Duniya
The Earth seen from Apollo 17.jpg
inner planet
bangare naEarth-Moon system Gyara
farawa4540 million years BCE Gyara
name in kanaちきゅう Gyara
named afterƘasa (shinfidar ƙasa), dirt Gyara
wuriinner Solar System Gyara
located on terrain featurecircumstellar habitable zone Gyara
coordinates of easternmost pointno value Gyara
coordinates of northernmost point90°0′0″N 0°0′0″E Gyara
coordinates of southernmost point90°0′0″S 0°0′0″E Gyara
coordinates of westernmost pointno value Gyara
highest pointMount Everest, Chimborazo Gyara
lowest pointChallenger Deep Gyara
studied byEarth sciences, Ilmin duwatsu, geophysics Gyara
maƙirƙiri Gyara
catalog code806.4616.0110 Gyara
parent astronomical bodyRana Gyara
type of orbitheliocentric orbit Gyara
dissolved, abolished or demolishedunknown value Gyara
tutaflag of the Earth Gyara
has qualityEarth mass, Earth's magnetic field, planetary habitability Gyara
manifestation ofopen system Gyara
notationEarth symbol Gyara
opposite ofsky Gyara
shapegeoid Gyara
geography of topiclabarin ƙasa Gyara
tarihin maudu'ihistory of the world, history of Earth Gyara
WordLift URLhttp://data.thenextweb.com/tnw/entity/earth Gyara

Duniya halitta ce daga cikin dimbin duniyoyin dake cikin sararin samaniya. Hakika wannan duniya da muke ciki yar karama ce idan aka kwatanta ta da sauran duniyoyi kamar duniyar Jupiter. Duniyar da muke ciki itace ta uku a nisa tsakaninta da Rana daga cikin abinda ake kira wato falakin duniyoyi da turanci kuma solar system, Kuma ita kadaice duniya a yanzu wacce ake samun halittu masu rai saboda wasu dalilai kaman... i). Ita kadaice ruwa ke gudana a cikinta, a nau'uka uku, ruwa (liquid), qanqara (solid) da raba' (gas) wanda ke gudana a koramu da Tekuna. Amma sauran duniyoyi basuda ruwa. ii). Ita kadaice ke da qasa (soil) wacce ke amintar tsirowar tsirrai (plants). iii). Ita kadaice duniya da ke da iska wacce ke amintar rayuwa ta mutane, dabbobi da kuma tsirrai.

sauran duniyoyin ko Iska babu a cikinsu. ballantana har akai ga samun abu mai rai.

Hakika Allah shine mahaliccin komai shi kadai ne yasan abinda ya dace da Bayinsa shi yasa ya zabar mana wannan duniya domin ita kadaice za a iya rayuwa aciki.

Duniyoyi
wannan sune duniyoyin dake cikin sararin subuhana wato Solar system

Zuwan dan adam sararin samaniya; abu mai yiwuwa da mara yiwuwa [1]

