Gombe (jiha)
Gombe jiha ce dake Arewa maso Gabashin Najeriya. Tayi iyaka daga Arewa da Arewa maso gabas da jihohin Borno da Yobe, daga Kudu kuwa da Jihar Taraba, daga Kudu maso yamma kuwa da Jihar Adamawa sannan daga Yamma da Jihar Bauchi. Ta samo asalin sunanta daga babban birninta kuma yanki mafi girma a jihar wato Babban Birnin Gombe - kuma an ƙirƙireta ne daga sashin Jihar Bauchi a ranar 1 ga watan Oktoban shekara ta alif ɗari tara da cassain da shida 1996. Jihar na daga cikin jihohin da ke ɗauke da ƙabilu iri-iri a Najeriya. Acikin jihohi 36 da Abuja na Najeriya, Jihar Gombe itace Jiha ta 21 a girma, kuma ta 32 a yawan jama'a, da mutane aƙalla miliyan 3.25 dangane da ƙiyasin shekarar 2016.[1]
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
|
|||||
![]() | |||||
| |||||
Suna saboda | Gombe | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Gombe | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 3,256,962 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 173.54 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 18,768 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Jihar Bauchi | ||||
Ƙirƙira | 1 Oktoba 1996 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa |
executive council of Gombe State (en) ![]() | ||||
Gangar majalisa |
Gombe State House of Assembly (en) ![]() | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-GO | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | nigeria.gov.ng… |


Ta fuskar yanayin ƙasa, Jihar tana da ƙasa nau'in Tropical West Sudanian Savanna. Muhimman wurare a jihar sun haɗa Kogin Gongola, wanda ke kwarara ta arewaci da Gabashin Gombe zuwa cikin tafkin Dadin Kowa Dam zuwa gaɓar Tsaunukan Muri da ke can yankin kudancin jihar. Daga cikin dabbobi asali na jihar akwai nau'in macizai irin su: carpet viper, puff adder, da kuma Egyptian cobra da kuma dabbobi irin su dorinar ruwa, Senegal parrot, da kuma grey-headed kingfisher.
Jihar Gombe na ɗauke da ƙabilu da dama, yayinda Ƙabilar Fulani suka mamaye yankin arewaci da tsakiyar jihar tare da Bolewa, Kanuri, da kuma Hausawa. A yayin ƙabilu irin su Cham, Dadiya, Jaranci da Kamo, Pero, Tangale, Tera, da kuma mutanen Waja da suka mamaye yankunan gabashi da kudancin jihar.
Kafin zuwan Turawa, yankin Jihar Gombe ta yau tana ɗauke da ƙasashe da dama masu zaman kansu, har zuwa farkon karni na 1800, lokacin da Fulani suka ƙwace yankuna da dama na yankin kuma suka haɗeta a matsayin Masarautar Gombe a ƙarƙashin Daular Sokoto. A cikin karni na 1900, Turawan mulkin mallaka sun mamaye masarautar da yankunan gefen ta kuma sun haɗeta acikin Yankin Mulkin Mallaka na Arewacin Najeriya, inda daga baya ta zamo Colonial Nigeria, kafin daga bisani ta samu 'yanci a1960 kuma ta zamo ƙasa Najeriya. Bayan samun 'yancin kai kuwa, Jihar Gombe ta yau ta faɗa ƙarƙashin Arewacin Najeriya har zuwa 1967 lokacin da aka raba yankin kuma jihar ta faɗa ƙarƙashin Jihar Arewa ta Gabas. Bayan an raba Jihar Arewa maso Gabas, an ƙirƙiri Jihar Bauchi a shekarar 1976 tare da Sauran jihohi guda goma. Shekaru ashirin bayan haka (1996) an cire wasu gungun ƙananan hukumomi daga yammacin Jihar Bauchi don samar da Jihar Gombe.
Dangane da fannin tattalin arziƙi, Jihar Gombe ta dogara ne akan noma da kiwo, da man fetur, inda ake shuka gero, masara, gyaɗa, dawa da tumatir tare da kiwon dabbobi kamarsu raƙumma, shanu, akuyoyi da kuma tumaki. Sauran muhimman masana'antu sun haɗa da hidindimu na zamani da ake gudanarwa musamman a birnin Gombe. Jihar Gombe itace jiha ta huɗu a jerin ƙarancin Cigaban al'ummaa.
Tana da yawan fili kimanin kilomita murabba’i 18,768 da yawan jama’a miliyan biyu da dubu uku da hamsin da uku (ƙidayar yawan jama'a shekara ta 2006). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Gombe. Muhammadx Inuwa Yahaya shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Dr Manasa Daniel Jatau. Dattijan jihar su ne: Sarakunan gargajiya, Malaman addini da kuma jigogin siyasa.[2]
Bayani Gyara
Jihar na da faɗin fili na kimanin 20,265 km2 da kuma mutane kimanin mutum 2,365,000 a shekara ta 2006. An ƙirkire ta ne a cikin watan Oktoban 1996, daga yankin tsohuwar Jihar Bauchi a lokacin mulkin Shugaba Sani Abacha. Jihar na nan a yankin ƙasar Najeriya mai nau'in tsirrai irin na Guinea savannah da Sudan savannah. Akwai tuddai masu ɗan bisa, duwatsun ƙasa da kuma duwatsu na daga witar volcano a yankunan tsaunukan garin. Zaman jihar a yankin savanna na arewa maso gabashin Najeriya yasa jihar ta haɗa iyaka da jihohi kaman Borno, Yobe, Taraba, Adamawa da Bauchi.
Jihar Gombe ta na yanayi guda biyu: yanayin rani (daga watan Nuwamba zuwa March) da kuma damuna (daga watan Aprelu zuwa Oktoba) tare da matsakaicin ruwam sama na kimanin 850mm.
Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa ke javorancin jihar tare da taimakon muƙarrabai 24 daga majalisar dokoki na jihar. Jihar Gombe na da ƙananan hukumomi 11 da kuma masarautu na gargajiya guda 14. Tana da sanatoci guda 3 da kuma 'yan Mjalisar Tarayyar Najeriya guda shida.
Ƙananan Hukumomi Gyara
Jihar Gombe nada Kananan hukumomi guda goma sha ɗaya (11). Sune kamar haka:
Karamar Hukuma | Fadin kasa (km2) | Adadin 2006 Mutane |
Cibiyar Karamar Hukuma | Lambar aika sako |
---|---|---|---|---|
Akko | 2,627 | 337,853 | Kumo | 771 |
Balanga | 1,626 | 212,549 | Tallase | 761 |
Billiri | 737 | 202,144 | Billiri | 771 |
Dukku | 3,815 | 207,190 | Dukku | 760 |
Funakaye | 1,415 | 236,087 | Bajoga | 762 |
Gombe | 52 | 268,000 | Gombe (city) | 760 |
Kaltungo | 881 | 149,805 | Kaltungo | 770 |
Kwami | 1,787 | 195,298 | Mallam Sidi | 760 |
Nafada | 1,586 | 138,185 | Nafada | 762 |
Shongom | 922 | 151,520 | Boh | 770 |
Yamaltu/Deba | 1,981 | 255,248 | Deba Habe | 761 |
Al'umma Gyara
Jihar Gombe na ɗauke da al'ummomi iri-iri, yayinda Fulani suka mamaye mafiya yawancin yankin arewacin jihar. Fulani sun mamaye Kusan ƙananan hukumomi guda 6 na Jihar Gombe. Waɗannan ƙananan hukumomi sun haɗa da Dukku, Kwami, Funakaye, Nafada, Akko, kuma ƙaramar hukumar Gombe. Bayan Fulani akwai kuma Tangale, da ke rayuwa a yankin Billiri da Kaltungo. Sauran ƙabilu sun haɗa da the Hausawa Tula, Tera (Yamaltu-Deba), Waja, Bolewa, da kuma Kanuri.
