Muhammadu Buhari

Shugaban Kasar Najeriya

Muhammadu Buhari (An haife shi a ranar 17 ga watan Disamban shekara ta 1942), Ya kuma kasance tsohon soja ne mai ritaya, kuma dan siyasa ne. Ya zama zaɓaɓɓen shugaban kasar Nijeriya ne a zaben shekarar 2015 a Karon farko,inda ya kada tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Muhammadu Buhari ya sake samun nasarar zama shugaban kasar Najeriya a Karo na biyu a shekarar 2019 yayin da yakada Dan takarar Jam'iyar hamayya watau Alhaji Atiku Abubakar. Muhammad Buhari yayi shugaban PTF watau (Asusu na Musamman don Tattara Kudin Man Fetur Wanda aka fi sani da (Petroleum Special Trust Fund (PTF) wanda tsohon Shugaban mulkin soja wato Sani Abacha ya bashi matsayin, kuma yayi Ministan man-fetur a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha.[1][2][3]

Simpleicons Interface user-outline.svg Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari.jpg
15. shugaban ƙasar Najeriya

29 Mayu 2015 -
Goodluck Jonathan
7. shugaban ƙasar Najeriya

31 Disamba 1983 - 27 ga Augusta, 1985
Shehu Shagari - Ibrahim Babangida
Gwamnan Jihar Borno

ga Yuli, 1975 - ga Maris, 1976
Musa Usman (en) Fassara - Mustapha Amin (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Daura, 17 Disamba 1942 (78 shekaru)
ƙasa Najeriya
ƙungiyar ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta United States Army War College (en) Fassara
Jami'ar Tsaron Nijeriya
military education and training (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a soja da ɗan siyasa
Kyaututtuka
Aikin soja
Fannin soja Nigerian Army (en) Fassara
Digiri Manjo Janar
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress
Congress for Progressive Change (en) Fassara
thisisbuhari.com
Hoton Shugaba Buhari a shekara ta 2015.

Farkon rayuwaGyara

 
Muhammadu buhari

An haife Muhammad Buhari a ranar 17 ga watan Disamba 1942 a garin Daura da ke cikin jihar Katsina, a arewacin tarayyar Nigeria. Sunan mahaifanshi Harɗo Adamu da Hajiya Zulaihatu Musa, an haifeshi ne a Daura.[4] Mahaifinshi shine shugababn ƙauyen Dumurkol, ya haifa yara ashirin da mata daban-daban, Muhammadu Buhari shine yaranshi na ƙarshe a gurin Hajiya Zulaihatu Harɗo, wacce ita kuma cikakkiyar bahaushiya ce ƴar ƙabilar Haɓe na hausawa. Kuma shine yaro na ƙarshe a gun babanshi, wato Auta. Babanshi da kakanshi cikakkun fulani ne.[4]  Muhammadu Buhari ya rasa mahaifansa a lokacin yana da shekara goma (10), wanda kawai zai iya tino cewa mahaifinsa dogo ne kuma mai tsayin halitta.Mahaifiyarsa Hajiya Zulaihatu itace ta raine shi har ya girma yayi makaranta.(p2 Ana kiran Muhammadu Buhari da “Leko” kamar Gambo kenan da hausa saboda an haifeshi ne bayan mahaifiyarsa ta haifi ƴan biyu kuma dukan su-sun rasu, sai aka haifeshi.[5] Sunan Muhammadu Buhari ya samo asali ne daga sunan shahararren masanin ilmin Hadisi wato Muhammad Al-Bukhari wannan ne ya sa duk mai suna Buhari, to cikakken sunan shi ne Muhammadu Buhari. Wannan ya saba wa tunanin mafiya yawan jama'a cewa Muhammad dan Buhari ne. Shi ya sa a tarihin Shugaba Muhammadu Buhari, za a ji sunan mahaifinsa.[1]

