Maiduguri

Babban birnin jihar Borno

Maiduguri shine babban birnin Jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya Maiduguri shi ne birnin da yafi kowane birni wajen girma da yawan jama'a a arewa maso gabashin Najeriya. Allah yayi birnin yanada jama'a fiye da miliyan daya.[1] Birnin Maiduguri tsohon birni ne, an kafa shine a shekara ta alif daya da dari tara da bakwai (wato a shekara ta alif ɗari tara da bakwai 1907). Maiduguri ta kunshi unguwar Yerwa (Yerwa yana nufin alheri a harshen kanuri) ta yamma da kuma tsohuwar Maiduguri datake ta bangaren gabas.

Maiduguri

Wuri
Map
 11°50′N 13°09′E / 11.83°N 13.15°E / 11.83; 13.15
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Borno
Ƙaramar hukuma a NijeriyaMaiduguri (en) Fassara
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 1,197,497 (2009)
Labarin ƙasa
Altitude (en) Fassara 320 m
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1909 (Julian)
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
taswirar maiduguri
Maiduguri a wasu shekaru da suka wuce
Yara a Maiduguri

Birnin Maiduguri a nan ne fadar mai martaba Shehun Borno take sannan kuma ita ce babban birnin jihar inda fadar gwamnatin jihar Borno take.

Kasuwanci da Tattalin Arziƙi

gyara sashe
 
Sojan sakai a maiduguri
 
Yan kasuwa

Babbar kasuwan dake Maiduguri ita ce kasuwarl litinin [Monday Market] wadda take a tsakiyar birnin Maiduguri. Abubuwan cinikinsu sun haɗa da tufafi, kayan masarufi, kayan abinci, tukwane, bangaren motoci da babura, kaseti na CD da DVD, akwatin kallo, tangaraho, takalma da sauransu. Kananan kasuwanni a Maiduguri sun hada da kasuwan kwastam wanda yake tsakanin unguwar Gamboru da Gwange, kasuwar Budum, kasuwar tashan Baga wanda yayi suna wurin cinikayyan kifi da ake kamawa a garin Baga wanda yake dabda tafkin Cadi.

 
kilishin rakumi Wanda ake yi a maiduguri
 
Manoma

Yawancin mutanen dake garin Maiduguri dai manoma ne amma akwai 'yan kasuwa da dama da kuma ma'aikatan gwamnati. Manyan masana'antun Maiduguri sun hada da Maiduguri Flour Mills, kamfanin sarrafa Dalaram (wanda a halin yanzu ta dur'kushe), kamfanin Coca Cola, Borno Aluminium company, Kamfanin Alewa ta Haske da kuma kamfanin sarrafa takalma ta Natel. Akwai bankuna masu yawa a Maiduguri a kan titin Shehu Laminu Way. Yawancin bankunan suna da akwatin daukan kudi da kanka wato ATM.

Zirga-zirga

gyara sashe
 
Jirage
 
Manyan Tituna

Maiduguri tana da filin jirgin sama wanda ake kira Filin jirgin saman Maiduguri. Jiragen sama kan tashi a kowace rana daga Maiduguri zuwa Abuja da Lagos da sauran garuruwa dake cikin kasa da waje. Akwai kuma jiragen da suke jigilan daukan Musulmai zuwa Saudiya lokacin aikin Hajji. Ta fannin jiragen 'kasa kuwa Maiduguri tana da Makeken tashan jirgin kasa wanda aka fi sani da Railway Terminus Maiduguri. Tashan jirgin kasan tana dab da inda rikicin Boko Haram ya barke a shekara ta 2009 a unguwar goni damgari bayan kwatas. daukan kayan noma kamar gyada, Wake, da kuma dabbobi kamar Raƙuma, saniya daga Maiduguri zuwa kudancin Najeriya yana daya daga cikin manyan dilalan kafa layin jirgin 'kasa a Maiduguri.

 
Manyan Titunan Mota

Maiduguri tana da manyan titunan mota kamar su Sir Kashim Ibrahim Road, Shehu Laminu Way, Bama Road, Jos Road da Baga Road. Hanyoyin motan sun hada Maidguri da sauran Birane kamar Yola, Kano da Bauchi. Akwai kuma hanyoyi zuwa kasashen waje kamar Chadi, Nijar da Kamaru.

Ilimi da Makarantu

gyara sashe

Akwai jami'a a birnin Maiduguri wanda ake kira da Jami'ar Maiduguri. Jami'ar tana kan hanyar Bama Road. Kwasa-kwasan da ake karantarwa a jami'ar sun hada da ilmi aikin likita, ilmin injiniyarin, ilmin watsa labarai, ilmin harshen turanci da kuma ilmin addini da al'adu. Jami'ar Maiduguri tana da Asibitin koyarwa (wato Univesity of Maiduguri Teaching Hospital). Sa'annan akwai Jami'ar Jihar Borno da kuma makarantar politeknik a Maiduguri mai Suna Ramat Polytechnic. Sauran Makarantu zirfin ilmi sun hada da College of Agriculture, Sir Kashim College of Education da Mohammed Goni College of Islamic and Legal Studies. Sa'annan akwai makarantun sakandare da dama a Maiduguri.

Masaukin Baki

gyara sashe

Wuraren saukan baki a Maiduguri sun hada da Lake Chad Hotel, Dujima Hotel, Deribe Hotel, Ali Chaman Guest Inn da kuma Maiduguri International Hotel.

Nishadi da Wuraren Bude Ido

gyara sashe
 
wurin shakatawa
 
wajajen tarihi da shakatawa

Ba'ki a Maiduguri sukan iya ziyartan makeken kasuwan litanin, fadan mai girma shehun Borno da kuma gidan zoo na Kyarimi Park wanda yake tsakiyan birni Maiduguri.

Yawancin mazauna birnin Maiduguri Musulmai ne. Amma akwai mabiya addinin kirista da dama a garin. Akwai manyan majami'o'i a garin kamar babban majami'an dake kan titin Kiri Kasamma. Maiduguri yayi suna kwarai wajen karatun alkur'ani a inda dalibai dake dukkan fadin Najeriya suke zuwa garin don neman ilmi. Manyan masallatai a garin sun hada da masallachin Mai Deribe, masallacin Madinatu, Masallacin Kofar Shehu, Masallacin Indimi da Masallacin Ibrahim Saleh. Akwai shahararrun malaman addinin Musulunci da dama a Maiduguri. A shekara ta 2009, wani malamin addinin Muslunci wanda aka fi sani da Mohammed Yusuf ya tada fitina a garin a inda yake ikirarin yaki da gwamnati da kuma ilmin boko wanda a ganinsa yana lalata al'umma. Sanda aka yi wajen mako guda ana fafatawa tsakanin sojoji da 'yan sanda da kuma magoya bayan Mohammed Yusuf. Wannan tarzoma tayo sanadiyyar rasa rayuka da dama. Daga karshe jami'an gwamnati sun ci galaba a kan Mohammed Yusuf wanda sojoji suka cefke kuma suka dan'ka shi a hannun 'yan sanda. A hannun 'yan sandan Mohammed Yusuf ya rasu. 'Yan sanda sun yi ikirarin cewa ya rasu ne a yayin da ake bindige shi lokacin da yake kokarin kubucewa. Masu bin hakkin bil Adama sun yi harsashen cewa kisan gilla a kayi masa.


Manazarta

gyara sashe