Jihar Zamfara
Sunan barkwancin jiha: Noma shi ne girmanmu.
Wuri
Wurin Jihar Zamfara cikin Nijeriya.
Ƙidaya
Harsuna Hausa, Fulani
Gwamna Bello Matawalle (PDP)
An kirkiro ta 1996
Baban birnin jiha Gusau
Iyaka 39,762km²
Mutunci
2011 (jimilla)

3,838,160
ISO 3166-2 NG-ZA

Jihar Zamfara Jiha ce a ƙasar Najeriya. Tana da yawan fili kimanin kilomita murabba’i 39,762 da yawan jama’a 3,838,160 (milyan uku da dubu dari takwas da talatin da takwas da dari daya da sittin) (jimilar shekara 2011). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Gusau. Bello Matawalle shi ne gwamnan jihar tun hukuncin da kotu ta yanke akan APC, shine ya bashi damar zama gwamnan ta a shekara ta 2019 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Mahadi Ali Gusau. Dattiban jihar su ne: Ahmad Rufai Sani, Mamuda Aliyu Shinkafi, AbdulAziz Yari, Hassan Nasiha, Sahabi Liman Kaura, Mansur Dan'Ali, Kabir Garba Marafa da Tijjani Kaura.

Tambarin Gwamnan jihar Zamfara
tambarin jihar zamfara

Tarihin ZamfaraGyara

Asalin Zamfarawa

 
mutanen zamfara sun kasance maharba a lokacin baya

Zamfara ta kasance dai daga ciki masarautun asali na Hausawa. Ta kasance ana lissafata dai daga cikin Banza Bakwai wadanda ba Hausawan asali ne ba. Dalilin hakan shine, ana ganin Bare-Bari ne asalin Zamfara. Sarkin musulmi Muhammadu yana ganin Zamfarawa sun samu asaline daga uba Bakatsine da uwa Bagobira. To su Zamfarawa suna kafa asalinsu daga Maguzawa maharba wadanda sun zauna a yankin kasar Kano kafin zuwan Bagauda tun kafin zuwan Barbushe a Dutshen Dala. Anan zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa Hausawa ne na asali tun can azal. Zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa dai asalinsu maharba ne daga Maguzawa. Watakila sun samu tasirin Bare- Bari a farkon tarihinsu ko koma a ce Bare-bari na asalin sarautar Zamfara. Tarihin ƙauyen Zamfara ya samo asalki ne daga mutum Na farko da ya fara zama a garin, daga garin ZAMFARA wanda ake kira da BAWA. Shi yasa ake kiran garin da suna Zamfara. Farkon fadar saurautan an rusa ta. Garin ya haɗa iyakoki da Rogo sabon gari da kuma Tsohuwar Rogo ta gabas, Bari da Kaduna daga gefen yamma, Kaduna daga Kudu da Bari da Tsohuwar Rogo ta arewa.[1]

Ana ganin Zamfarawan asali wasu irin manya-manyan mutane ne,a takaice dai Samudawa ne. Dakka, sarkin Zamfara na farko kamar dai Barbushe yake, mutun ne maitsananin girma da karfi da jarunta. Akwai wasu manya- manyan kaburbura guda shida a Dutsi wadanda akace kaburburan sarakuna Zamfara ne na asali. Sabo da girman kaburburan ana kiransu da kabuburan Samudawa. Ga alamu Zamfarawa asali na da garma jiki sosai.

Birnin Zamfara

 
dotsen kwatarkwashi

Zamfarawa sun fara kafa garinsu na farko ne mai suna Dutsi a kasar Zurmi ta yanzu. Don haka har yau Sarkin Zurmi na amsa sunan Sarkin Zamfara. Ance Zamfarawa saida suka kwashe shekara bakwai ba su nada sarki ba a Dutsi daga nan sai suka nada sarkinsu na farko mai suna Dakka.Don haka Sarkin Zamfara ana masa take da gimshikin gidan Dakka. Sarakuna hudu ne suka gaji Dakka a Dutsi. Daga nan sai sarauniyar Yar’Goje.

 
Zamfara

Daga Dutsi sai Zamfarawa suka yi tafiyar kamar mil takatin akan gulbin Gagare kusa da garin Isa na yanzu suka kafa wani sabon gari mai suna Birnin Zamfara. Ance Sarkin Zamfara na bakwai mai suna Bakurukuru ya kafa birnin. Amma wasu masana tarihi sun hakikan ce cewa sarakuna ashirin da uku ne aka binne a garin Dutsi don haka ba dai sarki na bakwai ba wanda ya kafa Birnin Zamfara.Zamfarawa sun gina garinsu wanda ya habaka sosai. Sun katange shi da ganuwa.Har yanzu akwai kufan tsohon garin akwai rusashiyar ganuwa mai tsawon mil goma-sha-uku da kofofin gari hamsin. A nan zamu iya fahimtar cewa Zamfarawa sun kafa garinsu na biyu wanda ya kasance babbar cibiyar mulkin Zamfara. Sannan garin ta samu arziƙin masarrafofin zamani irinsu Makarantun Boko, islamiyya, rijiyoyi da kuma Burtsatse da dai sauransu.[1]Ofishin siyasa ta mata an buɗeta ne a garin zamfara a shekarsr 2007. [2]

Kananan hukumomiGyara

 1. Anka
 2. Bakura
 3. Birnin-Magaji/Kiyaw
 4. Bukkuyum
 5. Bungudu
 6. Gummi
 7. Gusau
 1. Kaura-Namoda
 2. Maradun
 3. Maru
 4. Shinkafi
 5. Talata-Mafara
 6. Tsafe
 7. Zurmi

BibilyoGyara

 • Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4.
 • Bello, Ahmadu, Sir, 1910-1966. (1999). Alhaji Sir Ahmadu Bello, Sardauna of Sokoto : his thoughts and vision in his own words : selected speeches and letters of the great leader. Nchi, Suleiman Ismaila., Mohammed, Samai̕la Abdullahi. Makurdi: Oracle. ISBN 978-34637-2-1. OCLC 44137937.
 • G.karaye, Ibrahim. J. Shea, Philip. History of karaye. ISBN 978125341


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara

ManazartaGyara

 1. 1.0 1.1 G.karaye, Ibrahim. J. Shea, Philip. History of karaye. p.71 ISBN 978125341
 2. Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. p.164 ISBN 978-978-906-469-4.