Babura

Karamar hukuma ce a Najeriya

Babura ƙaramar hukuma ce dake a Jihar Jigawa, Arewa maso yammacin Najeriya. Babura ta kasance garinsu marigayi Alƙalin alƙalai justice Ɗahiru Mustafa da kuma marigayi Malam Lawan Saleh Dache Babura. Tana ɗaya daga cikin biranen jihar Jigawa sannan ta yi boda da Ɗambatta daga ɓangaren kudu. Garin Babura yanada tarihi sosai musamman bangaren sarauta. Sarki babura wanda ake yiwa lakabi da Mai cirimbi shine wanda ya kafa garin babura. Sarki ne mai Cikakken iko wanda yayi Gwagwarmaya da yake-yake da dama ciki har da bada kariya ga garin Kano zamanin da ake yaki tsakanin garin Kano da Damagaran din Nijar. Sarki Mai cirimbi yana da komai na sarauta kamar tambari fada da sauransu wukar yanka ce kadai yaqi karba saboda wasu dalilansa. Yanzu haka tsatson sarki Mai cirimbi sune suke sarautar Sarkin Gabas a garin Babura wanda yake matsayin babban dagachi.

Babura

Wuri
Map
 12°38′00″N 8°58′00″E / 12.6333°N 8.9667°E / 12.6333; 8.9667
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Jigawa
Labarin ƙasa
Yawan fili 992 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
babban masallaci a dutse


babura ɗaya ce daga cikin ƙananan hukumomi guda 27 a jihar Jigawa.

Manazarta

gyara sashe

[1] [2] [3]

  1. https://www.citypopulation.de/php/nigeria-admin.php?adm2id=NGA018002
  2. https://www.finelib.com/listing/Babura-Local-Government-Area/62476/
  3. https://www.rome2rio.com/s/Babura