IlimiGyara

Muhammadu Buhari ya halarci Katsina Middle school a shekarar 1953.[5] A shekarar 1955 kuma an mayar da makarantar kankiya, lokacin Muhammadu Buhari yana shekarar ƙarshe.[6] Daga nan sai ya tafi Provincial Secondary School a shekarar 1956, ya shiga gidan soja ne a shekarar 1962.[7]. Buhari ya zauna tare da yayanshi mai suna Dauda Daura, a lokacin yayan nashi yana karantarwa a Mai Aduwa Primary School. Banda karatun addinin dayi a gida Buhari ya shiga makarantar firamare ta Daura da Mai’adua, sannan ya je Katsina Model School a shekarar 1953, sai kuma Katsina Provincial Secondary School (wadda ake kira Government College Katsina a yanzu) daga shekarar 1956 har zuwa shekarar 1961.[1]

Aikin sojaGyara

 
Muhammadu Buhari a lokacin yakin neman zabe.

Daga nan ne ya shiga makarantar soji ta Nigerian Military Training College da ke kaduna, inda ya fara aikin soja. Buhari ya ci gaba da karatu a ciki da wajen kasar, a makarantu wadanda suka hada da,: Defence Services Staff College, Wellington, India, a shekarar 1973. Sa'annan kuma Army Mechanical Transport School borden a birnin Borden, na kasar Britania. Karatunsa na karshe shi ne na The United States Army War College (USAWC) a Carlisle, na jihar Pennsylvania, a kasar Amurka inda ya sami digiri na biyu ko kuma Masters Degree a ilmin sanin dabarbarun yaki ko Strategic Studies.[1][8]

Kafin ya zama shugaban kasa a karon farko a shekarar 1983, Buhari ya riƙe wasu manya manyan muƙaman gwamnati waɗanda suka haɗa da gwamnan jihar arewa maso gabas, da ministan man fetur da albarkatun kasa a lokachin mulkin soji.[1]

A shekarar 1983 Buhari da abokansa cikin rundunar sojojin kasar suka yi juyin mulki wa zabebben gwamnatin shehu shagari bayan zargin ta da lalata tattalin arzikin kasar sanadiyyar cin hanci da rashawa a tsakanin ma’ikatan gwamnati da 'yan siyasa.[1]

A cikin gwamnatin da ya jagoranta ba watannin 20, muhimman lamura daya aiwatar a bangaren tattalin arziki shi ne chanza launin kudaden kasar, don raya bankunan da kuma lalata shirin attajiran kasar wadanda suka bobboye kudade a wurere daban daban. Har’ila yau Buhari ya ki amincewa da bukatar Bankin lamuni ta duniya IMF na ya rage darajar Naira da kashi 60%, a maimakon haka ya takaita shigar da kayayyaki daga kasashen waje wadanda zasu cutar da tattalin arzikin kasar da sauransu.[1]

A kokarin gyara halayen yan Nigeria kuma, Buhari ya jefa yan siyasa da dama cikin gidan kaso tare da tuhumar su akan sata da cin hanci da rashawa, sannan ya gabatar da shirin yaki da rashin da’a da nufin kyautata halayen yan Nigeria. Sai dai kamar yadda aka zata ya sha suka daga banagren kungiyoyi da kasashen duniya kan take hakkin bil’adama musamman ma yan jaridu.[1]

Bayan an masa juyin mulki a shekarar 1985 Buhari, gwamnatin Baban gida ta tsreshi na wasu shekaru.[1]

Sai kuma bayan darewar marigayi Sani Abacha kan kujerar shugabancin kasar ya kafa hukumar PTF wacce ta gudanar da ayyukansa da karin kudaden man fetur da aka yi a shekarar 1994. Inda ya mikawa Buhari shugabancin hukumar.[1] PTF ta yi rawar gani a kyautata rayuwar yan Nigeria, PTF ta kyautata bangarori da dama a Nigeria wadanda suka hada da makarantu, kiwon lafiya, hanyoyi da sauransu. Wanda yan Nigeria basu manta da it aba.[1]

