Kebbi

jihace a arewacin Nijeriya
(an turo daga Jihar Kebbi)

[1]

Kebbi


Wuri
Map
 11°30′N 4°00′E / 11.5°N 4°E / 11.5; 4
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Birnin, Kebbi
Yawan mutane
Faɗi 4,440,050 (2016)
• Yawan mutane 120.65 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 36,800 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi jihar Sokoto
Ƙirƙira 27 ga Augusta, 1991
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa Executive Council of Kebbi State (en) Fassara
Gangar majalisa Kebbi State House of Assembly (en) Fassara
• Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 860001
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-KE
Wasu abun

Yanar gizo kebbistate.gov.ng
Garejin motoci a kebbi
Lambar motar kebbi
Mutanen jihar kebbi
Seal of kebbi state
Floods in Kebbi State, Nigeria
Kogin kebbi

Jihar Kebbi jiha ce dake a ƙasar Najeriya. Tana da yawan faɗin ƙasa kimanin kilomita murabba’i 36,800 da yawan jama’a milyan uku da dubu ɗari shida da talatin da ɗari takwas da talatin da ɗaya (jimillar 2005). An samar da jihar Kebbi ne daga Jihar Sakkwato a ranar 27 ga Agustan shekarar 1991 a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida. Babban Birnin Jihar shi ne Birnin Kebbi. Jihar Kebbi ta kasu zuwa kananan hukumomi 21, da masarautu hudu (Gwandu, Argungu, Yauri da Zuru), da gundumomi 35. Jihar Kebbi ta samo sunan ta ne daga karni na 14 " MULKIN KEBBI " wanda ya kasance lardin tsohuwar daular Songhai. Musulunci shine addini mafi rinjaye. Jihar tana Arewa maso yammacin Najeriya, jihar Kebbi tana da fadin murabba'in kilomita 36,800. Jihar Kebbi tana da iyaka da jihar Sokoto a bangaren arewa maso gabas, jihar Zamfara daga gabas, jihar Neja ta bangaren yamma sannan kudu da jamhuriyar Nijar a bangaren yamma.

TATTALIN ARZIKI

gyara sashe

Jihar Kebbi tana da wuraren da ake amfani da shi wajen noma tun da yake tana da arzikin kasa mai yawa, filayen gonaki masu yawa da kuma rafuka masu bunkasa fannin tattalin arziki da ke samar da yanayi mai kyau.

Bisa wadannan dalilai, noma ya kasance babbar hanyar samun kudaden shiga a jihar, kuma shi ne kashin bayan tattalin arzikin jihar.
Manyan kayan abinci da ake nomawa a yankin sun hada da gero, Dawa, masara, rogo, dankalin turawa, shinkafa, wake, albasa da kayan lambu, sannan kuma ana samar da kayan amfanin gona da suka hada da alkama, waken soya, ginger, rake, gyada a jihar.  Hakazalika, ana samar da 'ya'yan itatuwa irin su mangwaro, kashu, Goba, da Gwanda a karkashin aikin gona.
Jihar Kebbi tana da Hukumar Bunkasa Aikin Gona ta Kebbi wadda ke da alhakin aiwatar da manufofinta na noma.

Jihar Kebbi tana da rafukan dasuke taimakawa wajen inganta tattalin arzikintav irin su Neja da Rima domin bunkasa ayyukan kamun kifi. Kamun kifi ya kasance daya daga cikin muhimman ayyukan mazauna jihar.

Har ila yau jihar ta shahara a bangaren kiwon dabbobi sun sanya jihar ta zama tushen albarkatun kasa

===MA'ADANAN KASA=== ma'adinai a jihar sun hada da farar ƙasa, gishiri, yumbu da gypsum.

Bikin kamun Kifi

gyara sashe

Wannan dai na daya daga cikin bukukuwan da suka fi shahara a nahiyar Afirka kuma ana gudanar da shi a duk shekara a a garin Argungu, jihar Kebbi ta Najeriya. Daya daga cikin bukukuwan sana’o’i shi ne bikin kamun kifi da al’adu na Argungu. An fara gudanar da bikin Argungu a matsayin babban biki a shekarar 1934, inda aka shirya shi domin tunawa da ziyarar Sarkin Musulmi, Malam Hassan Dan Muazu a garin Argungu. Har ya zuwa yanzu, taron na masunta na Gudana duk Shekara inda dubban mutane ke taruwa domin Aiwatar da bikin wasan kamun kifin.

Bikin kamun kifinl na Argungu hanya ce ta rayuwa ga al’ummar jihar Kebbi. Bikin yana kiyaye al'ada kuma yana inganta ta. Bikin na shekara-shekara yana faruwa ne al watan Fabrairu kuma yana nuna ƙarshen lokacin noma da kuma lokacin kamun kifi.

Bikin kamun kifi na Argungu na shekara-shekara ne da ke jan hankalin jama'a daga ko'ina cikin Najeriya da wajen kuma taron al'adu ne na kwanaki hudu da ke zuwa tare da bikin kamun kifi a kogin Matan Fada inda duk wani mai kamun kifi da ya kama kifi mafi girma yana samun lada.

Ana ba masuntan sa'a guda ne kawai don su su kamo mafi girman kifia wannan lokacin, kuma kusan masunta dubu ne suke shiga cikin kogin tare da kayan kamun kifinsu da tarunsu don kama kifi mafi girma daga cikin Kogin, ana harbaba bindiga ne dokln ba masunta damar shiga cikin kogin.

Bikin na shekara-shekara baya ga bikin kamun kifi kuma yana kunshe da abubuwan kade-kade, al'adu, da na wasanni.
Wannan wata shahararriyar gasar kamun kifi ce da aka saba gudanarwa duk shekara a jihar Kebbi, kuma wurin yawon bude ido ne inda dukkan masunta ke fara farautar kamun kifi na awa daya.
Kogin Matan Fada shi ne wurin da za a gudanar da gasar kuma yana a garin Argungu, wanda shi ne babban birnin masarautar Argungu, kuma ba wai kawai zai zama wurin shakatawa ba ne a lokacin bikin kamun kifi na Argungu, har ma a matsayin al'adun gargajiya na mutanen Kabawa da ke da dimbin tarihi.  su ne manyan kabilun da ke zaune a masarautar Argungu.
Babu wani hani ga dukbwanda zai iya shiga gasar,
'Yan kallo suna da yawa sosai wanda ya haifar da haɓakar tattalin arzikin jama'a sakamakon fa'idar kasuwanci da ke da alaƙa da bikin.


cikin garin kebbi

Jihar Kebbi tana da iyaka da jihohi huɗu (4), sune: Sokoto, Zamfara da kuma jihar Niger.

Taswirar Jihar Kebbi
Makarantar allo a kebbi

[2]

Kananan Hukumomi

gyara sashe

Jihar Kebbi na da ƙananan hukumomi guda ashirin da ɗaya (21), da masarautu huɗu, su ne; (Masarautar Gwandu, MasarautarArgungun, Masarautar Yauri da Masarautar Zuru), tana kuma da gundumomi (35). Ƙananan hukumomin su ne:


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara


Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-06-18. Retrieved 2023-06-18.
  2. https://www.britannica.com/place/Kebbi-state-Nigeria