Abubakar Shehu-Abubakar (An haife shi a ranar 17 ga watan Disamba[1], na shekarar alif dubu daya da dari tara da sabin da bakwai 1977, Gombe[2], Nigeria[3]) shi ne shugaban gargajiyar Nijeriya[3] wanda aka nada shi a matsayin Sarkin Gombe na goma sha ɗaya (11) a watan Yunin, shekara ta 2014.[4] [5] Kuma shine shugaban sarakunan masarautun jihar Gombe.[2] Ya zama Sarki ne bayan rasuwar mahaifinsa, Shehu Abubakar, sarki na goma (10), wanda ya mutu a ranar 27 ga Mayu, 2014.[6][7] Abubakar Shehu-Abubakar shine da na biyu na Shehu Abubakar.

Abubakar Shehu-Abubakar
Emir of Gombe (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Jihar Gombe, 17 Disamba 1977 (46 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Mahaifi Shehu Abubakar
Karatu
Makaranta Kwalejin Barewa
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a emir (en) Fassara


An haifi Abubakar Shehu-Abubakar a garin Gombe, Najeriya. Ya halarci makarantar firamaren yara ta Gombe daga shekara ta 1982 zuwa 1988 da kuma makarantar sakandaren kimiyya ta gwamnati, Gombe, daga shekara ta 1989 zuwa 1995. Shehu-Abubakar ya sami digiri na farko a fannin kimiyyar siyasa daga jami’ar Maiduguri[8], inda ya kasance dalibi daga shekara ta 2001 har zuwa kammala karatunsa a shekara ta 2005 Abubakar ya yi aiki a matsayin kansilan mai kulawa a Majalisar Karamar Hukumar Gombe daga shekara ta 2006 zuwa 2007. [9]Daga shekara ta 2007 har zuwa shekara ta 2009, ya yi aiki a matsayin mai taimaka wa Daraktan Gudanarwa a Ma’aikatar Tsaro ta Tarayyar da ke Abuja. Daga baya ya zama shugaban kamfanin Kliptown Lagoon Nigeria Ltd. da babban darakta na Horizon Interlinks Global Resources.

 
Abubakar Shehu-Abubakar a cikin mutane

Mahaifin Abubakar Shehu-Abubakar, Sarkin Gombe na goma (10) wato Shehu Abubakar, ya mutu sakamakon cutar kansa a kasar Landan a ranar 27 ga Mayu, 2014. An naɗa shi a matsayin magajin Shehu Abubakar, a farkon watan Yunin 2014. Sakataren Gwamnatin Gombe (SSG), Abubakar Bage, ya gabatarwa da Shehu-Abubakar wasiƙar nadin nasa a Babban Masallacin Gombe a ranar 6 ga Yuni, 2014.

Manazarta

gyara sashe
  1. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.rfi.fr/ha/shirye-shirye/tattaunawa-da-ra-ayin-masu-saurare/20240206-an-shiga-rudani-a-senegal-sakamakon-dage-zaben-kasar-zuwa-disamba&ved=2ahUKEwjajPvZ8PaGAxW1QEEAHThTAlgQxfQBKAB6BAgLEAI&usg=AOvVaw2DIY0phyUqo9pX8oDPUgaf
  2. 2.0 2.1 https://www.sunnewsonline.com/gombe-community-weeps-as-emir-dies-16-months-after-coronation/
  3. 3.0 3.1 https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://guardian.ng/roofing-sheet-maker-aarti-steel-quits-nigeria/&ved=2ahUKEwihgfv48PaGAxUUUkEAHWNkDiMQxfQBKAB6BAgIEAI&usg=AOvVaw3rDYX-bYHnhFfsECC9S3wi
  4. https://archive.is/20140624023912/http://www.ngrguardiannews.com/news/national-news/164757-govt-appoints-new-emir-of-gombe
  5. https://www.premiumtimesng.com/news/162207-gombe-gets-new-emir.html
  6. https://allafrica.com/view/group/main/main/id/00030638.html
  7. http://www.pmnewsnigeria.com/2014/05/27/emir-of-gombe-dies-at-76/
  8. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://aminiya.ng/kotu-ta-%25C9%2597aure-farfesan-jamiar-maiduguri-shekaru-biyu/&ved=2ahUKEwjGwYWi8faGAxVnXEEAHYc9DJIQxfQBKAB6BAgPEAI&usg=AOvVaw0Mhw5TCUxyAy7oRLPAeLVh
  9. ab cd ef g hi jkl "Govt appoints new Emir of Gombe". The Guardian (Nigeria) . 2014-06-06. Archived from the original on 2014-06-24. Retrieved 2014-06-23.