Jihar Arewa ta Gabas

Tsohuwar Jiha a Najeriya

Jihar Arewa-maso-Gabas tsohuwar yanki ce ta mulkin aNajeriya. An kirkire ta ne a ranar 27 ga watan Mayun 1967 daga sassan Yankunan Arewa. Babban birnin Jihar itace birnin Maiduguri. Yankin Arewa-maso-gabas ta shahara wajen noma da isasshen abinci.[ana buƙatar hujja]

Jihar Arewa ta Gabas

Wuri
Map
 11°50′00″N 13°09′00″E / 11.833333°N 13.15°E / 11.833333; 13.15
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Maiduguri
Bayanan tarihi
Mabiyi Arewacin Najeriya
Ƙirƙira 27 Mayu 1967
Rushewa 3 ga Faburairu, 1976
Ta biyo baya Jihar Bauchi, Jihar Borno da Jihar Gongola
Jihar Arewa maso Gabas, tare da sunayen jihohin da suka gaje su.

A ranar 3 ga watan Fabrairun 1976 aka raba jihar zuwa jihohin Bauchi, Borno da Gongola. Daga baya an cire jihar Gombe daga Jihar Bauchi, jihar Yobe daga Borno sannan yankin Gongola ta rabu zuwa jihar Taraba da Adamawa.[1]

Gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas gyara sashe

  • Musa Usman ( tsakanin 28 May 1967 – Yuli 1975)
  • Muhammadu Buhari (daga July 1975 - Fabrairu 1976)

Manazarta gyara sashe

  1. "This is how the 36 states were created". Pulse Nigeria. 2017-10-24. Retrieved 2021-07-12.