Cross River
Jihar Cross River Sunan barkwancin jiha: Jihar birnin kwal. | ||
Wuri | ||
---|---|---|
![]() | ||
Ƙidaya | ||
Harsuna | Efik, Ejagham da Turanci | |
Gwamna | Benedict Ayade (PDP) | |
An kirkiro ta | 1967 | |
Baban birnin jiha | Calabar | |
Iyaka | 20,156km² | |
Mutunci 2006 (ƙidayar yawan jama'a) |
3,737,517 | |
ISO 3166-2 | NG-CR |
Jihar Cross River Jiha ce dake ƙasar Najeriya. Tana da yawan filin kasa kimanin kilomita araba’i 20,156 da yawan jama’a milyan uku da dubu dari bakwai da talatin da bakwai da dari biyar da sha bakwai (ƙidayar yawan jama'a shekara 2006). Babban birnin jahar ita ce Calabar. Benedict Ayade shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Ivara Esu. Dattijan jihar sun hada da: Gershom Bassey, Rose Okoji Oko da John Enoh.
Jihar Cross River tana da iyaka da misalin jihohi huɗu ne: Abia, Akwa Ibom, Benue kuma da Ebonyi.
Kananan HukumomiGyara
Jihar Cross River tanada Kananan hukumomi guda goma sha bakwai (17). Sune:
- Abi
- Akamkpa
- Akpabuyo
- Bakassi
- Bekwarra
- Biase
- Boki
- Etung
- Ikom
- Kalabar Municipal
- Kalabar ta Kudu
- Obanliku
- Obubra
- Obudu
- Odukpani
- Ogoja
- Yakuur
- Yala
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |