Abuja

Babban birnin tarayya

Abuja ne babban birnin tarayyar. Birni ne babba mai girman gaske, birnin ya koma na tarayya ne tun a lokacin mulkin Babangida a shekarar alif ɗari tara da casa'in da ɗaya (1991) wanda kafin lokacin birnin tarayyar yana a birnin Legas dake kudu maso yammacin Najeriya take. Birnin Abuja ya kasance birni ne gagara-misali saboda birnin ya ƙunshi abubuwa da dama wanda ido ne kadai zai iya tabbatar da haka. Manƴan Ma'aikatu, Makarantu,filayen jiragen sama, da filin wasa Baba. a dai sauran manya-manyan ma'aikatun gwamnati wanda suke juya akalar ƙasar baki ɗaya. A cikin birnin Abuja akwai mutane a kalla 776,298 a kiɗayar shekarar 2006, kasan cewar birnin na tarayya[1] ne wato ya tara duk jinsin mutane da kabilun dake Nijeriya gaba daya, ko wacce jiha a Nijeriya tana da wakilai a sassa daban-daban a cikin Abuja domin ganin sun wakilci jihar su a fage da dama don cigaban jihar su.A cikin birnin Abuja akwai wuraren shakatawa da dama ko wuraren bude ido musamman ga baki, wadanda suke muradin kashe kwarkwatar ido ta fagen kallon abubuwan ban al'ajabi, da debe kewa.

Globe icon.svgAbuja
The National Assembly Globe.jpg

Wuri
 9°03′20″N 7°29′29″E / 9.0556°N 7.4914°E / 9.0556; 7.4914
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
First-level administrative country subdivision (en) FassaraFederal Capital Territory (en) Fassara
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 1,235,880 (2011)
• Yawan mutane 1,733.35 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 713,000,000 m²
Altitude (en) Fassara 360 m
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1828
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Wasu abun

Yanar gizo fcta.gov.ng
Wannan alamar launin jan shine sashin Abuja acikin taswirar
Shugaban Nageriya Muhammadu Buhari
kofar Abuja
Wannan ita ce kofar shiga birnin tarayya Abuja
Masallacin Abuja
Wannan shine babban Masallacin Abuja
Majamiar Abuja
Wannan babban Majami'ar Abuja kenan
Abuja
Babban filin tashi da saukar jiragen sama na abuja
Tambarin gwamnatin Nigeria
Tambarin gwamnatin Nijeriya

.

Ƙananan hukumomiGyara

Babban Birnin tarayya Abuja nada kanan hukumomi guda Shida (6)

1.Abaji

2.Garki

3.Bwari

4.Gwagwalada

5.Kuje

6.Kwali[2]

SASSAN ABUJAGyara

Abuja tana da sassa wato (districts) da dama tun daga Phase 1 har zuwa phase 3 sune kamar haka: [3]

SASSA NA PHASE 1Gyara

 • Central cadastral zone A00
 • Garki I District cadastral zone A01
 • Wuse 1 District cadastral zone A02
 • Garki II District cadastral zone A03
 • Asokoro cadastral zone A04
 • Maitama Districts cadastral zone A05
 • Maitama cadastral zone A06
 • Wuse II District cadastral zone A07
 * Wuse II cadastral zone A08
 • Guzape District zone A09

SASSA NA PHASE 2Gyara

 • kukwuaba cadastral zone B00
 • Gudu cadastral zone B01
 • Durumi cadastral zone B02
 • Wuye cadastral zone B03
 • Jabi cadastral zone B04
 • Utako cadastral zone B05
 • Mabushi cadastral zone B06
 • Jahi cadastral zone B08
 • Kado cadastral zone B09
 • Dakibiyu cadastral zone B10
 • Kaura cadastral zone B11
 • Duboyi cadastral zone B12
 • Gaduwa cadastral zone B13
 • Dutse cadastral zone B14
 • Katampe Ext cadastral zone B19

SASSA NA PHASE 3Gyara

 • Institution and Research Cadastral Zone C00,
 • Karmo Cadastral Zone C01,
 • Gwarimpa Cadastral Zone C02.
 • Dape Cadastral Zone C04,
 • Kafe Cadastral Zone C05
 • Nbora Cadastral Zone C06,
 • Galadimawa Cadastral Zone C07,
 • Dakwo Cadastral Zone C08,
 • Lokogoma Cadastral Zone C09,
 • Wumba Cadastral Zone C10,
 • Idu Industrial Cadastral Zone C16

Manyan wurare a AbujaGyara

 • Gidan Shugaban kasa (Villa)
 • Majalisar Dattawa
 • Majalisar Wakilai (NASS)
 • Babban kotun koli (supreme court)
 • Babban Bankin Nijeriya (CBN)
 • Babban ofishin sojoji
 • Babban ofishin yan sanda na kasa
 • Ma'aikatar sufuri ta kasa
 • Babban ofishin kwastam na kasa
 • Ofishin gamayyar Afrika (ECOWAS)
 
Ginin majalissar wakilai ta abuja

Wajen GariGyara

Garuruwan da suke waje da birnin Abuja[4]

 • Dawaki
 • Gwagwalada
 • Karu
 • Kubwa
 • Mpape
 • Nyanya
 
Nicon luxury hotal abuja
 
Sitadiyo ta kallo a Abuja

Chanjin yanayi a sashen AbujaGyara


Ruwan sama a Abuja yana farawa ne daga watan Aprilu sannan ya kare a watan October, a yayin da zafin hasken rana yake kaiwa makin 28 °C (82.4 °F) zuwa 30 °C (86.0 °F) sannan kuma sanyin dare a maki mafi karanci yana kaiwa 22 °C (71.6 °F) zuwa 23 °C (73.4 °F). Amma a lokacin rani, zafin hasken rana a bisa maki mafi girma yana kaiwa 40 °C (104.0 °F) amma yanayin yana sauki da dare akan makin ma'aunin celcius 12 °C (53.6 °F). har zuwa karshen dare yana kaiwa 30 °C (86.0 °F). wannan shine adadin makin sauyin yanayi da sashin birni Abuja ke fuskata a takaice.

 
Ofishin Majalisar Wakilai

'

 
Wannan dutsen zuma kenan a yankin Abuja

SadarwaGyara

Tashoshin Gidan Radio a yankin AbujaGyara

 • 88.9 - Brila FM (Abuja) - sports
 • 92.1 - Vision FM
 • 92.9 - Kapital FM
 • 93.5 - ASO Radio
 • 94.7 - Rhythm FM (Abuja)
 • 96.9 - Cool FM (Abuja)
 • 98.3 - Hot FM (Abuja)
 • 99.5 - Wazobia FM (Abuja)
 • 99.9 - Kiss FM (Abuja)
 • 100.5 - RayPower FM (Abuja)
 • 104 - Love FM (Abuja)
 • 95.1 - Nigeria Info
 • 106 - WE FM

Wikimedia Commons on Abuja

ManazartaGyara

 1. "Tarihin kafuwar Najeriya tun shekaru aru-aru" http://www.bbc.co.uk/hausa/news/2010/09/100914_early_history_nigeria50.shtml
 2. https://nigeriazipcodes.com/4049/local-government-area-in-fct/
 3. [[http://abuja-ng.com/contactus.html
 4. https://www.villaafrika.com/fct-abuja-city-profile/