Harsuna Gyara
An zayyano harsunan Jihar Gombe dangane da ƙananan hukumominsu a teburi da ke ƙasa:
LGA | Area (km2) | Census 2006 population |
Administrative capital | Postal code |
---|---|---|---|---|
Akko | 2,627 | 337,853 | Kumo | 771 |
Balanga | 1,626 | 212,549 | Tallase | 761 |
Billiri | 737 | 202,144 | Billiri | 771 |
Dukku | 3,815 | 207,190 | Dukku | 760 |
Funakaye | 1,415 | 236,087 | Bajoga | 762 |
Gombe | 52 | 268,000 | Gombe (city) | 760 |
Kaltungo | 881 | 149,805 | Kaltungo | 770 |
Kwami | 1,787 | 195,298 | Mallam Sidi | 760 |
Nafada | 1,586 | 138,185 | Nafada | 762 |
Shongom | 922 | 151,520 | Boh | 770 |
Yamaltu/Deba | 1,981 | 255,248 | Deba | 761 |
Ilimi Gyara
Jami'o'i a jihar Gombe Gyara
Manyan jami'oi na Jihar Gombe sun haɗa da:
- Federal University Kashere[3]
- Gombe State University[4]
- Federal College of Education (Technical), Gombe[5]
- Federal College of Horticultural Technology, Dadin Kowa[6]
- Federal Polytechnic, Kaltungo
- College of Education, Billiri[7]
- Gombe State College of Legal Studies, Nafada[8]
- Gombe State Polytechnic, Bajoga[9]
- Gombe State University of science and Technology, Kumo[10]
Makarantun Sakandare[11] Gyara
- Matrix International Academy
- Gombe High School
- Pen Resource Academy
- Demonstration Secondary School
- Government Day Science Secondary School
- Ilimi International School
- Gombe international School
- JIBIWIS Arawa Secondary School
- All-saint Secondary School
- Darul Arqam Academy
- Government Day Hassan Central
- Yahya Ahmad Model School
- Government Senior Secondary School Herwagana, Gombe
- Government Senior Secondary School Gandu
Kiwon Lafiya Gyara
Jihar Gombe nada cibiyoyin kiwon lafiya masu yawa, dukkanin su i sun samu ne ta karkashin gudanarwa sashi guda uku, gwamnatin jiha, Gwamnatin tarayya da kuma cibiyoyi mallakin dai-daikun mutane. Wadannan cibiyoyi sun hada da :
Cibiyoyi Karkashin Gwanatin Tarayya Gyara
- Federal Teaching Hospital Gombe (FTHG)[12]
Cibiyoyi Karkashin Gwamnatin Jiha Gyara
- Billiri General Hospital
- Gombe State Specialist Hospital[13]
- Arawa Primary Healthcare
- Gabukka Primary Healthcare[14]
- Doma Primary Healthcare[15]
- Pantami Primary Healthcare[16]
- Zainab Bulkachuwa Women and Children Hospital[17]
- Town Maternity (Gidan Magani)
Cibiyoyin da ba na Gwamnati ba Gyara
- Miyetti Hospital
- Musaba Hospital
- Sabana Hospita
- AHAJAS Memorial Hospital
Cibiyoyin Magun-guna Gyara
- Kumbi chemist
- Sauki phamarcy
- A.A. Aliyu Mega Store
- Jam Bandu Pharmacy
Ma'adanai Gyara
Jihar Gombe na daya daga cikin jahohi masu tarin albarkatun kasa a Nigeria wanda ke samar da kayan tasarrufi da ma'aikatu ke amfani dashi, yan kasuwa ke kasuwance su, wasun kuma ake amfani dasu a matsayin abinci, wadannan ma'adanai sun hada da :
Ma'adanai da Ake Hakowa[18] Gyara
- Laka
- Dayen Mai[19]
Ma'adanai da Ke Tsira Gyara
Gwamnoni Gyara
A ƙasa an jero sunayen gwamnoni da jagorori na Jihar Gombe.
Name | Take | Lokacin hawa mulki | Lokacin sauka daga mulki | Jam'iyya |
---|---|---|---|---|
Group Captain Joseph Orji | Administrator | 7 Oct 1996 | Aug 1998 | Military |
Abubakar Habu Hashidu | Governor | 29 May 1999 | 29 May 2003 | APP |
Mohammed Danjuma Goje | Governor | 29 May 2003 | May 2011 | PDP |
Ibrahim Hassan Dankwambo | Governor | May 2011 | 29 May 2019 | PDP |
Muhammad Inuwa Yahaya | Governor | May 2019 | Incumbent | APC |
Sanannun Mutane Gyara
- Amina Mohammed, UN deputy secretary[22] Sheikh Adamu Muhammad Nafada teacher, preacher
- Sheikh Dahiru Bauchi, teacher, preacher[23]
- Sheikh Kabir Muhammad Haruna Gombe, preacher[24]
- Isa Ali Pantami, malami Kuma tsohon ministan sadarwa [25]
- Danladi Mohammed, Dan siyasa.
- Joshua M. Lidani, Dan siyasa
- Eli Jidere Bala, engineer
- Usman Bayero Nafada, politician[26]
- Samkon Gado, Nigerian-American otolaryngologist and American football player
- Zainab Adamu Bulkachuwa, jurist
- Jaaruma, entrepreneur
- Aliyu Modibbo Umar, politician[27]
- Mohammed Danjuma Goje, politician
- Helon Habila, novelist
- Dahiru Mohammed, Politician
- Abubakar Buba Atare, Emir of Tula Chiefdom
- Buba Yero, sarkin farko na Gombe
- Abubakar Shehu-Abubakar, sarki na goma shadaya a gombe
- Musa Dankyau, Professor of Family Medicine [28][1]
- Abdullahi Mahdi Educationalist
- Aliyu Usman El-nafati Professor of Gynecology
- Isah Usman Taliyawa[29]
- Sheikh Kabiru Gombe[30]
Wuraren ziyara a Gombe[31] Gyara
Wuraren buɗe idana a jihar sun haɗa da:[32]
- Shahararren Bima Hill
- Tula Plateau
- Bulok Warm Spring
- Kalam Hill
- Cham Valley
- Tsaffi burbushin Binga
- Maƙabartar Major Mash
- Maƙabartar LT Phillips
- Bace Hills
- Kanawa Forest
Manazarta Gyara
- ↑ https://www.britannica.com/place/Gombe-Nigeria
- ↑ https://www.britannica.com/place/Gombe-Nigeria
- ↑ "Official List of Courses Offered in Federal University, Kashere (FUK) - Myschool". myschool.ng (in Turanci). Archived from the original on 2021-10-27. Retrieved 2021-10-14.
