Mali
Mali da Turanci (Mali) da Faransanci (meli) ƙasa ce da ke a yammacin Afrika. Mali tana cikin manyan ƙasashen Afrika guda 8, ta na da faɗin ƙasa kimanin murabba'i 1,240,000,Km (480,000 sq, mi), kuma tana da yawan jama`a kimanin miliyan 19.1.[1] Bincike ya nuna cewa 67% na mutanen ƙasar shekarunsu bai wuce ashirin da biyar (25) ba, bisa ƙidayar da aka yi a shekarar 2017.[2] Bamako shi ne baban birnin ƙasar Mali.
Mali | |||||
---|---|---|---|---|---|
|
|||||
| |||||
| |||||
Take | Pour l'Afrique et pour toi (en) | ||||
| |||||
| |||||
Kirari |
«One people, one goal, one faith» «Един народ, една цел, една вяра» «Ein Volk, ein Ziel, ein Glaube» «ߡߌ߬ߙߌ߲߬ߘߌ߬ ߞߋߟߋ߲߫ ߸ ߟߊ߬ߢߌߣߌ߲߫ ߞߋߟߋ߲߫ ߸ ߘߍ߲߬ߞߣߍ߬ߦߊ߬ ߞߋߟߋ߲߫» «شعب واحد، هدف واحد، إيمان واحد» «Un pueblo, una meta, una fe» «En narod, en cilj, ena vera» «Mɔgɔ kelen, laɲini kelen, dannaya kelen» «Un peuple, un but, une foi» «Un bobl, un nod, un ffydd» | ||||
Suna saboda | Daular Mali | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Babban birni | Bamako | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 20,250,833 (2020) | ||||
• Yawan mutane | 16.33 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati |
Harshen Bambara Harshen Bobo Sarkanci Dogon harsuna Fillanci Hassaniya Larabci Harshen Kassonke Yaren Maninka Yaren Minyanka Senufo (en) Harsunan Songhay Harshen Soninke Tamacheq Tuareg | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | Afirka ta Yamma | ||||
Yawan fili | 1,240,192 km² | ||||
Wuri mafi tsayi | Mount Hombori (en) (1,153 m) | ||||
Wuri mafi ƙasa | Kogin Senegal (23 m) | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Mali Federation (en) , French Sudan (en) da French West Africa (en) | ||||
Ƙirƙira | 22 Satumba 1960 | ||||
Ranakun huta | |||||
Tsarin Siyasa | |||||
Gangar majalisa | National Assembly (en) | ||||
• Shugaban kasar mali | Assimi Goita (24 Mayu 2021) | ||||
• Prime Minister of Mali (en) | Choguel Kokalla Maïga (en) (6 ga Yuni, 2021) | ||||
Ikonomi | |||||
Nominal GDP (en) | 19,309,463,506 $ (2021) | ||||
Kuɗi | CFA franc Yammacin Afirka | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Suna ta yanar gizo | .ml (mul) | ||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | +223 | ||||
Lambar taimakon gaggawa | *#06#, 15 (en) , 17 (en) da 18 (en) | ||||
Lambar ƙasa | ML | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | primature.gov.ml |
Tarihi
gyara sasheWaɗannan ƙabilu Soninke da Mandinka ko (Mandingo da Malinke) sun ɓalle daga ƙasar Kongo a shekarar 1230, daga nan sarkin madingo Sundiata Keita sai ya yi ƙungiya ta waɗannan ƙabilu guda uku a gefan tafkin chadi, sannan masarautar Mali aka ƙirƙirota a wannan lokacin tafi masarautar Ghana. Mansa Musa yana da baban magame a ƙasa bayan sarki Sundiata Keita shi ne ɗan afirka na farko da ya je aikin Hajji da ƙafa a shekar (1324) ta hanyar misra, a wannan shekarar kuma aka zamar da Tomboucou kasuwar sayar da zinari da koyar da Addinin Musulunci. A ƙarshen karni na 14, Abizinawa suka zo daga kudancin hamada suka mamaye wannan birni a shekarar 1500, sai suka tsawaita ikonsu zuwa sama da tafkin issa.
A ranar 22 ga watan satumban, shekarar 1960, sai Jamhuriyar Sudan da Senegal suka samu 'yancin kai daga Faransa, suka haɗe tare suka zama tarayyar Mali bayan watanni sai Senegal ta ɓalle daga Jamhuriyar sudan. daga nan sai aka samata sunan Jamhuriyar Sudan. A shekarar (1991), aka yi gwamnati ta wucin-gadi daga nan aka kawo ƙarshen hukunci mai tsanani, kuma a shekarar 1992, aka yi zaɓe na farko a sabuwar dimokwaraɗiyya, shugaba Alfa Umar Kunare ya lashe zaɓen a shekarar 1997, sai aka sake zaɓensa a Karo na biyu kuma a shekara ta 2002 aka yi wani zaben, sai Ahamadu Tumane Ture ya lashe zaɓen har ila yau.[1]
Hotuna
gyara sashe
-
Begnimatou, Mali
-
Tutar kasar
-
Coat of Arms
-
Wani ɗan talla a Kasar Mali.
-
Tsohon Masallaci a Ƙasar Mali.
-
Ginin ƙauye a Mali.
-
Wani mutum ɗan ƙasar Mali.
-
Mawaƙan gargajiya a ƙasar Mali.
-
Mawaƙa a Ƙasar Mali.
Manazarta
gyara sashe
Ƙasashen Afirka |
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe |