Burutu
Burutu Karamar Hukuma ce ta Jihar Delta dake a kudu masu kudancin Nijeriya.[1] Tana nan a gabar tekun Niger-Delta. Burutu na da alaka da hanyoyin ruwa zuw tituna. Mafi akasarin mutanen wannan yanki sun fito ne daga harshen Ijo.
Burutu | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | jahar Delta | |||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 209,666 (2006) | |||
Labarin ƙasa | ||||
Altitude (en) | 1 m | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Lambar aika saƙo | 332105 | |||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Bayani
gyara sasheBirane da Kauyukan Burutu
gyara sasheKaramar Hukumar Burutu na da kananan hukumomi da suka hada da;[2]
- Burutu-Forcados: Burutu, Forcados, Keremo2
- Iduwun: Kolorugbene, Odimodi, Osamayigben Ogulagha:nBenibayo, Ogulagha, Yobebe, Yokrisobo
- Obatebe: Abadima, Okorogbene, Kalagfionene, Kenlogbene, Obatebe, Opuapale
- Ngbilebiri/Main: Agbodobiri, Akparegmobini, Amasuomo, Biokorgha, Egodor, Egologbene, Gbekebor, Kiagbo, New Town, Ngbilebiri, Ogbeingbene, Ogbolugbiri, Okrika, Yayogbene, Zion-Oyagbene.
- Operemor: Abadiama, Bolu-Ojobo, Bolou Ndoro, Egrangbene, Ekogbene, Ekumugbene, Ojobo, Rougbene.
- Seimibiri: Dunu-Ogusu, Edegbene, Nikorogha, Oboro, Ogbene, Okpokunon, Okuamo
- Toumo: Bolua-Tamigbe, Botu-Mangbebe, Bolu-Tebegbe, Douebido-zion, Founkoro-Gbene, Isreallo-zion, Ogbogbabene, Toru-Temigbe, Torugbene, Toubo Town.
Harkokin Kasuwanci
gyara sasheA farkon karni na 20, birnin ta fadada a dalilin ayyukan kamfanin Niger da kuma daga baya United African Company (UAC), wacce ke da harajin sufurin kayayyaki na kamfanin Niger (Niger Company) a Burutu.[3] Kafin farkon. karni na 20, tashar kamfanin na Niger na can a Akassa amma daga baya sun koma yammacin yankin izuwa Burutu zuwa kusa da Forcados. Sai daga baya Burutu ta fara aiki a matsayin tashar jirgin ruwa na sufurin kayayyaki na kamfanonin Niger da kuma UAC, suna jigilar kayayyaki daga jiragen ruwa zuwa garuwan yankunan arewacin Najeriya da yankunan Faransa ta River Niger da River Benue.[3]
A da tashan jirgin ruwan na Burutu na karkashin kulawar UAC,[4] amma daga baya ta koma karkashin tashar Nigeria Port Authority.[5]
Hanyoyin Waje
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ "Burutu | Nigeria | Britannica". www.britannica.com. Retrieved 2022-01-31.
- ↑ places (1970-01-01). "Towns & Villages in Burutu « Delta State « Nigeria". Towns & Villages. Retrieved 2022-01-31.
- ↑ 3.0 3.1 "Report". Lagos: Commission of Enquiry into the Disturbances Which Occurred at Burutu on 21 June 1947. 1948: 1. OCLC 34553671
- ↑ "An Ocean-going Vessel Alongside the Main Wharves of the United Africa Company's Private Port at Burutu, in Nigeria." Financial Times, 1 June 1954, p. 8. The Financial Times Historical Archive
- ↑ "Buxton, James. "Cargocats Revitalise Burutu." Financial Times, 18 Feb. 1976, p. 4. The Financial Times Historical Archive