Burkina Fasoƙasa ce dake yankin yammacin Afirka. A da chan ana kiranta da suna "Upper Volta", ƙasar Faransa suka yi mulkin mallaka a ƙasar Burkina Faso. Kuma ƙasar ta samu 'yanci kanta a shekara ta Alif 1960. Birnin Ouagadougou ne babban birnin ƙasar. A ƙidaya da akayi a shekara ta 2005 ya nuna cewa ƙasar Burkina faso na da kimanin mutane 13,228,000 suke zaune a ƙasar. Kasar Burkina faso ta haɗa boda da ƙasar Mali daga arewa maso yamma, kasar Nijar daga arewa maso gabas, ƙasar Benin tafarkin kudu maso gabacin kasar, sai kuma Ƙasar Togo da Ghana daga kudancin kasar, akwai kuma ƙasar côte ƊIvoire wanda ke yankin kudancin kasar. Ana kiran mutane 'yan asalin kasar Burkina faso da suna "Burkinabé" (furuci burr-KEE-na-bey).
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
.
Kasar burkina fasoIbrahim Traoré shugaban kasar ta Burkina Faso
Wasu mayakan Burkina Faso a karnin bayaAvenue Burkina faso
Tarihi ya nuna cewa ada can, a tsakanin ƙarni na Goma sha biyar zuwa ƙarni na sha-shida al'umma daga mutanen da ake kira Dogon sun zauna a yankin arewacin da arewa-maso-yammacin Burkina faso. A cikin nasara sai Faransa ta karbi mulkin mallaka daga hannun masu mulkin Burkina faso. Bayan Yakin duniya II (na biyu), ƙasar ta yi kira bisa kogin volta. A shekara ta 1960, bisa kogin volta ta yantacciyar daga Faransa. A shekara ta 1984, an canza sunan ƙasar zuwa Burkina faso.