Tutar Najeriya an kuma tsarata a shekarar 1959 kuma an gabatar da ita a hukumance a ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1960. Tutar na da bamgarori uku wato kore, fari, kore. Korayen guda biyu na nuna arzikin Najeriya yayin da farin na tsakiya ke nuna zaman lafiyar ƙasar.

Tutar Najeriya
national flag (en) Fassara
Bayanai
Farawa 1 Oktoba 1960
Applies to jurisdiction (en) Fassara Najeriya
Nau'in vertical triband (en) Fassara
Aspect ratio (W:H) (en) Fassara 2:1 (en) Fassara
Color (en) Fassara Kore da Fari
Depicts (en) Fassara field (en) Fassara da pale (en) Fassara
Tutar Najeriya

Tsarawa gyara sashe

Michael Taiwo Akinkunmi ne ya tsara tutar Najeria a wata gasa da aka shirya ga masu zane na su tsara tutar da zata zama ta Najeriya a shekarar 1959. A lokacin Akinkunmi nada shekaru 23 kuma yana dalibi. Yana karatu a makarantar Norwich Technical College a London kasar Ingila, sai yaga sanarwa a jarida ta anaso a zana sabuwar tutar Najeriya. Asalin tutar da Akinwumi ya tsara akwai wata alama a tsakiyar ta, bayan masu tantancewa sun duba ne sai suka cire wannan alamar tare da zabarta. Najeriya dai ta samu yancin kanta ne daga kasar Ingila.[1]

Najeriya nada tutoci daban daban na sassan gudanarwar ta. Wasu jahohin na Najeriya nada nasu tutocin.[2]

Mahadin fitar da kala gyara sashe

Yadda za'a hada tutar Najeriya.

Tsarin Kala Kore Fari
RAL
None
9003
Signal white
CMYK 100.0.39.47 0.0.0.0
Hexadecimals #008753 #FFFFFF
Decimals 0,135,83 255,255,255

Wasu tutocin gyara sashe

Tutocin Jahohi gyara sashe

Tutoci na tarihi gyara sashe

Wadannan sune tutocin Najeriya kafin samun yancin kanta.


Sake duba gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. "Archived copy". Archived from the original on 2014-07-14. Retrieved 2014-06-30.CS1 maint: archived copy as title (link)
  2. Nigeria: One Nation, Many Flags