Kagarko

Karamar hukuma ce a Nigeria

Kagarko karamar hukuma ce a jihar Kaduna, a Najeriya. Hedkwatarta tana cikin garin Kagarko. Ta mamaye yanki mai girman 2,356 km2 da yawan jama'a 239,058 dangane da ƙidayar 2006. Nasara Rabo ke jagorantar Ƙaramar hukumar. Lambobin tura saƙo zuwa yankin sune 802.

Kagarko

Wuri
Map
 9°27′N 7°41′E / 9.45°N 7.68°E / 9.45; 7.68
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar Kaduna
Labarin ƙasa
Yawan fili 1,864 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
62394-Leherketa_Nigerian_2007an
Kagarko post ofis
Open fields in kagarko
Shrubs acikin kagarko
A_bridge_on_a_flowing_river

Karamar hukumar Kagarko (Wogon) tana da iyaka da karamar hukumar Kachia a arewa, karamar hukumar Jaba daga gabas, jihar Neja zuwa yamma da kuma babban birnin tarayya Abuja a kudu.

Yaruka/Kabilu

gyara sashe

Mutanen dai manoma ne. Mutanen Batinor (Koro) sune ke da rinjaye a yankin. Sauran sun hada da Fulani, Gbagyi, Ham, Hausa da Adara . Suna aiki tukuru kuma galibi manoma, kusan kashi 70% na ginger da ake nomawa a jihar Kaduna daga Kagarko suke.

Sanannun mutane a Kagarko

gyara sashe
  1. Nenadi Usman. Tsohuwar sanatan a kudancin Kaduna kuma tsohuwar ministar kuɗi
  2. Caleb Zagi. Tsohon sanatan a kudancin Kaduna. #Muhammad Bello Umar Kagarko. Tsohon kwamishina na kana nan hukomomi kuma kwamishina na ilimi.

Kujerun gargajiya

gyara sashe

Kagarko ya ƙunshi sarakuna uku:

  1. Masarautar Kagarko : Mai martaba Sarkin Kagarko Alh. Sa’ad Abubakar, mai hedikwata a Garin Kagarko;

2. Jere Royaldom : Sarkin Jere, Marigayi Dr. Sa'ad Usman (OFR)

3. Koro masarautar : Ere-Koro, Ere Yohanna Akaito (JP), mai hedikwata a Kurmin Jibril (Maraban Kubacha) ;

Manazarta

gyara sashe