Muhammad Inuwa Yahaya
Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya (an haife shi a ranar 9 ga watan Oktoba[1], a shekara ta alif ɗari tara da sittin da ɗaya, 1961)[2] Dan Najeriya ne, Dan kasuwa[3], kuma Dan siyasa. Shi ne gwamnan Jihar Gombe[4] wanda aka zaɓa a ranar 9 ga watan Maris a shekara ta dubu biyu da goma sha tara, 2019 ƙarƙashin jam'iyyar All Progressive Congress (APC).[5]
Muhammad Inuwa Yahaya | |||
---|---|---|---|
29 Mayu 2019 - ← Ibrahim Hassan Dankwambo | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Muhammad Inuwa Yahaya | ||
Haihuwa | Jihar Gombe, 9 Oktoba 1961 (63 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mazauni | Jihar Gombe | ||
Ƙabila | Hausawa | ||
Harshen uwa |
Hausa Fillanci | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello | ||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya Fillanci Larabci Waja (en) Tangale (en) Bolanci Harshen Pero | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa, ɗan kasuwa, governor (en) da investor (en) | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci | ||
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Farkon Rayuwa
gyara sasheAn haifi Muhammadu Inuwa Yahaya a ranar 9 ga watan Oktoba, shekara ta alif ɗari tara da sittin da ɗaya (1961) a anguwar Jekadafari, a garin Gombe, Jihar Gombe. Mahaifinsa, Alhaji Yahaya Umaru, shahararren ɗan kasuwa ne a garin Gombe.[6]
Karatu
gyara sasheBayan kammala karatun sa na firamare da sakandare, Muhammad Inuwa yasamu gurbin cigaba da karatu a babban makarantar gaba da sakandare a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria[7], inda ya karanta lissafi na fannin banki (Accounting) a shekara ta alif ɗari tara da tamanin da uku, 1983.[6]Ya samu shaidar Bachelor's degree.[8]
Siyasa
gyara sasheAlhaji Muhammad Inuwa Yahaya ya tsunduma cikin siyasa a shekara ta dubu biyu da uku, 2003. Amma ya yi suna ne a shekara ta dubu biyu da goma sha biyar (2015), inda ya zama ɗan takarar gwamna a jam'iyar All Progressive Congress (APC) na jihar Gombe. A ɗaya ga watan Oktoba, shekara ta dubu biyu da goma sha takwas (2018) ya sake lashe zaɓen cikin gidan jam'iyar All Progressive Congress (APC), a karo na biyu dan yin takarar gwamnan Jihar Gombe a babban zaɓen Najeriya na shekara ta dubu biyu da goma sha tara, 2019.[9][10]
Alhaji Muhammad Inuwa Yahaya yayi nasara a zaɓen shekara ta dubu biyu da goma shatara 2019 wanda ya gudana ranan 9 ga watan Maris, shekara ta dubu biyu da goma sha 2019. Ya samu adadin ƙuri'u 364,179, inda ya buge abokin takararsa na jam'iyar Peoples Democratic Party (PDP), Sen. Usman Bayero Nafada wanda yasamu tashi adadin ƙuri'un 222,868.[11]
Yanzu haka gomna ne a jihar Gombe.
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.voahausa.com/amp/manuniya-batun-kudin-da-aka-ce-yan-majalisar-najeriya-ke-samu-oktoba-20-2024/7318926.html&ved=2ahUKEwj988iH9PaGAxVpX_EDHaOsAb0QyM8BKAB6BAgFEAI&usg=AOvVaw3ZjbJTPcUOiqDfPkQOAmUZ
- ↑ https://www.bing.com/ck/a?!&&p=5cdf3e006abedfeeJmltdHM9MTcxOTAxNDQwMCZpZ3VpZD0yNDE5NGEyMS03NTBiLTZiYjItMzNmMi01ZTg1NzRhMTZhMTkmaW5zaWQ9NTIyOA&ptn=3&ver=2&hsh=3&fclid=24194a21-750b-6bb2-33f2-5e8574a16a19&psq=Alhaji+Muhammadu+Inuwa+Yahaya+biography&u=a1aHR0cHM6Ly9wb2xpdGljaWFuc2RhdGEuY29tL2NvbnRlbnQvbXVoYW1tYWQtaW51d2EteWFoYXlhLw&ntb=1
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/articles/cx7l9925de2o.amp&ved=2ahUKEwiWru3O9PaGAxVpQUEAHbOnBeQQyM8BKAB6BAgMEAI&usg=AOvVaw0CDqBUZoAJ4auqFshjWUYO
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://dailynigerian.com/low-rainfall-forces-gombe/&ved=2ahUKEwiunpis9PaGAxXVRPEDHZ8WCzAQxfQBKAB6BAgNEAI&usg=AOvVaw27FMzYM3puOixfqOK9Fet3
- ↑ Published. "INEC declares APC's Inuwa Yahaya Gombe Gov-elect". Punch Newspapers (in Turanci).
- ↑ 6.0 6.1 "Brief biography of Gombe State Governor-Elect". Daily Trust (in Turanci). 2019-03-19. Archived from the original on 2019-03-20. Retrieved 2019-06-16.
- ↑ https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.thisdaylive.com/index.php/2024/06/21/abu-zaria-honours-apitainment-ceo-with-distinguished-personality-award/&ved=2ahUKEwji4c3q9PaGAxXwXUEAHeh8B2UQxfQBKAB6BAgSEAI&usg=AOvVaw0LOhdutn5Qtd-GGtbLIy5s
- ↑ https://dailytrust.com/brief-biography-of-gombe-state-governor-elect/
- ↑ editor (2018-10-01). "APC Votes Yahaya as Gombe Guber Candidate". THISDAYLIVE (in Turanci).CS1 maint: extra text: authors list (link)
- ↑ "Gombe 2019: The game changers". Tribune Online (in Turanci). 2018-09-25. Archived from the original on 2019-06-16. Retrieved 2019-06-16.
- ↑ https://dailytrust.com/brief-biography-of-gombe-state-governor-elect/