Bakori
Bakori karamar hukuma ce dake Kudancin Jihar Katsina a Najeriya. An kirkiri karamar hukumar a ranar 15 ga watan Mayu, shekara ta alif Dari tara da tamanin da tara 1989, wanda gwamnan jihar Katsina a lokacin mulkin soja wato Major General Lawrence Onoja ya kirkire ta. Bakori na da fadin kilomita 679kmsq da yawan jama'a kimanin mutum 641,576 a kidayar shekarar 2006. [1]Garin nada postal code 831.[2]
Bakori | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jiha | Jihar Katsina | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 679 km² | |||
Bayanan tarihi | ||||
Ƙirƙira | 1989 | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Tarihi gyara sashe
An kirkiri karamar hukumar Bakori a ranar 15 ga watan Mayu, na shekara ta alif 1989.
Labarin Kasa gyara sashe
Bakori ta hada iyaka da kananan hukumomin Danja, Malumfashi, Kankara da kuma Funtua.
kauyukan Bakori gyara sashe
Akwai kauyuka da yawa a karkahin karamar hukumar Bakori, wanda suka hada da:
Barde
Kakumi
Kandurawa
Jargaba
Gazara
Dawan Musa
Kabomo
Guga
Kurami
Magaji Rafin kanya
Tattalin Arziki gyara sashe
Noma shine al'amari mafi amfani ga mutanen Bakori, sukan noma masara, shinkafa, dawa,farin wake da waken suya. kiwo wani abu ne mai muhimmanci a yanki wanda mafi akasarin mazajen garin makiyaya ne da manoma. daga nan sai harkar kasuwanci wanda ke taka rawan gani wajen cigaban garin da kasuwanni kaman Kasuwar Sama.
Sanannun Mutanen Bakori gyara sashe
Senator Mohammad Tukur Limann - tsohon shugaban ma su rinjaye na majalisar dattawan kasa wato majority leader. No
Manazarta gyara sashe
Hanyoyin hadi na waje gyara sashe
https://web.archive.org/web/20180413051419/http://www.bakorilga.kts-ng.org/