Malumfashi
Malumfashi (ko Malum Fashi ) karamar hukuma ce a Jihar Katsina, Najeriya. Hedkwatar ta tana cikin garin Malumfashi.
Malumfashi | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jahar Katsina | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 674 km² | |||
Bayanan tarihi | ||||
Ƙirƙira | 1975 | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Tana da fadin kasa kimanin 674 km² da yawan mutum 182,920 a bisa ƙidayar 2006. Shugaban Ƙaramar hukumar na yanzu shine Alhaji Muktar Ammani sannan kuma Mai shari'a Saddiq Abdullahi Mahuta shine Galadiman Katsina kuma Hakimin Malumfashi.
YANAYIN GARIN
gyara sasheLokacin zafi yana kaiwa kimanin wata 1.9 a malumfashi, wanda yanayin zamin yana kaiwa 95°F sannan yanayin sanyi yana kaiwa kimanin watanni 2.7 wanda kimanin yana kaiwa 86°F a gaba daya shekara yanayi yana caccanzawa.
Lambar ofishin tura sakonni na yankin ita ce 822.[1]
Wakilin majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Malumfashi/Kafur shine Ibrahim Babangida Mahuta.[2]
Malumfashi tana da kyakkyawar mu'amala tsakanin al'ummar kiristoci da Musulmai Hausawa. Suna zaune lafiya da makwabtansu Hausawa da danginsu.
Fitattun mutane
gyara sashe- Mai shari’a Saddik Abdullahi Mahuta, wanda ya fi kowa dadewa a kan mulki a jihar Katsina, daga shekara ta alif 1991 zuwa shekara ta 2013 da kuma Galadiman Katsina na 11, Hakimin Malumfashi.
- Sunusi Mamman, Tsohon Vice Chancellor na Umaru Musa Yar'adua University and Sa'in Galadiman Katsina, daga ƙaramar hukumar Malumfashi.