- ↑ "Official List of Courses Offered in Gombe State university (GOMSU) - Myschool". myschool.ng (in Turanci). Archived from the original on 2021-10-27. Retrieved 2021-10-14.
- ↑ https://leadership.ng/federal-govt-commissions-road-project-in-fcet-gombe/
- ↑ "Federal College of Horticulture, Dadinkowa – Horticulture" (in Turanci). Archived from the original on 2022-01-26. Retrieved 2022-03-29.
- ↑ "College of Education Billiri". www.billiricoe.edu.ng. Archived from the original on 2021-07-26. Retrieved 2022-03-29.
- ↑ https://leadership.ng/periscoping-inuwas-2023-budget-of-further-consolidation-in-gombe/
- ↑ https://infoguidenigeria.com/gombe-state-polytechnic-post-utme-form/
- ↑ https://www.thisdaylive.com/index.php/2022/12/04/muhammad-barde-ill-leverage-courage-integrity-and-technology-to-change-gombes-story/
- ↑ https://dailytrust.com/after-gombe-model-schools-upgrade-parents-now-scramble-to-enrol-wards/
- ↑ https://independent.ng/gombe-federal-teaching-hospital-receives-medical-equipment-from-mtn-foundation/
- ↑ https://leadership.ng/gombe-specialist-hospital-accredited-for-postgraduate-training-on-obstetrics-gynecology-others/
- ↑ https://wikkitimes.com/investigation-genotype-scam-how-health-workers-in-gombe-issue-fake-genotype-certificates-for-a-token/
- ↑ https://www.afro.who.int/countries/nigeria/news/bringing-primary-health-services-closer-underserved-people-gombe-state
- ↑ https://von.gov.ng/gohealth-gombe-enrols-40000-vulnerable-people/
- ↑ https://soamaps.com/country/NG/160321/zainab-bulkachuwa-women-and-children-hospital
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/regional/nnorth-east/255262-gombe-start-preliminary-exploration-mineral-resources.html
- ↑ https://punchng.com/on-recent-oil-discovery-in-the-north/
- ↑ https://www.environewsnigeria.com/dry-season-farming-maize-farmers-record-bumper-harvest-in-gombe/
- ↑ https://punchng.com/gombe-moves-to-sustain-cotton-production/
- ↑ "Nigeria's Amina Mohammed reappointed UN Deputy Secretary-General" (in Turanci). 2022-01-11. Archived from the original on 2022-02-11. Retrieved 2022-02-11.
- ↑ Agencies (2020-02-16). "Governor Buhari congratulates Sheikh Bauchi over doctorate degree". TODAY (in Turanci). Archived from the original on 2022-02-11. Retrieved 2022-02-11.
- ↑ https://hausa.leadership.ng/sheikh-dahiru-bauchi-ya-halarci-waazin-da-kungiyar-izala-ta-gudanar-a-bauchi/
- ↑ https://www.thisdaylive.com/index.php/2022/12/09/skills-rather-than-just-degrees/
- ↑ https://www.blueprint.ng/fidelis-makka-usman-bayero-nafada-where-are-they-now/
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/511435-interview-how-abuja-a-virgin-land-became-nigerias-best-planned-city-ex-minister-modibbo.html
- ↑ "| DokiLink".
- ↑ https://hausa.legit.ng/1337945-allah-ya-yiwa-babban-sakataren-izalah-malam-mukhari-ibrahim-rasuwa.html
- ↑ https://hausa.legit.ng/1433841-sheikh-kabiru-gombe-ya-yafewa-muaz-magaji-sun-gana-ido-da-ido.html
- ↑ "Gombe State: The History, Ethnic Groups and Tourist Attractions – Global Tourism Academy" (in Turanci). Archived from the original on 2022-04-29. Retrieved 2022-04-06.
- ↑ https://ogavenue.com.ng. "Fields in Gombe | Gombe | Venues in Nigeria". ogaVenue.com (in Turanci). Archived from the original on 2022-10-16. Retrieved 2022-09-06.
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |