Oluremi Tinubu
Oluremi Tinubu (an haife ta 21, ga watan Satumba 1960)[1] ƴar asalin jihar Ogun ce, Nijeriya, tsohuwar matar shugaban jihar Legas ce kuma a yanzu haka sanata ce mai wakiltar Lardin Sanatan Legas ta Tsakiya a Majalisar Dokokin Najeriya. Ita mamba ce a jam’iyyar siyasa ta All Progressives Congress (APC).[2][3]
Oluremi Tinubu | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
29 Mayu 2023 - ← Aisha Buhari
ga Yuni, 2019 - ← Munirudeen Adekunle Muse
ga Yuni, 2015 - District: Lagos Central
6 ga Yuni, 2011 - 4 ga Yuni, 2015 District: Lagos Central | |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Ogun, 21 Satumba 1960 (64 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||
Ƴan uwa | |||||||||
Abokiyar zama | Bola Ahmad Tinubu | ||||||||
Yara |
view
| ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta | Jami'ar Obafemi Awolowo | ||||||||
Matakin karatu | Digiri a kimiyya | ||||||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||
Employers | Najeriya | ||||||||
Imani | |||||||||
Jam'iyar siyasa |
Action Congress of Nigeria All Progressives Congress |
Rayuwar farko da ilimi.
gyara sasheFasto Oluremi Tinubu ta kasance mafi ƙaramar cikin yara 12; ta tashi ne a jihar Ogun.[4][5]
Tinubu ta fara karatun gaba da firamare a makarantar Our Lady of Apostles Secondary School Ijebu-Ode inda ta samu takardar shaidar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE) a shekarar 1979, da kuma digiri na biyu (PGD) daga The Redeemed Christian Bible college a shekara ta 2010.[6]
Tinubu ya samu shaidar kammala digirin farko B.S.-(Bachelor of Science) a fannin ilimi daga Jami’ar Ife, da takardar shedar ilimin botany da dabbobi-(Zoology) daga Kwalejin Ilimi ta Adeyemi.[6]
Harkar siyasa.
gyara sasheFasto Tinubu ta zama uwargidan gwamnan jihar Legas lokacin da aka zaɓi mijinta, Bola Tinubu a matsayin gwamna. A matsayinta na uwargidan shugaban gwamna, ta kafa gidauniyar New Era, wacce aka sadaukar domin kafa cibiyoyi don "duk cigaban matasa da inganta wayar da kan jama'a game da kiwon lafiyar muhalli da taimakon al'umma."
Lokacin da aka zaɓi Tinubu, an kalubalance shi a Kotun ɗaukaka ƙara kan zaɓen majalisar dokoki - wacce daga baya ta yi taro ta kuma tabbatar da zaben a 2012.
Tinubu tana ɗaya daga cikin sanatoci sama da 100, da aka zaɓa a majalisa ta 8, a 2015. Shida daga cikin wadannan mata ne. Sauran su ne Stella Oduah da Uche Ekwunife, wadanda dukkansu ke wakiltar Anambra, Fatimat Raji Rasaki, Rose Okoji Oko da Binta Garba . [7] A babban zaben shekarar 2019, ta ci gaba da rike kujerar sanata mai wakiltar Lagos ta Tsakiya, wanda ya sanya ta zama ta uku a ofis
Rayuwar mutum
gyara sasheFasto Oluremi Tinubu ya auri tsohon Gwamna kuma Sanatan Jihar Legas, Bola Tinubu
Ita Kirista ce. kuma limamin coci ne wanda aka zaɓa na Ikilisiyar Kirista da aka fanshe ta Allah.
Nadin nata ya faru ne a Old Arena na RCCG, Lagos / Ibadan Expressway inda cocin yake a halin yanzu yana da babban taron shekara-shekara na 66 taken "Dominion".
Manazarta.
gyara sashe- ↑ "Remi Tinubu: Trauma of living in exile in US led me to Christ". TheCable (in Turanci). 2020-09-26. Retrieved 2021-04-19.
- ↑ "Senator Remi Tinubu Full Biography". 7 December 2016.
- ↑ "Oluremi - Tinubu, Politician, Senator and Entrepreneur, Nigeria, Personality Profiles". nigeriagalleria.com. Retrieved 2020-05-30.
- ↑ Akinkuotu, Eniola (9 March 2019). "Remi Tinubu is from Delta, ex-NHRC boss Odinkalu says". punchng.com. punchng.com. Retrieved 11 March 2019.
- ↑ "About Oluremi". Oluremi Tinubu. Archived from the original on 15 February 2017. Retrieved 20 May 2012.
- ↑ 6.0 6.1 "Pastor Oluremi Tinubu". politiciansdata.com. Omobolaji Folajinmi. 28 May 2018. Archived from the original on 24 April 2021. Retrieved 24 April 2021.
- ↑ The 6 female senators in 8th National Assembly, Naij,com, Retrieved 15 February 2016