Gyaɗa (peanut) wani abinci[1] ne, asalinsa tsiro ne da ake shukawa, yana kuma fitar da ƴaƴa a cikin kasa ƙarƙashin jijiyoyinta. Kuma ana sarrafa shi ne don amfani da shi a matsayin abinci da sauransu ta hanyoyi daban-daban kamar wurin yin kunu[2], mai.[3][4] (mangyada), Madara[5], kuli kuli, ko zubawa a miyar taushe, da sauransu. Ana iya dafa gyada[6] ana iya soyata, ana kuma yin kantu. Gyada[7] na da sinadarin dake gina jiki, "protein" wanda ke da amfani sosai a jiki, musamman ma wajen kara girman jiki da bai wa jiki kariya, shiyasa yake da kyau a riƙa amfani da shi a cikin abinci. Kuma ita gyada ta kasu Kashi daban daban, akwai, Kampala, yar dakkar, Mai bargo da sauransu.[4]

Gyaɗa
oil seed (en) Fassara, nut (en) Fassara da dan-ice
Tarihi
Mai tsarawa Gyaɗa
Gyada a tushen ta
tugaggiyar gyaɗa bayan an ginota kafin a tsigeta daga tushen ta
ƙuli-ƙuli na gyaɗa da kantu
Sa hoto
Peanut collection
haka Gyada yake in'an soya
gyada me bawo
Daffafan gyada

In da ake nomawa

gyara sashe

Yawancin inda suke nomata. Zamfara da Nasarawa da Kaduna da kuma Kwara. Duk dadai yanzu akwai sabon irin gyada da yake yi a jihohin yankin gabashin kasar nan, musamman ma jihohin Enugu da Anambra.[8]

Hanyoyin Sarrafa Gyada

gyara sashe

Ana Sarrafa gyada ta hanyoyi daban-daban kuma ana amfani da ita a duk fadin duniya, sai dai a nan za mu duba kadan ne daga irin hanyoyin da ake sarrafa gyada a matsayin abinci.

  • Madaran Gyada, za a iya yin madara da gyada, idan aka sami danyen gyada sai a bare ta, a wanke sannan kuma a bari ta jiku a ruwa, sai a niketa, idan aka nika sai a tace, bayan an tace sai a dafa, idan ya dahu sai a bar ta ta huce, shikenan an samu madarar gyada, za a iya bai wa yara wadanda ba su samun cikakken abinci domin karin lafiya.
  • Mangyada, za a iya hada mai da gyada idan aka samu gyada aka bare ta, aka bar ta ta bushe, ko kuma aka samu wanda aka riga aka busar, sai a soya ta ba da wuta sosai ba ko kuma za a iya kin soyawa, soyawa ba dole ba ne, idan an soya, sai a nika ta, to, ta zama tunkuza bayan an nika, daga nan sai a matse tunkuzar ta hanyar juyawa, za'a ga mai din na kadan kadan daga jikin tunkuzar.
  •  
    ana sarrafa gyada a samar da man kuli kuli
    Kulikuli, idan anason yinsa za'a bi yanayin da aka bi dan yin mangyda ne, amma a dai-dai lokacin da aka gama fitar da mai din gyadar daga jikin tunkuzar, to tunkuzar da aka riga aka fidda mai acikinta, shine za'a haɗa da sinadirai kamar magi, gishiri, barkono, citta da kuma sikari da sauransu sai a rinka diba ana curawa ana soyawa da mai din da aka fitar, idan aka soya yasoyu, to ansama kulikuli.
 
Gyaɗa wadda ba ɓara ba a cikin bukitai

Gyadar da aka sarrafa

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://hausa.premiumtimesng.com/2024/06/shirin-samar-da-abinci-gwamnan-kano-zai-sayo-wa-manoman-kano-takin-zamani-na-naira-biliyan-5/&ved=2ahUKEwjh9vOjiveGAxUeSEEAHcyACwYQxfQBKAB6BAgPEAI&usg=AOvVaw33ahKAHlMMMWmYGM6UrmJc
  2. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://dailytrust.com/cholera-fg-asks-nigerians-to-avoid-locally-prepared-kunu-zobo/&ved=2ahUKEwjV9eO7iveGAxUIZ0EAHR79Cb0QxfQBKAB6BAgFEAI&usg=AOvVaw0RHiougysLpROT0LScucDs
  3. https://www.voahausa.com/a/cin-kwayaoyi-dangin-su-gyada-bashi-da-matsala-ga-mata--ga-mata-masu-ciki/1831526.html
  4. 4.0 4.1 https://www.muryarhausa24.com.ng/2019/10/karanta-jerin-abincin-hausawa-kafin-zuwan-yar-thailand-kafin-zuwan-shinkafa-yar-ƙasashen-waje-girke-girken-gargajiya-sunayen-abincin-gargajiya-abincin-zamani-filin-girke-girke-abincin-zamani-filin-girke-girke.html
  5. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/labarai-53648022.amp&ved=2ahUKEwiO55nriveGAxVkW0EAHfrjCt8QyM8BKAB6BAgNEAI&usg=AOvVaw35Q7RRfrfA4uWo1iVNfewv
  6. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://hausa.leadership.ng/uwargidan-gwamnan-kebbi-ta-tallafawa-mata-500-da-buhunan-gyada-da-tsabar-kudi/&ved=2ahUKEwiVwab_iveGAxVQSEEAHcQGBGIQxfQBKAB6BAgNEAI&usg=AOvVaw29zgtRSKX1HtpA6G1F-IIc
  7. https://proveg.com/ng/recipes/kunnu-gyada/
  8. https://aminiya.dailytrust.com/sarrafa-albarkatun-gona-gyada-3/