Dandume
Dandume (ko Dan Dume ) karamar hukuma ce a cikin jihar Katsina, Najeriya. Hedikwatarta kuma tana cikin garin Dandume da ke yammacin yankin. a11°27′30″N 7°07′37″E / 11.45833°N 7.12694°E.
![]() | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Jahar Katsina | |||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 145,323 (2006) | |||
• Yawan mutane | 344.37 mazaunan/km² | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 422 km² | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |


Tana da yanki na kimanin murabba'in km 422, da yawan jama'a 145,739 a ƙidayar shekara ta 2006. Sannan kuma mutanen karamar hukumar dandume suna gudanar da ayyukan noma, kiwo da kasuwanci. Mutanen karamar Dandume mutane ne masu al’adu iri ɗaya. Kuma Allah ya albarkacesu da masu ilimi boko da na zamani. Kama daga mahaddata Al Qur'ani Mai girma, karatun littattafai na Hadithi, Fikihu, larabci da sauransu. Haka bangaren karatun boko ma ba'a barsu a baya ba inda suke da masu Difloma, NCE, Digiri, Mastas, PhD har ma da Professor.
Lambar gidan waya na yankin ita ce 830.[1]
Karamar Hukumar Dandume ta jahar Katsina tana da Mazaɓu guda goma sha ɗaya (11) a karkashinta.
Ga jerin sunayen su kamar haka;[2]
- Dandume A
- Dandume B
- Dantankari
- Magaji wando A
- Magaji wando B
- Mahuta A
- Mahuta B
- Mahuta C
- Nasarawa
- Tumburkai A
- Tumburkai B
By Yusuf Sahabi Badole
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Post Offices- with map of LGA". NIPOST. Archived from the original on 2009-10-07. Retrieved 2009-10-20.
- ↑ https://nigeriadecide.org/polling_unit_category.php?state=Katsina&lga=Dandume