Fannin ilimin Sararin Samaniya Astronomy na daga cikin abubuwan da suka fi kayatar da ni, da wasu dimbin jama’a da nake da yakinin hakan su ma yana kayatar da su. Sai dai ba zai yiwu lokaci daya a gama fasaltawa mutum irin dimbin abubuwan mamaki da Allah Ta’ala Ya taskance a cikin sararin samaniya ba. Don haka, na hakaito mana wani dogon jawabi da wani shahararren masanin sararin samaniya mai suna Edward Tellar ya yi, mai cike da abubuwa muhimmai a shekarar 1961, dangane da tafiya zuwa sararin samaniya. A cikin jawabinsa ya fadi abin da yake ganin zai iya yiwuwa, da abin da yake ganin ba zai yiwu ba.Da farko ya yi hasashen cewa daga shekarar da ya yi bayanin a wancan lokaci,wato 1961, ba za a kai shekara ta dubu biyu (2000) ba har sai an samu damar zuwa duniyoyi da ke makwabtaka da duniyarmu ta Earth kamar su Mars, da benus da Jupiter da kuma duniyar wata. Sai dai a cewarsa, `”Mene ne burin da muke son cin mawa idan mun ziyarci wadannan duniyoyi? Shin, za mu koma duniyoyin ne mu ci gaba da rayuwa ko kuwa ‘ya’yanmu ne za su mai da rayuwarsu zuwa can?’’Ya ci gaba da cewa “Za a iya tunanin zuwa can domin samo abubuwa masu daraja kamar su zinare, da azurfa da yuraniyon, sai dai kuma zinare da azurfa ana kokarin lalubo su a nan duniyarmu, shi kuwa sinadarin yuraniyon, dauko shi daga wata duniyar zuwa wannan duniyar tamu abu ne mai matukar hadari. Kawai dai abin daza mu so mu dauko shi ne abu mara nauyi,wanda mu a nan muka rasa shi; wannan ba komai ba ne sai Ilimi.’’Edward ya ci gaba da cewa, “Kasancewar Rana daya ce daga cikin Taurari kimanin guda biliyan dari dake cikin rukunin taurarin gungun taurari (Galady) wanda aka baiwa suna “Milky Way,” ba lalle ne a ce duk cikin taurarin nan Tauraruwarmu (Rana) ita kadai ce ke da duniyoyin da ba wanda zai iya rayuwa a cikin su. Haka kuma ba gungun taurarinmu (Galady) ne kadai ba; akwai wani gungun taurari (Galady) dake makwabtaka da mu mai suna “Andromeda Galady),” wanda aka yi hasashen nisansa da gungun taurarinmu ya kai nisan da idan ka tura haske zai yi shekaru miliyan biyu kafin ya isa wajen (2 million light years). Bayan gungun taurarin “Andromeda”, akwai wasu miliyoyi irinsa. Daga can gefe, daura da wannan gungun taurari iya nisan zangon tafiyar haske shekaru miliyan dari, akwai wasu gungun taurari (Galady) guda biyu dasuka yi karo da juna, wanda hakan ya samar da wani kara mai tsanani tare da fitar wani rada (Radar), wanda a cewarsa sai da ya keto har cikin sararin samaniyar duniyarmu.A cikin bincikensa, Edward Teller ya tabbatar da cewa a duniyar Mars akwai wasu launuka masu wulkitawa a duk saddaaka kalli duniyar ta amfani da madubin hangen nesa mai suna “Spectroscope”. Mutum zai ga wasu alamomi da suke nuna alamun wanzuwar wasu hade-haden sinadarai da suke tabbatar da cewa akwai rayuwa a duk inda aka same su, wato sinadaran “Carbon-Hydrogen Bond,” irin sinadaran da ake samu a cikin man fetur. Malaman kimiyyar man fetur kuma sun tabbatar da cewa abin da ke samar da man fetur shi ne rubewar matattun abubuwa kamar su halittun ruwa da sauransu. Don haka, ta yiwu samun wadancan sinadarai a wurin na da nasaba da samun rayuwar halittu a can, sai dai zai yi wahala a samu mutane kamar mu masu rayuwa a can duk da dai muna da burin zuwa can kuma za mu je.

duniya da mars
Dubi bambancin duniyarmu da duniyar Mars

Wani abin kuma shi ne, a kimiyar ilimin sinadarai (Chemistry) mun sani cewa dukkan wani abu mai rayuwa a nan duniyatushensa daya ne, domin muna da tabbacin irin kwayoyin halittar dake jikin mutum; akwai wasu a jikin biri, da kifi, cututtuka masu rai da dai sauransu. Abin tambayar a nan shi ne; shin, idan akwai halittu masu rayuwa a duniyar Mars tun d ga sinadaran da aka gano a can kuma da akwai irinsu a jikin mutum dama sauran halittun dake nan duniya, shin, tsatsonmu daya da su kenan ko kuwa kowa tsatsonsa daban? Ina da tabbacin dai ba mu kadai neke rayuwa ba a cikin sararin wannan duniya. Amma kuma wani abu mai rikitarwa shi ne; a hasashen da aka yi, wannan duniya tamu ta yi shekaru biliyan goma da wanzuwa. Rayuwar mutane kuma a duniyarmu ta wanzu kimanin shekaru rabin miliyan zuwa milkiyan, ai kuwa za a samu masu rai da suka rayu tun farkon duniyoyin nan kafin wanzuwarmu, lalle zan so na ji ina wadanncan mutane dasuka rayu gabaninmu suka tafi?Sai ya ce zuwanmu duniyar wata ne zai ba da damar hango nisan zangon da a nan duniyar ba za mu iya hangowa ba, har daga bisani a tabbatar da cewa duniyar gungun taurari ba ta da iyaka, ko kuma watakila a hango iyakarta da ma wasu biliyoyin irinta. Da akwai wani abu mai launin ja da ya taba bayyana a duniyar Jupiter tun a karnin da ya wuce, wanda zuwa yanzu ba a san ko mene ne ba kuma ana ganin shi kadan-kadan har zuwa yau. Don haka, zuwanmu daya daga cikin duniyoyi masu makwabtaka da mu ne zai sa mu samu ilimin sauran duniyoyin da mana wasu abubuwan.Sai dai a cewarsa, duk wadannan ba su ne manyan muhimman abubuwan ba. A matsayinmu na mutane masu numfashi, babban abin da muka fi so mu sani shi ne amsar tambayar nan da wasunmu suka sha yi: shin, akwai abu mai rai a duniyar wata da sauran duniyoyi? Domin ni ban yarda da fadar mutane cewa halittun da kerayuwa a sauran duniyoyi (Martians) wai kamu daya ba ne, kuma kalarsu koriya ce. Bayan haka kuma za mu so mu ji shin, a cikin Sararin samaniya akwai duniyoyi masu dauke da mutane irinmu? Daga nan sai mu kara bincike akan kara nkanmu. Haka kuma, mu nce muna so kafin karshenkarnin nan mu zagaye duniyoyin Rana (planets), shin, yaushe za mu fara tafiya zuwa sauran taurari? Tauraruwa dai mafi kusanci da Tauraruwarmu rana itace PROdIMA CENTAURI, ba kamar yadda wasu ke cewa “Alpha centauri” ba, kuma nisan dake tsakanin Tauraruwa, rana da “Tauraruwa Prodima,” nisan tafiyar haske ne a shekaru hudu, (4 light years). Ga shi kuma kamar yadda masanin nan Einstein ya fada, babu wani mahaluki da zai iya yin gudu a wani abin hawa dai-dai da saurin haske matukar yana da nauyi, sai dai idan zai zamo ba shi da nauyi ko kadan.To amma duk da haka, ko da za mu iya tafiya dai-dai da gudun haske, tazarar shekaru hudu ba karamar tafiya ba ce, ga shi kuma lalle muna so sai mun je “Prodima Centauri.” Sannan alal misali, idan yanzu na yi amfani da kayayyaki na wannan zamani, na’urar Rocket din da zan iya kerawa zai yi gudu dai-dai daya bisa ashirin na gudu da saurin haske (1/20), kenan idan muka durfafi “Prodima,” ba za mu iya kaiwa gare ta ba sai nan da shekaru tamanin! Wannan lokaci ne mai tsawon gaske.

kumbo columbia
Wannan kumbo kenan a tashar yan sama jannati na Columbia kafin a cillashi zuwa sararin samaniya

Flanetis dake sararin SamaniyaGyara

Duniyar Jupiter

Jupiter wata irin duniya ce mai ban al'ajabi saboda tasha banban da sauran duniyoyi gaba daya.

Yankunan duniya guda bakwaiGyara

Sararin samaniyaGyara

Halittu da shuke-shukeGyara

AnazarciGyara