria/nigeria-at-a-glance/en/
- ↑ Falola and Heaton, A History of Nigeria (2008) pp 158–59
- ↑ Murray, Senan (30 May 2007). "Reopening Nigeria's civil war wounds". BBC News. Archived from the original on 5 March 2012. Retrieved 28 May 2011.
- ↑ "Nigerian Constitution". Nigeria Law. Archived from the original on 25 May 2016. Retrieved 17 July 2015.
- ↑ Daly, Samuel Fury Childs (7 August 2020). A History of the Republic of Biafra. Cambridge University Press. doi:10.1017/9781108887748. ISBN 978-1-108-88774-8. S2CID 225266768.
- ↑ Background Paper on Nigeria and Biafra, Declassified Documents Reference System.
- ↑ David Williams, President and power in Nigeria: The life of Shehu Shagari (Routledge, 2018).
- ↑ Nigeria, Military Faces Daunting Challenges", AP Press International, 3 March 1984. Retrieved 22 February 2007
- ↑ Siollun, Max (25 October 2018), Levan, Carl; Ukata, Patrick (eds.), "Civil Military Affairs and Military Culture in Post-Transition Nigeria", The Oxford Handbook of Nigerian Politics, Oxford University Press, pp. 272–287, doi:10.1093/oxfordhb/9780198804307.013.13, ISBN 978-0-19-880430-7
- ↑ Daly, Samuel Fury Childs (7 August 2020). A History of the Republic of Biafra. Cambridge University Press. doi:10.1017/9781108887748. ISBN 978-1-108-88774-8. S2CID 225266768.
- ↑ Murray, Senan (30 May 2007). "Reopening Nigeria's civil war wounds". BBC News. Archived from the original on 5 March 2012. Retrieved 28 May 2011.
- ↑ Metz, Helen Chapin (1991). "Nigeria: A Country Study – Civil War". Library of Congress Country Studies. Archived from the original on 5 June 2011. Retrieved 28 May 2011.
- ↑ The Arabic name nahr al-anhur is a direct translation of the Tuareg.
- ↑ https://books.google.com/books?id=bs5rTH7GClgC&pg=PA48
- ↑ The Biafra War and the Age of Pestilence". Litencyc.com. Archived from the original on 20 August 2018. Retrieved 28 July 2014.
- ↑ McDonald, Gordon C., Area Handbook for the Democratic Republic of the Congo (Congo Kinshasa) (1971), p. 263
- ↑ Michael I. Draper, Shadows: Airlift and Airwar in Biafra and Nigeria 1967–1970.
- ↑ Stearns, Jason K. Dancing in the Glory of Monsters: The Collapse of the Congo and the Great War of Africa (2011), p. 115
- ↑ Wrong, Michela. In the Footsteps of Mr Kurtz: Living on the Brink of Disaster in Mobutu's Congo (2000), p. 266
- ↑ Watts, Michael (1987) State, Oil and Agriculture in Nigeria, Institute of International Studies, University of California, ISBN 0-87725-166-5.
- ↑ Iliffe 2011, pp. 42–43; Derfler 2011, p. 81.
- ↑ Derfler 2011, p. 82.
- ↑ Iliffe 2011, p. 44.
- ↑ Iliffe 2011, p. 43; Derfler 2011, p. 81.
- ↑ Iliffe 2011, pp. 48–49; Derfler 2011, p. 85.
- ↑ Iliffe 2011, p. 50; Derfler 2011, p. 85
- ↑ African Concord (1990). The New Helmsmen. Concord Press, Ikeja, Lagos. 13 August 1990
- ↑ Pereltsvaig, Asya (16 June 2011). "Linguistic diversity in Africa and Europe – Languages Of The World". Archived from the original on 15 May 2012. Retrieved 4 July 2019.
- ↑ Iliffe 2011, p. 48
- ↑ Bilski, Andrew, "Broken Promises", Maclean, 6 September 1993
- ↑ Diamond, Larry; Kirk-Greene, Anthony; Oyeleye Oyediran (1997) Transition without End: Nigerian Politics and Civil Society Under Babangida, Vantage Publishers, ISBN 978-2458-54-6.
- ↑ Bilski, Andrew, "Broken Promises", Maclean, 6 September 1993.
- ↑ "The countries with the 10 largest Christian populations and the 10 largest Muslim populations". Pew Research Center. April 2019. Archived from the original on 18 January 2021. Retrieved 25 May 2020.
- ↑ Wiwa et al v. Royal Dutch Petroleum et al". Center for Constitutional Rights. Archived from the original on 26 March 2015. Retrieved 24 August 2016.
- ↑ Nigerian Lawyer: Abacha accounts apparently in Switzerland, Luxembourg, France, and Germany", AP press, 10 January 2000.
- ↑ Abdusalam Abubakar" Archived 4 May 2015 at the Wayback Machine, Encyclopædia Britannica Online, accessed 26 October 2012.
- ↑ Falola and Heaton, A History of Nigeria (2008) pp. 211–34.
- ↑ NASS confirms Sambo as vice president". The Nigerian Voice. 18 May 2010. Archived from the original on 5 August 2020. Retrieved 29 May 2011.
- ↑ Final Report" (PDF). EU Election Observation Mission Nigeria 2007. Archived from the original (PDF) on 16 February 2008. Retrieved 24 January 2008.
- ↑ "Nigeria Fact Sheet" (PDF). United States Embassy in Nigeria. Archived from the original (PDF) on 18 October 2020. Retrieved 23 September 2018.
- ↑ Nossiter, Adam (16 April 2011). "Nigerians Vote in Presidential Election". The New York Times. Archived from the original on 24 August 2019. Retrieved 17 April 2011.
- ↑ Akinlade, Muruf (18 May 2010). "National Assembly confirms Sambo as Vice President". MyOndoState.Com. Archived from the original on 27 April 2011. Retrieved 29 May 2011
- ↑ Udo, Bassey (14 May 2015). "Missing $20 bn: Sanusi faults Alison-Madueke, says audit report proves at least $18.5bn lost". Premium Times Nigeria. Archived from the original on 4 October 2022. Retrieved 5 October 2022.
- ↑ Nigeria election: Muhammadu Buhari wins". BBC.
- ↑ APC praises Jonathan for conceding defeat". The Nation. Archived from the original on 8 July 2015. Retrieved 4 April 2015.
- ↑ Obama praises Nigeria's president for conceding defeat". Vanguard. 1 April 2015. Archived from the original on 21 August 2019. Retrieved 4 April 2015
Ƙasashen Afirka |
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe |