Jihar Kano jiha ce dake a ƙasar Najeriya. Tana da yawan fili kimanin kilomita murabba’i 20,131 da yawan jama’a milyan sha ɗaya da dubu hamsin da takwas da dari uku (jimillar shekara 2011). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Kano. Abdullahi Umar Ganduje shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Nasiru Gawuna. Dattijan jihar sune; Aminu Kano, Maitama Sule, Sani Abacha, Murtala Mohammed, Sanusi Lamido Sanusi, Ibrahim Shekarau, Isyaka Rabi'u, Aliko Dangote, Rabiu Musa Kwankwaso, Barau I Jibrin da Kabiru Ibrahim Gaya.

Fadar sarkin kano
Jihar Kano
Sunan barkwancin jiha: Cibiyar kasuwanci
Wuri
Location of Kano State in Nigeria
Ƙidaya
Harshe Hausa, Fulani, Kanuri
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje (APC)
An ƙirkiro ta 1967
Baban birnin jiha Kano
Iyaka 20,131km²
Mutane
1991 (ƙidayar yawan jama'a)
2011 (jimilla)

5,632,040

11,058,300
ISO 3166-2 NG-KN

Jihar Kano tana da iyaka da misalin jihhohi huɗu, su ne: Kaduna, Katsina, Jigawa kuma da Bauchi.Jahar kano ina mata kirari da kano koda me kazo an fika.Muhammadu Sanusi II shine sarkin kano

Kano ita ce tsakiyar bankin musulunci a Najeriya.[1]

Kananan hukumomiGyara

Kano tanada kananan hukumomi guda 44 sune :

 
Taswirar Jihar kano, tana nuna dukkan kananan hukumomin kano guda Arba'in da hudu
File:Kano , Kano State , Nigeria.jpg
Taswirar Jihar Kano, gani daga sararin samaniya


Jihohin Najeriya
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa

Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara

  1. [1]