Majalisar Ɗinkin Duniya dai tsari ne wanda kasashen duniya suka amince da kerawa domin magance rikice-rikice da yake faruwa bayan yakin duniya na Biyu (2). An kafa ta ne a shekara ta alif dubu daya da dari tara da arba'in da biyar 1945, domin samar da kwanciyar hankali a cikin duniya baki daya. Kuma ta kunshi kusan dukkanin kasashen duniya, banda kasashe biyu; palestinu da Saint-siege. Muhimmin, Jawabin da Majalisar ɗinkin duniya ta bayyana game da Hakkokin 'Yan-adam a shekara ta alif dubu daya da dari tara da arba'in da takwas 1948.

Majalisar Ɗinkin Duniya

Hymn to the United Nations (en) Fassara
Bayanai
Suna a hukumance
United Nations, 联合国, Organización de las Naciones Unidas, Организация Объединённых Наций, منظمة الأمم المتحدة, Organisation des Nations unies, Vereinte Nationen da Organizacja Narodów Zjednoczonych
Gajeren suna 🇺🇳, ONU, OSN, UN, БДО, PBB, BM, FN, YK, ONU, ÜRO, PBB, ONU, ООН, VN, ONZ, ANO, UN, UN, VN, 国連 da או"מ
Iri intergovernmental organization (en) Fassara da international organization (en) Fassara
Ƙasa Tarayyar Amurka
Ideology (en) Fassara internationalism (en) Fassara
Aiki
Bangare na United Nations System (en) Fassara
Ƙaramar kamfani na
Mulki
Shugaba António Guterres
Sakatare António Guterres
Mamba na board
Hedkwata New York
Subdivisions
Tsari a hukumance intergovernmental organization (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 1945
Wanda ya samar
Wanda yake bi League of Nations (en) Fassara
Awards received

un.org


gini Majalisar Ɗinkin Duniya
majalisar dinkin duniya
Majalisar Ɗinkin Duniya

Tarihin Majalisar Ɗinkin Duniya.

gyara sashe

Koda yake kafin kafuwar Majalisar ta Ɗinkin Duniya akwai wasu ƙungiyoyi da aka kafa domin haɗin kai da cigaban ƙasashen duniya, irin su ƙungiyar ma'aikatan sadarwa ta ƙasa da ƙasa a shekara ta alif dubu daya da dari takwas da sittin da biyar 1865, da kuma ƙungiyar ma'aikatan gidajen wasiƙu a shekara ta alif dubu daya da dari takwas da casa'in da hudu 1874. Wa'yanda daga bisani suka rikiɗe zuwa hukumomin Majalisar ta Ɗinkin Duniya bayan da aka kafa ta.

Taron farko da aka gudanar a ƙarƙashin lemar Majalisar Ɗinkin Duniya itace wanda aka gudanar a birnin Hague. Wannan taro dai shine yakai ga kafa kotun duniya dake birnin na Hague a ƙasar Holland a shekara ta alif dubu daya da biyu 1902.

A shekara ta alif dubu daya da dari tara arba'in da biyar 1945 ne ƙasashen duniya hamsin 50 suka gudanar da taro a Jihar San Francisco na Amurika domin ƙaddamar da dokoki ko jadawalin aiyukan ta Majalisar Ɗinkin Duniya. Manyan ƙasashen duniya da suka rattaba hannu a wannan yarjejeniyar dai sun haɗa da Amirka da China da Tarayyar Rasha da Birtaniya da kuma Faransa, wa'yannan ƙasashen ne kuma daga bisani suka zama wakilai na dindindin na masu ƙarfin faɗa aji.

A ranar ashirin da hudu 24 ga watan Oktoban shekara ta alif dubu daya da dari tara da arba'in da biyar 1945 ne dai wa'yannan ƙasashe suka rattaba hannu a daftarin ƙarshe da ya kafa Majalisar ta Ɗinkin Duniya, abinda ma yasa a duk ranar ashirin da hudu 24 ga watan na oktoba Majalisar ke bikin zagayowar ranar da aka kafa ta. Kuma a bana Majalisar ta cika shekaru sittin da hudu 64 da kafuwa. Kuma tun bayan kafuwan ta tayi shugabanni da dama kuma na baya bayan nan sune Butrus Butrus Ghali daga Masar da Kofi Annan na Ghana da kuma maici yanzu Ban Ki-Moon daga ƙasar Koriya ta Kudu. [1]

 
Tambarin Majalisar Ɗinkin Duniya
 
Majalisar Ɗinkin Duniya
 
  Membobin Majalisar Dinkin Duniya
  Jahohin Masu Sa ido na Majalisar Dinkin Duniya (Palestine, Vatican)
  Ƙasashen da ba mamba ba (Niue, Cook Islands)
  Ƙasashen Masu Mulkin Kai
  Antarctica (yankin duniya)

Manazarta

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe