Kasar Misra, ko Masar tana kudu maso gabashin Afrika, kuma tana kudu maso yammacin Asiya [1] ɗaya daga cikin muhimman siffofin da take taƙama da su shi ne na kasancewa ta a kan mararraba ta kusa da nahiyar Turai. Sannan kuma tana matsayin ƙasar da ta kasance mashiga tsakanin Afirka da nahiyar Asiya. Har ila yau kuma, ita ce kuma ta haɗa hanyar safara ta cikin ruwa, tsakanin tekun Mediterrenean da tekun Indiya ta hanyar Bahar Maliya.

Misra
جُمهورِيّةُ مِصرَ العَرَبيّةِ (ar)
Flag of Egypt (en) Coat of arms of Egypt (en)
Flag of Egypt (en) Fassara Coat of arms of Egypt (en) Fassara

Take Bilady, Bilady, Bilady (en) Fassara

Suna saboda Ptah (en) Fassara da Mizraim (en) Fassara
Wuri
Map
 27°N 29°E / 27°N 29°E / 27; 29

Babban birni Kairo
Yawan mutane
Faɗi 94,798,827 (2017)
• Yawan mutane 93.82 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Larabci
Labarin ƙasa
Bangare na Arewacin Afirka, Gabas ta tsakiya da Yammacin Asiya
Yawan fili 1,010,407.87 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Bahar Rum da Nil
Wuri mafi tsayi Mount Catherine (en) Fassara (2,629 m)
Wuri mafi ƙasa Qattara Depression (en) Fassara (−133 m)
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Kingdom of Egypt (en) Fassara da All-Palestine Government (en) Fassara
Ƙirƙira 28 ga Faburairu, 1922Kingdom of Egypt (en) Fassara
Tsarin Siyasa
Tsarin gwamnati jamhuriya
Gangar majalisa Parliament of Egypt (en) Fassara
• Shugaban kasar Egypt Abdul Fatah el-Sisi (8 ga Yuni, 2014)
• Prime Minister of Egypt (en) Fassara Mostafa Madbouly (en) Fassara (14 ga Yuni, 2018)
Ikonomi
Nominal GDP (en) Fassara 424,671,765,456 $ (2021)
Kuɗi Fam na Masar
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
UTC+02:00 (en) Fassara
UTC+03:00 (en) Fassara
Suna ta yanar gizo .eg (en) Fassara da .مصر (en) Fassara
Tsarin lamba ta kiran tarho +20
Lambar taimakon gaggawa 122 (en) Fassara, 123 (en) Fassara da 180 (en) Fassara
Lambar ƙasa EG
Wasu abun

Yanar gizo egypt.travel
Tuta Misra
Taswirar Misra
Kasar masar
wani gini amisira
masar

Dalar Giza da ke birnin Al-ƙahirar Kasar. Misra ko ƙasar Masar dai ta kasance ƙasa mafi yawan al'umma a cikin dukkanin ƙasashen Larabawa, kuma babban birninta wato birnin Al'ƙahira shi ne birni mafi girma a nahiyar Afirka tun ƙarnoni da dama da suka gabata. Sannan kuma har ila yau, ga ta a ƙarshen kogin nilu, wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. Saboda haka, idan aka yi la'akari da waɗannan dalilai na tarihi, to za a iya fahimtar dalilin da ya sa matsayin ƙasar Misra yake da ƴar rikitarwa.

Su ma kansu Misirawan a tsakanin su, sukan kasance cikin ruɗani a game da batun nahiyar da ya kamata su yi tutiya da ita a matsayin nahiyarsu. Ga su dai a cikin kwazazzabon nilu, da mediterenean, da Sahara, har ila yau kuma ga su cikin duniyar Musulmai, dukkan waɗannan siffofi, siffofi ne da kuma ba kasafai ya kamata a ce wata ƙasa guda ɗaya ta haɗa su ba. To, sai dai duk da haka za a iya cewa, mafi yawan faɗin ƙasar yana ɓangaren nahiyar Afirka ne. To, amma fa duk da haka ana kallon garuruwan da suke lardin Sinai na ƙasar Misiran a matsayin ɓangaren nahiyar Asiya, kasancewar su, suna yankin gabashin ƙasar ne.

Kogin Nilu wanda shi ne kogi mafi girma a duniya. A zamanin da can, dangantakar Misra da ƙasashen da ke Afirka na da matukar ƙarfi. To amma tun lokacin da Siriyawa da ke ƙarƙashin daular Rumawa suka mamaye Misira, a ƙarni na bakwai kafin zuwan Annabi Isa Alaihissalam, sai Misira ta fuskanta zuwa ga Yankin Gabas ta Tsakiya, ta fuskar harkokin al'adunta, da na addininta da na siyasarta da kuma na tattalin arzikinta. Kuma mafiya yawan Misirawa suna danganta kansu ne da Larabawa kuma ƴan Yankin Gabas ta Tsakiya. Har ila yau, kuma wasu da yawa daga cikinsu, kusan ace waɗanda suke su ne 'yan asalin ƙasar ta Misira, waɗanda kuma aka fi sani da Nubiyawa, suna danganta kansu ne da Afirka. Hasali ma suna iƙirarin su jinin Afirka ne.

masar

Babu shakka dai idan aka bi salsala ta tarihi, shekaru kimanin 200 da suka gabata, Misra tana da alaƙa mai ƙarfi da ƙasashe irin su Sudan da Habasha da Libya da ma wasu ƙasashe da dama na nahiyar ta Afirka. Kuma ba tare da wani kokwanto ba, Misra za ta cigaba da cin tudu biyu, a matsayinta na ruwa-biyu, wato ga ta dai 'yar Afirka, kuma 'yar yankin Gabas ta Tsakiya, yana daga cikin tarihin Misira kasancewarta

Abdel Fattah El-Sisi shugaban kasar na yanzu

gari na farko a tarihi da sheɗan da kansa ya bayyana ga azzalumin sarki Fir' auna a lokacin da Fir'auna ya ce shi Ubangiji ne.

Tarihi Gyara

Kasar na da matukar tarihin gaske a yankin Afirka da duniya gabaki daya

Al'adu Gyara

Abinci Gyara

Tufafi Gyara

Yarika Gyara

Mulki Gyara

 
Gwamnatocin Masar
 
Tarukan gwamnati a Masar


 
Tarurrukan gwamnati a Masar

Kasan misra tana da karfin mulki.

Sufuri Gyara

 
Gadar sama a birnin Cairo

Arziki Gyara

Noma Gyara

Kasar Misra na da dabino da furanni daban-daban.

Kiwon lafiya Gyara

Akwai asibitoci da'ake kula da marasa lafiya

Wasanni Gyara

Addini Gyara

Musulunci Gyara

Kiristanci Gyara

Tsaro Gyara

Manazarta Gyara


Ƙasashen Afirka
Afirka ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Moris | Muritaniya | Misra | Morocco | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe