Shehu Shagari
Shehu Shagari Ɗan siyasan Nijeriya ne. (An haife shi a ranar ashirin da biyar 25 ga watan Fabrairu, shekara ta alif ɗari tara da ashirin da biyar 1925) a garin Shagari, Arewacin Najeriya (a yau jihar Sokoto)[1], ya kuma rasu ne a ranar ashirin da takwas 28 ga watan Disamba, shekara ta dubu biyu da sha takwas 2018 bayan jinya da gajeriyar rashin lafiya da yayi a wani asibiti dake Abuja. Ya rasu yana ɗan shekara casa'in da uku (93) da haihuwa. Shehu Shagari ya zama shugaban ƙasar Najeriya a watan Oktoban shekara ta alif dari tara da Saba'in da tara (1979), inda yayi mulki har zuwa Disamban shekara ta alif da dari tara da tamanin da uku (1983), wanda sojoji suka kwace mulki a hunnunsa, a jagorancin Muhammadu Buhari. Shehu Shagari shine shugaban Najeriya da ya hau mulki ta sanadiyar zaɓe na farko.[2] Olusegun Obasanjo ne ya bayar da mulkin zuwa ga farar hula, a dalilin haka da matsi da mulkin sojoji ke fuskanta, ga rashin yin katabus, ganin hakan ne dai yasa Obasanjon ya bayar da mulkin amma ba'a kai ko’ina ba sai sojojin suka sake dawowa suka kwace mulki daga hannun farar hula, inda suka zargi mulkinsa da cin hanci da rashawa, hakane ne dai ya kai ga Muhammadu Buhari ga zama shugaban Ƙasa a wanchan lokacin.[3][4]
Shehu Shagari | |||||
---|---|---|---|---|---|
1 Oktoba 1979 - 31 Disamba 1983 ← Olusegun Obasanjo - Muhammadu Buhari →
1971 - 1975 ← Obafemi Awolowo - Asumoh Ete Ekukinam (en) → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Shagari (Nijeriya), 25 ga Faburairu, 1925 | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Mutanen Fulani | ||||
Mutuwa | Abuja, 28 Disamba 2018 | ||||
Ƴan uwa | |||||
Yara | |||||
Ƴan uwa |
view
| ||||
Karatu | |||||
Makaranta | Kwalejin Barewa | ||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Imani | |||||
Addini | Mabiya Sunnah | ||||
Jam'iyar siyasa | Jam'iyyar National Party of Nigeria |
Tarihi
gyara sasheTarihi ya nuna cewa Shehu Shagari ya samo asali ne daga Muhammadu,wanda ɗan uwan kakan-kakan Shehu Shagari ne, Makiyayi ne kuma yana yawo da iyalansa baki daya. Kuma an nuna cewa sun zauna a sifawa a shekara ta 1810, kuma ya zama daga cikin dakarun Shehu Usman Ɗan Fodiyo[1]. Hakazalika tarihi ya nuna cewa Shagari wani wuri ne wanda ya samo asali lokacin Shehu Ɗan Fodio sun tsaya tare da mutanen Muhammadu a wani wuri domin hutawa, sai dan Fodiyo yace, "Ku Sha Gari” (Fura da Nono). Daga nan aka sanya ma wurin Shagari, shi kuma shugaban Muhammadu Shagari. Muhammadu Shehu Shagari ya rasu kuma an binne shi a Shifawa, inda aka binne Shehu Usman Ɗan Fodiyo. Muhammadu Shagari ya rasu ya bar yaya biyu Usman Da Iggi, wanda Iggi ne babba kuma an nada Iggi a matsayin magajin Shagari watau shugaban garin Shagari (Najeriya). Bayan nadin sarautan Magajin Shagari, Igge tare da kawunsa Shehu dan Fodiyo suka karo dakarun tsaro kuma aka zagaye garin Shagari da ganuwa[5]. Daga nan garin Shagari ya fara bunƙasa a harkokin kasuwanci har ma ya mamaye ƙauyukan Sokoto ta kudu[1].Ƴan kasuwa da matafiya kan yada zango a garin Shagari a duk lokacin da dare yayi musu. Saboda mutanen garin suna da kara da kyawawan dabi'u da halaye masu kyau. Garin Shagari ya zama amintaccen gari mai zaman lafiya duk da yaƙe-yaƙe da akai tayi a ƙarni na 19th a ƙarƙashin magajin Shagarin. Sarautar Sokoto ƙarƙashin shari’ar musulunci[1].
Bayan Turawa sun kama Sokoto, sababbin ƙauyuka sun samu an sanya garin Shagari ƙarƙashin mulkin Yabo[1]. Muhammadu Basharu ɗan Magaji Rufa’i ya sake zama magajin Shagari duk da sun rasa mulki bayan da Turawa suka zo. A lokacin da aka haɗa kudanci da Arewacin Najeriya, a shekara ta alif ɗari tara da sha huɗu (1914) aka naɗa Aliyu baban Shehu Shagari wanda ya gaji Galadima Bayan rasuwarsa da karban mulki daga hannun Muhammadu Basharu[1]. Bayan ƙirƙirar Jihohi, da ƙananan hukumomi a 1996, shagari ya zama sabon cibiyar ƙaramar hukumar- da yawan mutane 83,540 a ƙauyuka 10 dake ƙarƙashinsa. Garin Shagari Ya rasa mutane dalilin sabbin hanyoyin kasuwanci na zamani[1]. Duk da garin Shagari ba wata muhimmiyar alƙarya bace, amma tarihi ya nuna cewa garin ya wanzu cikin zaman lafiya da riƙon amana kusan mutanen garin na kula da harkokin gabansu ba tare da katsalandan ba[6].
Tarihi ya nuna cewa an haifi Shehu Shagari ne a ranar laraba 8 ga watan Sha’aban (watan musulunci) a Shekarar 1925[7].(p14) Mahaifiyar Shehu Shagari na kiransa da inkiya Balarabe, saboda an haifeshi a Sha’aban[8]. Asalin sunan Shehu Shagari “Usman” wanda ya samo asali daga Uthman Ibn Affan sannan kuma sunan kakansa ne ƙanin Muhammadu shagari (wanda ya ƙirƙiro garin shagari) hakazalika sunan Shehu Usman Ɗan Fodiyo[9]. Hausawa kan kira Usman Shehu. Shehu shagari ɗa na uku ne a wajen mahifiyarsa[10].
Rayuwa da Ilimi
gyara sasheShehu shagari ya fara ganin mota a rayuwarsa a lokacin yana dan shekara biyar a shekarar 1930, lokacin da sultan muhammadu Tambari (1925-1931) yazo garin shagari ya kwana a gidan shehu shagari. (p16Tarihi ya nuna tun kafin a tura shehu shagari makarantar boko ya riga ya koyi ilimin addinin musulunci a wurin iyayensa da kuma manyan malamai[11]. (p17
Shehu shagari yayi zurfin karatu a ilimin addini kuma a duk lokacin da ya sami hutu yakan tsaya ya koyar da ilimi a ƙauyensa[12]. (p20) saboda a fahimatarsa, ilimi wani abu ne da ya jiɓinci rayuwa gaba ɗaya, tun daga farko har ƙarshe. Shehu Shagari ya shafe tsawon shekara 34 yana kuma koyarwa. Shehu Shagari ya bar garin shagari a karo na farko a shekarar 1931, inda ya tafi neman ilimin zamani watau boko a garin yabo. Mahaifinsa ya rasu lokacin yana da shekara biyar[13].
Siyasa
gyara sasheA shekara ta 1962 sultan Sir Saddiq Abubakar III ya naɗa shehu Shagari Turakin sokoto a matsayin minista wanda sir Ahmadu Bello ya naɗa a kawu a watan Aprilu a garin kaduna[14].
A zaɓen watan oktoba, shekara ta 1960, wacce zata kawo ƴanci a ƙasar nan, jam’iyyan NPC (wanda sir Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa Balewa a matsayin mataimakinsa) yaci. An kuma naɗa shehu shagari da Alhaji Muhammadu Ribaɗu, Alhaji Inuwa Wada, Zanna Bukar Dipchorime, Waziri Ibrahim, Usman Sarki, Musa yar,adu'a matsayin ministocin ƙasa bayan da da Najeriya ta samu ƴanci kai[15].
An naɗa shehu shagari a matsayin ministan ayyuka da ɗuba a watan Mayun shekara ta 1965[16]. Aikin shehu Shagari na farko a matsayinsa na minista shine canza sakatarorin gwamnati na turawa da ƴan najeriya[17].
A ranar 23 ga watan oktoba, shekara ta 1978, shehu shagari ya yanke shawara fitowa takaran shugan ƙasa akan cewa zai janye idan har bai cinye yawan kuri’u ba[18]. A zaɓen da akayi a ranar asabar 9 ga watan December shekara ta 1978, shehu shagari ya cinye ƙuri’u 975, Maitama Sule 504, Adam Girome 293, Dr. Saraki 214, Traka 104, Prof Abubakar 92. (primary election held at casino cenema)[19].
Jam’iyyar NPN na shehu shagari ta lashe kujeru 36 (37.89%) na sanatoci da 168 (37.41%) na kujerun ƴan majalissu. A ranar Alhamis da ƙarfe 12:40pm aka sanar shehu shagari yaci zaɓen shugaban ƙasa da ƙuri’u 5, 688857[20]. An rantsar da shugaba na farko da aka zaɓa a Najeriya (Shehu Shagari) ranar litinin a Tafawa Ɓalewa Square wanda dake Legas.
Ayyukan Cigaba
gyara sasheDaga cikin kamfanonin da shehu shagari ya samar sun haɗa da:
- Ministry of steel develpment
- Aledja steel plant a shekarar 1982
- Steel rolling mills katsina
- Steel rolling mills oshogbo
- Steel rolling mills jos.
- Anambra motor company a shekarar 1980
- National truck manufacturing company kano a shekarar 1981
- Stey motors bauchi
- Leyland Ibadan
- Private assembley company Illorin, Onitsha, Gusau, Benin & Porthercourt[21].
Bibliyo
gyara sashe- Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). ISBN 978-129-932-0. OCLC 50042754.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 1.6 Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 13. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ https://hausa.legit.ng/news/1537778-tarihin-mulkin-najeriya-jerin-shugabannin-najeriya-16-da-kuma-jihohin-da-suka-fito/
- ↑ https://www.theguardian.com/world/2019/jan/09/shehu-shagari-obituary
- ↑ https://www.pmnewsnigeria.com/2018/12/28/life-and-time-of-alhaji-shehu-shagari/
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 5. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 13. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 14. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p.14. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). pp. 14-15 ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 8. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 17. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 20. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 31 ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria).pp. 57-58. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). pp. 70-80. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 103. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p.90. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p.200. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). pp. 213-214. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria). p. 227. ISBN 978-129-932-0.
- ↑ Shagari, Shehu Usman Aliyu, 1925-2018. (2001). Shehu Shagari : beckoned to serve : an autobiography. Ibadan: Heinemann Educational Books (Nigeria).p. 310. ISBN 978-129-932-0.