Rayuwar Muhammadu BuhariGyara

 
shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da yake zantawa da Sakataren Kasashen Waje na Amurka John Kerry a yayin wani taro da kasar Burtaniya ta shirya a Lancaster don yaki da cin hanci da rashawa

Buhari ne da na 23 a cikin yayan mahaifinsa malam Adamu, sannan ya tashi a hannun mahaifiyarsa mai suna Zulaihatu bayan rasuwar mahaifinsa yana dan shekaru 4 a duniya.

Banda karatun addinin a gida Buhari ya shiga makarantar Primari ta Daura da Mai’adua, sannan ya je Katsina model school a shekarar 1953, sai kuma Katsina Provincial Secondary School (wanda ake kira Government College Katsina a yanzu) daga shekara ta 1956 zuwa shekarar 1961.

Aikin sojaGyara

Daga nan ne ya shiga makarantar soje ta Nigerian Military Training College da ke kaduna , inda ya fara aikin soja. Buhari ya ci gaba da karsatu a ciki da wajen kasar, a makarantu wadanda suka hada da,: Defence Services Staff College, Wellington, India, a shekara 1973. Sannan Army Mechanical Transport School a birnin Borden, na kasar Britania .Karatunsa na karshe shi ne na The United States Army War College (USAWC) a Carlisle, na jihar Pennsylvania, a kasar Amurka inda ya sami digiri na biyu ko kuma Masters Degree a ilmin sanin dabarbarun yaki ko Strategic Studies.

SiyasaGyara

Kafin ya zama shugaban kasa a karon farko a shekarar 1983, Buhari ya rike wasu manya manyan mukaman gwamnati wadanda suka hada da gwamnan jihar arewa maso gabas, da ministan man fetur da albarkatun kasa.

A shekarar 1983 Buhari da abokansa cikin rundunar sojojin kasar suka yi juyin mulki wa zabebben gwamnatin shehu shagari bayan zargin ta lalata tattalin arzikin kasar sanadiyyar cin hanci da rashawa a tsakanin ma’akatan gwamnati da yan siyasa.

A cikin gwamnatin da ya jagoranta ba watannin 20, muhimman lamura daya aiwatar a bangaren tattalin arziki shi ne chanza launin kudaden kasar, don raya bankunan da kuma lalata shirin attajiran kasar wadanda suka bobboye kudade a wurere daban daban. Har’ila yau Buhari ya ki amincewa da bukatar Bakin lamuni ta duniya IMF na ya rage darajar Naira da kashi 60%, a maimakon haka ya takaita shigir da kayaki daga kasashen waje wadanda zasu cutar da tattalin arzikin kasar da sauransu.

A kokarin gyara halayen yan Nigeria kuma, Buhari ya jafa yan siyasa da dama cikin gidan kaso tare da tuhumar sata da cin hanci da rashawa, sannan ya gabatar da shirin yaki da rashin da’a da nufin kyautata halayen yan Nigeria. Sai dai kamar yadda ake zata ya sha suka daga banagren kungiyoyi da kasashen duniya kan take hakkin bi’adama musamman yan jaridu.

Bayan an masa juyin mulki a shekarar 1985 Buhari, gwamnatin Baban gida ta tsareshi na wasu shekaru.

Bayan Mutuwar Abacha a shekarar 1998 da kuma dawowar Democradiyya a shekarar 1999, Buhari ya shiga harkokin siyasa da kuma neman takarar shugabancin kasar a shekaru 2003, 2007, 20011, amma ba tare da samun nasara ba, sai a karo na 4 wato a wannan shekara ta 2015.[9]

Idan muka dubi halin da kasar take ciki a lokacinda Buhari ya sake dawowa a matsayin shugaban kasa a karo na biyu, zamu ga cewa matsalolin da kasar take fama da su sun ninninka wanda ya tarar a a shekara ta 1983. Sai dai ayi masa fatan alheri a cikin gagarumin aikin da ke gabansa.[1]

Shugaban PTFGyara

Sai kuma bayan darewar marigayi Sani Abacha kan kujerar shugabancin kasar ya kafa hukumar PTF wacce ta gudanar da ayyukansa da karin kudaden man fetur da aka yi a shekarar 1994. Inda ya mikawa Buhari shugabancin hukumar.

PTF ta yi rawar gani a kyautata rayuwar yan Nigeria, PTF ta kyautata bangarori da dama a Nigeria wadanda suka hada da makarantu, kiwon lafiya, hanyoyi da sauransu. Wanda yan Nigeria basu manda da it aba.

 
lokacin da Muhammad buhari yayi nasarar zabe a shekara 2015

Bayan Mutuwar Abacha a shekara 1998 da kuma dawowar Democradiyya a shekarar 1999, Buhari ya shiga harkokin siyasa da kuma neman takarar shugabancin kasar a shekaru 2003, 2007, 20011, amma ba tare da samun nasara ba, sai a karo na 4 wato a wannan shekara ta 2015.

 
Mutum Mutumin Shugabar Kasar Najeriya Kenan. Muhammad Buhari.

Idan muka dubi halin da kasar take ciki a lokacinda Buhari ya sake dawowa a matsayin shugaban kasa a karo na biyu, zamu ga cewa matsalolin da kasar take fama da su sun ninninka wanda ya tarar a a shekara ta 1983. Sai dai ayi masa fatan alheri a cikin gagarumin aikin da ke gabansa.

Iyali da dangiGyara

Buhari ne ɗa na 23 a cikin ƴaƴan mahaifinsa malam Adamu, sa'annan ya tashi a hannun mahaifiyarsa mai suna Zulaihatu bayan rasuwar mahaifinsa yana ɗan shekaru 4 a duniya.[1]

DangiGyara

IyaliGyara

Shugaba Muhammadu Buhari ya auri mata biyu a rayuwarsa. Akwai Safinatu Yusuf wacce itace matarsa na farko da ya aura (dagaa 1971 zuwa 1988) kuma ta rasu ta bar manyan yaya kafin ya auri Aisha Halilu a shekarar 1989

'Yaya

Muhammad Buhari yana da 'ya'ya guda goma Wanda suka had a da;

 • Zulaihat (marigayiya)
 • Fatima
 • Musa (marigayi)
 • Hadiza
 • Safinatu
 • Aisha
 • Halima
 • Yusuf
 • Zarah
 • Amina

BibiliyoGyara

 • Atim, Tyodzua. (1998) Muhammadu Buhari: The Making Of a Legend. ISBN: 778-31385-1-0

ManazartaGyara

 1. 1.00 1.01 1.02 1.03 1.04 1.05 1.06 1.07 1.08 1.09 1.10 1.11 1.12 https://www.britannica.com/biography/Muhammadu-Buhari
 2. https://www.globalsecurity.org/military/world/nigeria/muhammadu-buhari.htm
 3. https://www.aljazeera.com/tag/muhammadu-buhari/
 4. 4.0 4.1 Tim, Tyodzua. (1998) Muhammadu Buhari: The Making Of a Legend.p. 1. ISBN 778-31385-1-0
 5. 5.0 5.1 Tim, Tyodzua. (1998) Muhammadu Buhari: The Making Of a Legend.p.5. ISBN 778-31385-1-0
 6. Tim, Tyodzua. (1998) Muhammadu Buhari: The Making Of a Legend.p. 6. ISBN 778-31385-1-0
 7. Tim, Tyodzua. (1998) Muhammadu Buhari: The Making Of a Legend.p.7. ISBN 778-31385-1-0
 8. https://ke.opera.news/ke/en//393cb33173db32ebb97138b1f7ab9236
 9. Shugaban kasa