Tambarin Najeriya ko Kan Sarki wata alama ce gwamnatin Najeriya take amfani da ita a hukimance a matsayin hatin kasa. Tambarin na dauke da hotuna kamar haka; Akwai Mikiya daga sama, tana nuni da karfin Najeriya, sai fararen dokuna biyu a gefe da gefe, suna nuna martabar Najeriya, akwai kuma zane biyu daya daga hagu dayan daga dama sun hade a waje guda, suna nuna kogunan Neja da na Benue da mahadar su a Lokoja. Wannan bakin da zane yabi ta kansa kuma yana nuna albarkatun kasar da Najeriya ke dashi ne. Koriyar ciyawa ta kasa kuma na nuna arzikin Najeria.[1]

Tambarin Najeriya
national coat of arms (en) Fassara
Bayanai
Farawa 20 Mayu 1960
Applies to jurisdiction (en) Fassara Najeriya
Depicts (en) Fassara Costus spectabilis (en) Fassara, doki, Nijar, Benue da eagle (en) Fassara
Tambarin Najeriya

Jar fulawa ta ciki na nuna fulawar Najeriya Costus spectabilis, anzabi wannan fulawar ne saboda ana samun ta a ko'ina a sassan Najeriya.

Alamomim gwamnati gyara sashe

Alamomin Jahohi gyara sashe

Wasu jahohin nada nasu tambarin.

Alamomi na tarihi gyara sashe

Wasu tambari wadanda akayi amfani dasu a baya.

Sake duba gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. "National Symbols - Emblem". Nigeria's 50th Independence: Celebrating Greatness. Archived from the original on May 6, 2011. Retrieved May 21, 2012.