Kogi

Karamar hukuma a Jihar Kogi, Najeriya

Kogi karamar hukuma ce a jahar Kogi, Najeriya mai iyaka da jahar Neja da Kogin Neja ta yamma, Babban birnin tarayya a arewa, jihar Nasarawa a gabas da Kogin Benuwai zuwa mashigar ta da Nijar ta kudu. Hedkwatarta tana cikin garin Koton Karfe (ko Koton Karifi) akan babbar hanyar A2.