Abubakar Habu Hashidu
Abubakar Habu Hashidu (10 ga watan Afrilu shekarar 1944 - 27 ga watan July shekarar 2018) ɗan siyasan Nijeriya ne kuma tsohon gwamnan jihar Gombe, Nijeriya daga watan Mayu shekarar 1999 zuwa watan Mayu shekarar 2003.
Abubakar Habu Hashidu | |||
---|---|---|---|
29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2003 ← Mohammed Bawa - Mohammed Danjuma Goje → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jihar Gombe, Bauchi da Dukku, 10 ga Afirilu, 1944 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Hausawa | ||
Harshen uwa |
Hausa Tula (gari) Fulani | ||
Mutuwa | Jihar Gombe, 27 ga Yuli, 2018 | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Ahmadu Bello University of New Hampshire (en) Utah State University (en) University of Missouri (en) Lincoln University (en) University of Pittsburgh (en) | ||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya Harshen Tula Mutanen Fulani | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | All Nigeria Peoples Party |
Hashidu ya kasance ministan Albarkatun Ruwa sannan kuma ya kasance Ministan Noma da Raya Karkara a lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Babangida. Ya kuma kasance memba na kwamitin hangen nesa na shekarar 2010 wanda Janar Sani Abacha ya kafa don tsara taswirar ci gaban kasa
Siyasa
gyara sasheHashidu shi ne kuma zababben gwamnan jihar Gombe na farko, da ya hau mulki a ranar 29 ga watan Mayu, shekarar 1999, a karkashin jam'iyyar All People Party (APP). Mataimakinsa shine Joshua Lidani.
A watan Janairun shekarar 2003 All Nigeria Peoples Party ta amince da Hashidu a matsayin dan takararta na gwamna a zaben watan Afrilun shekarar 2003. Ba a sake zabarsa ba kuma ya yarda da yabo ga Hukumar Zabe ta Kasa. Ya kuma sake zama dan takarar gwamnan jihar Gombe a shekarar 2007 a karkashin jam'iyyar DPP. An kama shi a cikin watan Maris shekarar 2007 kuma aka gabatar da shi a gaban kotu kan rikicin da ake zargin ya barke bayan ya fara kamfen din siyasa. Magoya bayan da ke ɗauke da makamai sun kutsa kai a kotun majistare, inda suka ‘yanta Hashidu tare da raunata alkalin da ke shari’ar tasa.
Mutuwa
gyara sasheHashidu ya mutu a gidansa a safiyar ranar 27 ga watan Yulin na shekarar 2018, bayan fama da rashin lafiya.[1]