Sani Abacha
Muhammad Sani Abacha. An haife shi ne a ranar 20 ga watan Satumba, a shekara ta alif ɗari tara da arba'in da uku (1943A.C) Miladiyya.[1] Shi tsohon Janar ne na soja. Haifaffen Kano, da ke Arewacin Najeriya (a yau jihar Kano). Ya mutu a ranan talata 8 ga watan Yuni a shekara ta alif ɗari tara da chasa'in da takwas 1998.[2] Sani Abacha shugaban Ƙasar Najeriya ne daga watan Nuwamba, a shekarar alif ɗari tara da chasa'in da uku 1993 zuwa watan Yuni shekarar alif ɗari tara da chasa'in da takwas 1998 (bayan Ernest Shonekan - kafin Abdulsalami Abubakar).[3]
![]() | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
17 Nuwamba, 1993 - 8 ga Yuni, 1998 ← Ernest Shonekan - Abdulsalami Abubakar →
ga Augusta, 1990 - Nuwamba, 1993 ← Domkat Bali (en) ![]() ![]()
ga Augusta, 1985 - ga Augusta, 1990 ← Ibrahim Babangida - Salihu Ibrahim →
| |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Kano, 20 Satumba 1943 | ||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||
Harshen uwa | Hausa | ||||||||
Mutuwa | Aso Rock Villa, 8 ga Yuni, 1998 | ||||||||
Makwanci | Kano | ||||||||
Yanayin mutuwa |
unnatural death (en) ![]() | ||||||||
Ƴan uwa | |||||||||
Abokiyar zama | Maryam Abacha 1998) | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta |
Mons Officer Cadet School (en) ![]() | ||||||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa da soja | ||||||||
Aikin soja | |||||||||
Digiri |
lieutenant general (en) ![]() | ||||||||
Ya faɗaci |
Yaƙin basasar Najeriya First Liberian Civil War (en) ![]() | ||||||||
Imani | |||||||||
Addini | Musulunci | ||||||||
Jam'iyar siyasa |
independent politician (en) ![]() | ||||||||
![]() |

Sani Abacha ya kasance shugaban hafsan sojojin ƙasa na Najeriya, tun daga shekarar alif ɗari tara da tamanin da biyar 1985 zuwa shekarar ta alif ɗari tara da chasa'in dai-dai 1990. sannan kuma shugaban tsaron Najeriya daga shekarar alif ɗari tara da chasa'in dai-dai 1990 har zuwa shekara ta alif ɗari tara da chasa'in da uku 1993, sannan daga bisani kuma Ministan Tsaro na ƙasa.
Matakan da ya kai a Soja gyara sashe
Mutuwa gyara sashe
A ranar 8 ga watan Yuni a shekarar alif ɗari tara da chasa'in da takwas 1998, Abacha ya rasu a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa dake Abuja. An yi jana’izarsa a wannan ranar kamar yadda addinin musulunci ya tanada ba tare da tantance gawar shi ba, wanda hakan ya kara rura wutar hasashen da ake yi na cewa kashe shi akayi.[4] Sai dai Gwamnati ta bayyana dalilin mutuwarsa a matsayin bugun zuciya wanda ya taso mashi ba zato ba tsammani.[5] Jami'an diflomasiyya na ƙasashen waje, ciki har da manazarta leƙen asirin Amurka, sun bayyana cewa mai yiwuwa an sanya masa guba ne. Babban jami’in tsaronsa Hamza al-Mustapha ya yi imanin cewa wasu jami’an Isra’ila ne suka sanya masa guba a cikin kamfanin Yasser Arafat ta hanyar gaisawa (wato Nussbaum) daga wannan lokacin ne ya fara ganin canji a jikin shugaban.[6] Wanda har ake tunanin an sanya masa guba ne a Tuffa (Apple). Kafin mutuwarsa, yana gab da miƙa mulki ga gwamnatin farar hula a watan Oktoba shekarar alif ɗari tara da chasa'in da takwas 1998, wanda aka aiwatar a watan Oktoban shekarar alif ɗari tara da chasa'in da biyar 1995.[7] Bayan rasuwar Abacha, Janar Abdulsalami Abubakar ya zama shugaban ƙasa, wanda A dalilin gajeren wa'adinsa yasa aka samu Jamhuriyar Najeriya ta huɗu.[8]
Manazarta gyara sashe
- ↑ "Sani Abacha". Opera News.
- ↑ Kaufman, Michael T. (9 June 1998). "NEW CHAPTER IN NIGERIA: THE OBITUARY; Sani Abacha, 54, a Beacon of Brutality In an Era When Brutality Was Standard". Nytimes.com. Retrieved 11 February 2023.
- ↑ {cite news|url=https://ng.opera.news/tags/sani-abacha%7Ctitle=Sani Abacha}
- ↑ "General Sani Abacha Profile". Africa Confidential. Retrieved 12 February 2023.
- ↑ Weiner, Tim (11 July 1998). "U.S. Aides Say Nigeria Leader Might Have Been Poisoned". The New York Times. Retrieved 12 February 2023.
- ↑ Opejobi, Seun (2017-06-19). "Details of how Abacha died in 1998 – Al-Mustapha". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-02-12.
- ↑ "BBC News | Analysis | Nigeria: General Abacha's era of dictatorship".
- ↑ "Sani Abacha: Timeline of the late Nigerian dictator's life". BBC News (in Turanci). Retrieved 2023-02-12.