Ibrahim Hassan Dankwambo

Gwamnan jihar Gombe, Nigeria

Ibrahim Hassan Dan kwambo An haife shi a ranar 4 ga watan Afrilu a shekara ta alif da ɗari tara da sittin da biyu, 1962 a unguwar Herwagana dake garin Gombe [1]. Dan Nijeriya ne, kuma dan siyasa wanda shine tshohon gwamnan Jihar Gombe, dake arewacin Nijeriya. Kuma tsohon Accountant General na kasa.

Ibrahim Hassan Dankwambo
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

13 ga Yuni, 2023 -
District: Gombe North
gwamnan jihar Gombe

Mayu 2011 - 29 Mayu 2019
Mohammed Danjuma Goje - Muhammad Inuwa Yahaya
District: Gombe North
Rayuwa
Haihuwa Gombe, 4 ga Afirilu, 1962 (62 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Ƴan uwa
Abokiyar zama Adama
Yara
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Jami'ar Lagos
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Mai tattala arziki da ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party

[2]

Tarihin rayuwarsa da karatun sa gyara sashe

Ya kammala karatun digirin sa na farko a jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya a shekarar alif da ɗari tara da tamanin da biyar, 1985, inda ya karanci Accounting. Baya haka ya samu nasarar kammala karatun sa na Masters a fannin Economic a Jami'ar Legas a shekarar alif dari tara da chasain da huɗu, 1994.[3] Sannan ya kammala PhD ɗinsa a fannin Accounting a Jami'ar Igbinedion.[4]

Ya fara aikinsa da Coopers & Lybrand a shekarar alif dari tara da tamanin da biyar, 1985, sannan yayi aiki da Babban Bankin Najeriya daga shekarar 1988 zuwa 1999. A wancan lokacin ne aka sanya shi akaunta janar (Accountant General) na jahar Gombe, ya riƙe wannan matsayi har shekarar dubu biyu da biyar, 2005.[5] Ya riƙe wannan ofishin har sanda ya ajiye saboda ya fara neman takarar sa ta kujerar Gwamnan jihar Gombe a watan junairun 2011.[6]

Siyasa gyara sashe

Ibrahim Dankwambo ya samu nasarar lashe zaben gwamna a jihar Gombe a ranar 26 ga watan Afrilu a shekara dubu biyu da shaɗaya, 2011. Ya lashe zaɓen ne da ƙkuri'u 596,481 inda ya mawa Alhaji Abubakar Aliyu na jami'ar APC fintakau wanda yake da ƙuri'u 91,781 da sanata Sa'idu Umar Kumo na jam'iyyar ANPP mai ƙkuri'u 84,959.[7]

Yana kan karagar mulki ne, Dankwambo ya rasa mataimakin sa, David Miyims Albashi, wanda ya rasu a ranar 4 ga watan Nuwamba shekarar dubu biyu da goma sha ɗaya a asibitin Jamani yayin jinya da yakeyi saboda hatsarin mota a ranar 28 a watan Agusta shekarar 2011.[8] A 17 ga watan Disamban shekara ta dubu biyu da shaɗaya, 2011, Dankwambo ya sanya Tha'anda Rubainu a matsayin mataimakin Gwamnan.[9] Bayan sake zaɓen sa na shekarar 2015, Charles Yau shine ya kasance mataimakin Gwamna har ya zuwa ƙarshen tenuwan sa na biyu a shekarar dubu biyu da goma sha tara, 2019.[10] Shine jigon jam'iyyar PDP a jahar Gombe kuma ɗan takarar sanatan Gombe ta arewa a zaɓen da za'a gabatar a shekarar 2023.[11][12]

Manazarta gyara sashe

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
  1. https://m.guardian.ng/tag/alhaji-ibrahim-hassan-dankwambo/
  2. https://ng.opera.news/tags/ibrahim-hassan-dankwambo[permanent dead link]
  3. https://www.cbn.gov.ng/aboutcbn/TheBoard.asp?Biodata=dankwambo&Name=Alhaji+Ibrahim+Hassan+Dankwambo,+OON
  4. http://thenationonlineng.net/gov-dankwambo-bags-phd-igbinedion-varsity/
  5. http://sunday.dailytrust.com/index.php?option=com_content&view=article&id=5720:day-ibrahim-hassan-dankwambos-home-coming-turned-carnival&catid=16:community-news-pyramid-trust&Itemid=28
  6. http://sunday.dailytrust.com/index.php?option=com_content&view=article&id=5720:day-ibrahim-hassan-dankwambos-home-coming-turned-carnival&catid=16:community-news-pyramid-trust&Itemid=28
  7. http://allafrica.com/stories/201104280577.html
  8. https://www.vanguardngr.com/2011/11/gombe-state-deputy-governor-passes-on/
  9. https://t.guardian.ng/slide/governor-ibrahim-dankwambo-of-gombe-state-lmiddle-with-the-deputy-mr-tha-anda-rubainu-right-and-director-general-of-his-campaign-organisation-at-a-campaign-in-kaltungo-on-january-4-2015/
  10. https://dailytrust.com/deputy-governors-series-6
  11. https://guardian.ng/news/nigeria/dankwambo-is-gombe-north-pdp-senatorial-candidate/
  12. https://dailypost.ng/2022/05/23/2023-dankwambo-picks-pdp-gombe-north-senatorial-ticket/