Lagos (jiha)
Jihar Lagos jiha ce da ke kudu maso yammacin Najeriya. Acikin duka jihohin Najeriya, itace jiha mai Mafi yawan jama'a, Kuma itace mafi banbanta ta fuskar
Lagos | |||||
---|---|---|---|---|---|
Lagos State (en) Ìpínlẹ̀ Èkó (yo) | |||||
| |||||
| |||||
Suna saboda | Lagos | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | ||||
Babban birni | Ikeja | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 11,000,598 (2016) | ||||
• Yawan mutane | 3,075.37 mazaunan/km² | ||||
Harshen gwamnati | Turanci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Yawan fili | 3,577 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Tekun Guinea da Lagos Lagoon | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Ƙirƙira |
1472: Port settlement (en) 27 Mayu 1967 | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Majalisar zartarwa | Majalisar Zartaswa ta Jihar Legas | ||||
Gangar majalisa | Lagos State House of Assembly | ||||
• Gwamnan Legas | Babajide Sanwo-Olu (29 Mayu 2019) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | NG-LA | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | lagosstate.gov.ng |
Girma. Ta hada iyaka da daga kudu da Bight of , daga yamma kuwa da iyaka na kasa da kasa da Jimhurriyar Benin, Jihar Legas ta hada iyaka da Jihar Osun daga gabas da kuma yamma wanda hakan ya sanya ta zamo jiha kadai da ta hada iyaka da wata jiha daga bangarori guda biyu. Ta samo sunanta daga babban birnin na Legas, wanda itace birni mafi girma ta fuskar yawan jama'a a Afirika. Jihar ta samo asali ne daga Jihar Yammacin Najeriya kuma tsohuwar Babban Birnin Najeriya a ranar ashirin da bakwai 27, ga watan Mayun shekara ta dubu daya da dari tara da sittin da bakwai 1967.
Ta fuskar yanayin kasa, Jihar mamaye take da ruwaye wadanda suka mamaye adalla Kason uku cikin hudu na fadin jihar wanda suka hada suka hada da ta kuna, creek da kuma koguna. Mafi girmansu sune tafkin lagoon dake Legas da kuma Lekki a yankin cikin garin inda ruwa daga kogin Osun da na Ogun ke kwararar a cikinsu. Koramu da tafkuna da dama na kwarara a cikin garin kuma suna cikin muhimman hanyoyin sufuri na mutane da kaya a jihar. Akan kasa kuwa, akwai kauyuka da dama a yankunan barin jihar wadanda ke da dabbobi da suka fara kwarewa kaman birrai nau'in Mona, tree pangolin, angulu da sauran tsirarun nau'ikan giwayen Afirka a dazukan. Acikin ruwa kuwa akwai dabbobi iri-iri wadanda suka hada da dabbar African manatee da kadoji.
Kabilu da dama ne ke zaune a Jihar Legas na tsawon shekaru tare da kabilar Yarbawa a matsayin asalin mazauna garin wadanda ke zaune a ko ina a fadin jihar tare da mutanen Ewe da Mutanen Ogu daga can kuryar yammacin jihar. A dalilin hijira da ya wanzu tun a karni na 19, mutane iri iri 'yan asalin Najeriya da kasahen kewaye ke zaune a yankin kamar Mutanen Edo, Fulani, Hausawa, Igbo, Mutanen Ijaw, Mutanen Ibibio da Nufawa da dai sauransu. Har wayau akwai kabilu daga kasashen wajen Najeriya ta yau wnda suka hada da Saro (Mutanen kasar Sierra Leone) da kuma Amaro (Mutanen Brazil) da ke zaune a Najeriya wadanda iyalai ne na bayi da suka dawo Afirka a karni na dubu daya da dari takwas 1800. Tare da sauran 'Yan gudun hijira na kwanannan daga yankunan kasashen Sin, Ghana, Indiya, Togo da kuma Birtaniya wadanda ke taka muhimmin rawa a bangaren bunkasar yawan mutanen jihar. Ta fuskar addinai kuwa, Jihar ta rarrabu tsakanin kaso Hamsin da biyar 55% a Matsayin kiristoci, musulmai kuma Kusan kimanin kaso arba'in 40%, da kuma kaso biya 5% wadanda ke bin addinan gargajiya ko wani hakan.
Tana da yawan fili kimani na kilomita araba’in 3,577, da yawan jama’a miliyan sha bakwai da dubu dari biyar da hamsin da biyu da dari tara da arba'in (jimillar shekarar dubu biyu da sha biyu 2012). Babban birnin tarayyar jahar ita ce Legas. Babajide Sanwo-Olu, shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta dubu biyu da sha biyar 2015, har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Oluranti Adebule. Dattijai a jihar sun hada da: Bola Tinubu, Oluremi Tinubu, Solomon Olamilekan Adeola da Gbenga Bareehu Ashafa.
kananan Hukumomi.
gyara sasheJihar Lagos ta rabu gida Biyar (5) wurin rabe-raben ayyuka, wadanda suka kara rabuwa zuwa kananan Hukumomi ashirin (20). Sune:[1]
Sunan Karamar hukuma | Fadin kasa (km2) | Kidayar Jama'a ta dubu biyu da shida 2006 |
Cibiyar Karamar hukuma | Lambar Aika Sako |
---|---|---|---|---|
Agege | 11 | 459,939 | Agege | 100 |
Alimosho | 185 | 1,277,714 | Ikotun | 100 |
Ifako-Ijaye | 27 | 427,878 | Ifako | 100 |
Ikeja | 46 | 313,196 | Ikeja | 100 |
Kosofe | 81 | 665,393 | Kosofe | 100 |
Mushin | 17 | 633,009 | Mushin | 100 |
Oshodi-Isolo | 45 | 621,509 | Oshodi/Isolo | 100 |
Shomolu | 12 | 402,673 | Shomolu | 101 |
Ikeja Division | 424 | 4,801,311 | ||
Apapa | 27 | 217,362 | Apapa | 101 |
Eti-Osa | 192 | 287,785 | Ikoyi | 101 |
Lagos Island | 9 | 209,437 | Lagos Island | 101 |
Lagos Mainland | 19 | 317,720 | Lagos Mainland | 101 |
Surulere | 23 | 503,975 | Surulere | 101 |
Lagos Division | 270 | 1,542,279 | ||
Ajeromi-Ifelodun | 12 | 684,105 | Ajeromi/Ifelodun | 102 |
Amuwo-Odofin | 135 | 318,166 | Festac Town | 102 |
Ojo | 158 | 598,071 | Ojo | 102 |
Badagry | 441 | 241,093 | Badagry | 103 |
Badagry Division | 746 | 1,841,435 | ||
Ikorodu | 394 | 535,619 | Ikorodu | 104 |
Ikorodu Division | 394 | 535,619 | ||
Ibeju-Lekki | 455 | 117,481 | Akodo | 105 |
Epe | 1,185 | 181,409 | Epe | 106 |
Epe Division | 1,640 | 298,890 | ||
Total | 3,474 | 9,019,534 | Ikeja |
Sha shidan (16) farko na sunayen dake sama, sun kunshi wurare ne daga cikin garin birnin Lagos. Sauran kananan hukumomi hudun (4) kuma, wato (Badagry, Ikorodu, Ibeju-Lekki ds Epe) suna daga Jihar ne, amma ba daga cikin garin Birnin Lagos ba.
A shekara ta dubu biyu da uku 2003, yawancin kananan hukumomi ashirin (20) dake nan a yanzu, an rarraba su domin harkokin gudanar da aiki zuwa Local Council Development Areas. Wadanda sune a yanzu adadin su ya kai hamsin da shida 56, sune: Agbado/Oke-Odo, Agboyi/Ketu, Agege, Ajeromi, Alimosho, Apapa, Apapa-Iganmu, Ayobo/Ipaja, Badagry West, Badagry, Bariga, Coker Aguda, Egbe Idimu, Ejigbo, Epe, Eredo, Eti Osa East, Eti Osa West, Iba, Isolo, Imota, Ikoyi, Ibeju, Ifako-Ijaiye, Ifelodun, Igando/Ikotun, Igbogbo/Bayeku, Ijede, Ikeja, Ikorodu North, Ikorodu West, Ikosi Ejinrin, Ikorodu, Ikorodu West, Iru/Victoria Island, Itire Ikate, Kosofe, Lagos Island West, Lagos Island East, Lagos Mainland, Lekki, Mosan/Okunola, Mushin, Odi Olowo/Ojuwoye, Ojo, Ojodu, Ojokoro, Olorunda, Onigbongbo, Oriade, Orile Agege, Oshodi, Oto-Awori, Shomolu, Surulere and Yaba.[2]
Manazarta.
gyara sashe- ↑ "Lagos State - Population". Archived from the original on 2011-06-15. Retrieved 2018-12-18.
- ↑ "Local Government Areas". Archived from the original on 2010-03-24. Retrieved 2010-03-20.
Jihohin Najeriya |
Babban birnin tarayyar (Abuja) | Abiya | Adamawa | Akwa Ibom | Anambra | Bauchi | Bayelsa | Benue | Borno | Cross River | Delta | Ebonyi | Edo | Ekiti | Enugu | Gombe | Imo | Jigawa Kaduna | Kano | Katsina | Kebbi | Kogi | Kwara | Lagos | Nasarawa | Neja | Ogun | Ondo | Osun | Oyo | Plateau | Rivers | Sokoto | Taraba | Yobe | Zamfara |