Ebonyi
Jihar Ebonyi Sunan barkwancin jiha: Gishirin Al'ummar. | ||
Wuri | ||
---|---|---|
![]() | ||
Ƙidaya | ||
Harsuna | Igbo, Turanci | |
Gwamna | David Umahi (PDP) | |
An kirkiro ta | 1996 | |
Baban birnin jiha | Abakaliki | |
Iyaka | 5,533km² | |
Mutunci 2006 (ƙidayar yawan jama'a) |
2,176,947 | |
ISO 3166-2 | NG-EB |
Jihar Ebonyi Jiha ce dake a kudu maso gabas a ƙasar Najeriya. Tana da yawan fili kimani na kilomita murabba’i 5,533 da yawan jama’a miliyan biyu da dubu dari da saba'in da shida da dari tara da arba'in da bakwai (ƙidayar yawan jama'a shekara 2006). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Abakaliki. David Umahi shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Eric Kelechi Igwe. Dattiban jihar su ne: Sam Egwu, Sonni Ogbuoji da Joseph Ogba.
Jihar Ebonyi tana da iyaka da misalin jihhohi hudu su ne: Jihar Abia, Jihar Benue, Cross River kuma da Jihar Enugu.
Kananan HukumomiGyara
Jihar Ebonyi nada adadin Kananan hukumomi guda goma sha uku (13). Wadanda Sune:
- Abakaliki
- Afikpo ta Arewa
- Afikpo ta Kudu (Edda)
- Ebonyi
- Ezza ta Arewa
- Ezza ta Kudu
- Ikwo
- Ishielu
- Ivo
- Izzi
- Ohaozara
- Ohaukwu
- Onicha
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |