Ganuwa wata katanga ce da ake yi a duk gari, domin kare kai daga harin abokan hamayya, musamman a zamanin da. ita wannan ganuwa ana saka bayi ne su haka rami sai su tarar kasar tazama kamar wata jigawa da haka ne idan abokan gaba sun kawo hari to da zarar ankulle kofofin gari shikenan sai dai su koma idan kuwa suka hau ta kan ganuwa to zasu gangaro ne su fada cikin ruwa ko kuma dakarun garin su kashesu. Idan kaje manyan garuruwan hausawa zaka samu wannan ganuwa kamar kano katsina da kuma daura

Wikidata.svgGanuwa
Ganuwa a Jihar Kano