Dambatta
Danbatta (ko Dambatta ko Damrta ) karamar hukuma ce a jihar Kano, Najeriya. Tana da nisan mil 49 daga arewacin birnin Kano a kan iyakar Arewa da jihar Kano da jihar Jigawa.Tana da hedikwata a garin Danbatta, dake kan babbar hanyar A2.
Dambatta | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | jihar Kano | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 732 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Yana da girman yanki daya kai kimanin 732km2 da yawan jama'a 2 a ƙidayar shekarar 2006.Ta yi iyaka da arewa da gabas da kananan hukumomin Kazaure da Babura na jihar Jigawa, sannan daga kudu da yamma ta yi iyaka da kananan hukumomin Minjibir da Makoda na jihar Kano.
Garin shine wurin Kwalejin Aikin Gona ta Audu Bako (ABCOA)[1]da Makarantar Ungozoma ta Jihar Kano. Sannan gida ne na shiyya ta uku na hukumar kula da asibitocin jihar Kano (HMB), ofishin shiyya na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano (MOE), kantin magani na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano (MOH), ofishin shiyya na aikin gona na jihar Kano. da Hukumar Raya Karkara (KNARDA) da Ofishin Shiyya na Hukumar Injiniya da Gine-gine ta Jihar Kano (WRECA).
Lambar gidan waya na yankin ita ce 702.[2]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Steve Packer; Pius Elumeze; M.B. Shitu (October 2006). "State Educational Sector Project: Institutional Assessment - Kano State" (PDF). ESSPIN. Archived from the original (PDF) on 2011-07-26. Retrieved 2010-05-16.
- ↑ "Post Offices - with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on November 26, 2012. Retrieved 2009-10-20.
Kananan Hukumomin Jihar Kano |
Dala | Kano | Kumbotso | Nasarawa | Rimin Gado | Tofa | Doguwa | Tudun Wada | Sumaila | Wudil | Takai | Albasu | Bebeji | Rano | Bunkure | Karaye | Kiru | Kabo | Kura | Madobi | Gwarzo | Shanono | Dawakin Kudu | Tsanyawa | Bichi | Dambatta | Minjibir | Ungogo | Gezawa | Gabasawa | Bagwai | Gaya | Dawakin Tofa | Warawa | Fagge | Gwale (Kano) | Tarauni | Ajingi | Garko | Garun Mallam | Rogo | Makoda | Kibiya | Kunchi |