Ingawa

Karamar Hukumar ce a jihar Katsina, Nigeria.

Ingawa Karamar hukuma ce a jihar Katsina a Najeriya . Hedikwatarta tana cikin garin Ingawa.

Ingawa

Wuri
Map
 12°38′23″N 8°03′01″E / 12.6397°N 8.0503°E / 12.6397; 8.0503
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
JihaJihar Katsina
Labarin ƙasa
Yawan fili 892 km²
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci

Garin Ingawa na da yanki na 892 km2 da yawan jama'a 2 a ƙidayar shekarar 2006. Kuma Shugaban Karamar Hukumar a halin yanzu shi ne Alhaji Labaran Magaji da kuma Hakimin hukumar a halin yanzu wato Alhaji Babangida Sule Abubakar Dambo Sarkin Fulani Dambo.

Lambar ofishin tura sakonni na yankin ita ce 823.[1]

Tarihi gyara sashe

Ingawa ta zama karamar hukuma ne a watan Mayun 1989. Ciyaman ne ke jagorantar harkokin karamar hukuma a hukumance. Mafi akasarin mazauna karamar hukumar Hausawa ne da Fulani. Muhimmin aikin su shine noma da kiwo.[2]

Haka kuma, A kan lambobin lasisin ababen hawa, an taƙaita Ingawa a matsayin NGW.[3]

An kafa hukumar ilimi ta Karamar Hukumar Ingawa a shekarar 1989 bayan kafa karamar hukumar Ingawa daga tsohuwar karamar hukumar Kankia.

Wadannan sun zama sakatarorin ilimi daga 1999 zuwa yau.

1. Alhaji Tukur Saude - 1999 – 2002

2. Alhaji Yusuf Bara'u - 2002 - 2012

3. Alhaji Abdu Ibrahim Yandoma - 2012 - Kwanan wata.[4]

Manazarta gyara sashe

  1. "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 2009-10-07. Retrieved 2009-10-20.
  2. "Katsina State- with History of Ingawa". Ingawa LGA. Retrieved 2013-01-04.
  3. "NGR - Nigeria - Where's That Vehicle Come From?". Retrieved 2013-01-04.
  4. "Ingawa LGA Educational Activities". Retrieved 2013-01-04.