Danladi Mohammed
Hon. Danladi Mohammed shine kwamishinan tsare-tsaren tattalin arziki na jihar Gombe ta Najeriya .
Danladi Mohammed | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Maiduguri |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Danladi Mohammed da ga Muhammad Pantami da Amina Pantami a ranar 29 ga watan Satumba shekara ta alif ɗari tara da sittin da takwas (1968). Ya fara karatun sa a makarantar firamare ta Jan-Kai da ke jihar Gombe. Ya sami digiri a kan ilimin tattalin arziki a Jami'ar Maiduguri. Ya sami MBA a harkar kudi, daga Jami'ar Abubakar Tafawa Balewa. Ya kuma halarci kwas a kan nazarin siyasa da aiwatar da manufofi a cikin shekara ta 2011 a Global Training Consultation London, an gudanar da jagoranci a cikin shekara ta 2014 a Howard, Washington, DC, Amurka, da kuma kwas ɗin kan kasafin kuɗi don samar da daidaito tsakanin maza da mata a Jami'ar Jihar Bowie a cikin shekara ta 2014.