.

Yobe state railway
Globe icon.svgYobe
Yobe State Flag.png
Tulutulu in yobe state Nigeria.jpg

Suna saboda Komadugu Yobe
Wuri
Nigeria Yobe State map.png
 12°00′N 11°30′E / 12°N 11.5°E / 12; 11.5
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Damaturu
Yawan mutane
Faɗi 3,294,137 (2016)
• Yawan mutane 72.4 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 45,502 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Komadugu Yobe
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Jihar Borno
Ƙirƙira 27 ga Augusta, 1991
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa executive council of Yobe State (en) Fassara
Gangar majalisa Yobe State House of Assembly (en) Fassara
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-YO
Wasu abun

Yanar gizo yobestategov.com
yobe state logo
Yobe state government
Yobe river
yobe village
yobe station
Yobe river transportation

.

Yobe ta kasance ɗaya daga cikin jerin jihohin shiyyar arewa maso gabashin Najeriya. Tana da yawan fili kimanin kilomita arabba’i 45,502 da yawan jama’a miliyan ɗaya da dubu ɗari huɗu da sha ɗaya da ɗari huɗu da tamanin da ɗaya (a ƙidayar yawan jama'a na shekarar 1991). Babban birnin tarayyar jihar shi ne Damaturu. Mai Mala Buni shi ne gwamnan jihar tun zaɓen shekara ta 2015 zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Idi Barde Gubana. Jihar Yobe dai tana da shiyyoyi guda uku: shiyyar gabas, kudu da kuma arewa. 'yan majalisar Dattijan jihar su ne: Ahmed Ibrahim Lawan mai wakiltar shiyyar arewaci, Ibrahim Gaidam shiyyar gabashi da Mohammed Ibrahim Bomai shiyyar kudanci.

yobe a wani karni na baya

Jihar Yobe tana da iyaka da jihohi huɗu, su ne: Bauchi, Borno, Gombe da kuma Jigawa. Tana kuma miyake da jamhuriyar ƙasar Nijar.

Duwatsu masu ban sha'awa na yobe

TarihiGyara

An ƙirƙiri jihar Yobe ne a ranar 27 na Agustan 1991.An ciro ta ne daga jikin jihar Borno a zamanin mulkin Ibrahim Badamasi Babangida kuma an yi hakan ne don a sauƙaƙa sha'anin tafiyar da mulki a yankin. Ranar 14 Mayu 2013, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya rattaba dokar ta ɓaci a jihar Yobe da Borno da kuma Adamawa. Saboda harin ta'addanci na kungiyar Boko Haram. Abubakar Shekau, shugaban ƙungiyar ta Boko Haram, haifaffen ƙauyen Shekau ne na jihar Yobe.

Kananan hukumomiGyara

Yobe tana da ƙananan hukumomi goma sha bakwai sun haɗa da:

HarsunaGyara

Waɗannan su ne harsunan mutanen Jihar da kuma ƙananan hukumomin da ake samun su:[1]

Kananan Hukumomi Harsuna
Bade Bade; Duwai
Bursari Bade
Damaturu Yerwa Kanuri; Karaikarai
Damagum Karaikarai
Fika Bolewa; Karaikarai; Ngamo
Fune Karaikarai
Geidam Yerwa Kanuri
Gujba Yerwa Kanuri
Gulani Maaka
Jakusko Bade
Nangere Karaikarai
Nguru Yerwa Kanuri; Hausa; Bade
Potiskum Karaikarai; Ngizim
Tarmuwa Fulani, kanuri
Yunusari /yusufari/ machina Kanuru

Sauran harsunan da ake samu a jihar Yobe sun hada da Bura-Pabir, Manga Kanuri, da kuma Zarma.[1]

Fitattun mutaneGyara

 • Usman Albishir - (15 Yuni 1945 – 2 Yuli 2012) tsohon sanata kuma shugaban majalisar dattawa maras rinjaye
 • Mai Mala Buni - (born 11 Nuwamba 1967) dan siyasa, tsohon sakataren jam'iyyar APC na kasa kuma Gwamnan jihar Yobe na yanzu.
 • Ibrahim Gaidam, tsohon gwamnan jihar Yobe kuma a yanzu dan majalisar dattawa mai wakiltar shiyyar gabashin jihar a fadar gwamnatin tarayya.
 • Buba Galadima - Dan siyasa kuma sakataren kasa na jam'iyyar Congress for Progressive Change (CPC).
 • Bukar Ibrahim - (shekarar haihuwa Aktoba 1950) tsohon gwamnan jihar Yobe kuma tsohon Dan takarar shugabacin kasa a jam'iyyar NNPP a shekarar 2007.
 • Khadija Bukar Abba Ibrahim - (shekarar haihuwa 6 Janairu 1967) matar tsohon gwamnan jihar Yobe Bukar Abba Ibrahim, tsohuwar 'yar majalisar wakilai na tarayya kuma Ministar kasa mai kula da harkokin waje karkashin jagorancin Muhammadu Buhari
 • Ahmed Ibrahim Lawan - sanata tun daga shekarar 1991 kuma shugaban majilisar dattijan Najeriya a yanzu kuma shi ne mutum na 9 a shugabannin majilisar kasar.
 • Ibrahim Talba - Dan siyasa kuma tsohon babban sakataren gwamnati a fadar shugaban kasa lokacin mulkin Olusegun Obasanjo kuma Ciroman masarautar Tikau
 • Adamu Waziri - (shekarar haihuwa 14 Satumba 1952) Dan siyasa kuma tsohon Dan takarar gwamnan jihar Yobe a karkashin jam'iyyar PDP kana tsohon ministan 'yan sanda na kasa kuma tsohon ministan jami'an kula da lafiyar hanya
 • Jamila Babayo - (shekarar haihuwa 17 May, 1983) marubuciya ce da ta kasance mace ta farko a shiryar arewa maso gabashin Najeriya da ta lashe gasar rubutu na mata zallah na BBC Hausa.

ManazartaGyara

 1. 1.0 1.1 "Nigeria". Ethnologue (22 ed.).


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara