Abinci
Abinci: wani abu ne mai dauke da sinadarai na yayan itatuwa da tsirrai da dabbobi wadanda ake sarrafawa ta hanyar dafawa, domin ya gamsar ko ya gusar da yunwar ɗan Adam.[1] Misalin tsirrai da yayan itatuwa sune kamar: shinkafa, taliya, macaroni, doya, dankali wake (na Hausa Dana Turawa), masara, hatsi, alkama, dawa, alayyahu, rama, yakuwa, karkashi, kubewa, daudawa, kabewa, zogale, ayayo, tattase, tumatir, tarugu, da kuma kuka, tuwo, da sauransu.
abinci | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | disposable product (en) da physical substance (en) |
Bangare na | Q13538519 |
Amfani | eating (en) |
Kayan haɗi | food ingredient (en) |
Yana haddasa | food allergy (en) da satiety (en) |
Karatun ta | culinary art (en) da food science (en) |
Amfani wajen | organism (en) |
Unicode range (en) | U+2615,U+1F33D,U+1F345-1F37C,U+1F382 |
Hannun riga da | non-food item (en) |
NCI Thesaurus ID (en) | C62695 |
Sinadaran, abinci suna da yawa a fadin duniya inda dan Adam ke buƙatar su domin rayuwar shi.
Ma'anar Abinci gyara sashe
Abinci shine duk wani abu da za'a ci don samun karfi da Lafiyan Jiki da kuma kuzari ga kwayoyin halitta na jikin dan Adam.[2] Yana iya zama danye ko sarrafaffe ko tsararre, dabbobi na cin shi da baki don girma, ko samun lafiya ko jin dadi.
Abinci A Duniya gyara sashe
Abinci a duniya ya banbanta, domin bincike ya nuna cewa, mutane suna cin abinci daban-daban daga faɗin inda suka fito a duniya. Wani lokacin a kasa daya ko kuma jiha daya zaka samu mutane suna rayuwa amma kuma kalar abincinsu daban-daban ne.
Manazarta gyara sashe
- ↑ https://www.britannica.com/topic/food
- ↑ https://en.wikipedia.org/wiki/Food#cite_note-:6-3